Me za ka yi idan shugabanka na nuna fifiko?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Idan ba kai ne mutumin da shugaban wurin aikinmu ya fi ƙauna ba, wani ne daga cikin takwarorinka ɗan gaban goshinsa, wannan ya isa ya sa ka damu har ya yi tasiri a aikinka?

To kada ka damu ga abin da za ka yi.

Ga binciken Elizabeth Garone

Har yanzu Karl Moore bai manta lokacin da suka bata da shugabansa ba. Yana aiki ne a matsasin manaja a kamfanin IBM a Toronto a lokacin da wani sabon ma'aikaci ya zo.

Kafin zuwan wannan sabon ma'aikaci Moore yana daya daga cikin 'yan gaban-goshin shugaban kamfanin, amma kwatsam sai komai ya sauya.

Wannan sabon ma'aikaci sai ya zama shi ne dan gaban-goshin shugaban nasu a wannan wuri.

Moore wandfa yanzu farfesa ne a jami'ar McGill a Montreal ta Canada, ya ce, ''wannan labari ne mai kyau ga ma'aikatan, to amma ni nan da nan sai na zama dan zaman ko-ta-kwana.

Ya ce, wannan abu bai yi masa dadi ba, kuma ba shakka hakan ya sa aikin ya kara zamar masa mai wuya.

Idan shugabanku yana fifita wasu abokan aikinku kuma ba ka daya daga cikinsu, ko akwai wani abu da za ka iya yi a kan hakan? Kuma ma shin wani abin damuwa ne idan ba ka cikin 'yan gaban-goshinsa? Tun da ma ai ba wanda yake son mai bambadanci.

Bayan shekara daya da faruwar wannan abu sai kuma kaunar ta sake dawowa kaina. A karshe sai Moore ya sake samun gindin zama a wurin wannan shugaba nasu. Amma dai an dauki lokaci kafin farin jinin wannan sabon ma'aikaci ya dan ragu a wurin shugaban nasu.

Wani abu mai muhimmanci ma shi ne, Moore ya da ce da yadda ya kawo wasu abubuwa na cigaba masu muhimmanci wadanda suka taimaka wa shugaban nasu ya yi nasara a ayyukan kamfanin.

Sabawa da shugaban wurin aikinka ba akan wani dalili mai tushe ba ba abu ne da za ka ji dadinsa ba. To amma ka sani ba abu ne na dindindin ba. Ga yadda za ka bullo wa lamarin.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Siyasar ofis na iya sa a mayar da wani ma'aikaci ɗan mowa

Ka yi tunanin abin da shugaban naka yake bukata ya yi nasara a aikinsa, kuma ka rika kyautata wa shugabanninsa (na wurin aikin) su ma. Ka yi kokari ka tabbatar da hakan.

Moore ya ce, ''daya daga cikin abubuwan da ke sa dukkanin shugabanninmu su rika kaunarmu, shi ne idan muka taimaka musu suka suka yi nasarar yin daya daga cikin abubuwa masu wuya da suka sanya a gaba na shekarar.''

Moore ya kara da cewa, ''idan za ka gano muhimman abubuwa uku da shugaban naka ya sanya a gaba, kuma ka taimaka masa ya yi nasara a daya daga cikinsu, nan da nan za ka ga zama daya daga cikin 'yan mowarsa.''

Farfesan ya ce, wani lokacin ba ma wani abu za ka yi ba, illa kawai ka tambayi abubuwan da ya fi so a yi (a wurin aikin), sai kawai ka taimaka abubuwan su tabbata shikenan.

Shugabanka a matsayin kwastomanka

A wurin Andew Wittman, tsohon sojan Amurka, da dan sanda da kuma jami'in leken asiri, mafita ita ce ka sauya tsarinka. Ya ce, ''duk inda kake aiki ko wa kake yi wa aiki, idan ka fuskanci aikinka ta sigar da ke cewa,' Shugabana ba shugabana ba ne; shi ko ita (shugaban) kwastoma na ne', sai komai ya sauya.''

Wittman wanda yanzu babban jami'i ne a kamfanin bayar da horo na Mental Toughness Trainin Center da ke Carolina ta kudu a Amurka, ya ce da ka dauki wannan tsarin to za ka ga yadda ba bata lokaci kai tsaye ka zama kai ne da ikon komai.

Kusan kana ba wa kamfanin hayar ayyukanka ne kawai. Sun zama kamar kwastomominka ne. Abu ne mai muhimmanci kada ka dauka cewa wai don kai ba ka cikin 'yan gaban goshin shugabanku abin ya fara damunka ba, in ji Wittman.

Idan ba haka ba, tunanin da za ka yi ta yi kenan, kuma da haka za ka rasa damar samun ci gaba.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Za ka iya sake zama ɗan lelen shugabanka

Idan ka mayar da hankalinka wurin kokarin gamsar da shugabanka a matsayin kwastoman da ya gamsu da aikinka tunaninka zai karkata ga cewa kai ne dan gaban goshin shugaban in ji Wittman.

Saboda haka za ka ga hankalinka ya karkata wajen magance matsaloli, kuma kana tafiyar da aikinka ta yadda shugaban zai kasance cikin farin ciki ko da yaushe.

'Yan gaban goshi

Kasancewar kana ganin kamar shugaba ba ya sonka, hakan ba ya nufin sauran mutane ma ba za su kaunace ka ba. Idan sauran mutane suna sonka, hakan zai iya sa shugaban ya sauya ra'ayinsa a kanka.

''Ka yi kokari ka zama kana dasawa da zaman mutunci da mutanen da shugaban ya fi so,'' in ji Vicky Oliver, marubuciyar littafin Bad Bosses, Crazy Coworkers & Other Office Idiots.

Abin da ya dace

Kada ka zake a kan shugabanka, ta yadda za ka sa abokan aikinka su tsane ka. Misali idan shugabanka ya yi wani barkwanci wanda ba me ban dariya ba ne sosai, to kada ka fi sauran abokan aikinka dariya da yawa, in ji Oliver.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Kada ka zaƙe a yabon shugaba don kada a ga ka zama mai bambaɗanci

''Idan kana da amsar wata matsala wadda ba wanda ya zo da ita, wannan zai kara maka kwarjini da farin jini,'' ta ce. ''Idan ka yaba wa sauran abokan aikin naka kan yadda suka taimaka ka samo wannan mafita, wannan zai kara maka matsayi a wurin shugaban da abokan aikin.

Abu ne mai wuya a zamanin nan ka samu shugaba ko wani ma'aikaci da ke karkashinka wanda za ku yi ta dasawa da shi har abada. To ka ga kenan idan ba za ka kasance da wannan shugaba da ba ya sonka ba har abada.

Watakila ka ba ma ka son shugaban da yake ware wani ma'aikaci ya nuna masa kauna fiye da saura, ko da kuwa kai ne wanda shugaban ya fi so.

Amma kada ka bari a san cewa kai ba ka son irin wannan tsarin, kai dai kawai ka ci gaba da yin aikinka kamar yadda ya dace, kuma ka nuna wa sauran abokan aiki cewa ka damu ka kowa.

Kuma kana hakan sai ka tabbatar kana kokarin karkatar da aikinka wurin shugaban da ya fi, ta yadda za a yi maka karin girmanka na gaba, in ji Moore.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What to do when your boss plays favourites