Kora daga aiki ka iya zama alheri

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Damuwarka ita ce ba ka da wani aiki takamaimai a kamfaninku, kana tunanin yadda za ka tsira kada a sallame ka kuma ka samu cigaba a aikin. To akwai yadda za ka iya ci gaba ko da an sallame ka.

Wadannan na daga cikin matsalolin ma'aikata kamar na banki da kamfanoni da makamantansu, kuma ba abu ne mai sauki ba ka iya shawo kansu.

Wadannan batutuwa na daga abubuwan da kwararru a shafin mu'amulla na ma'aikata na intanet Linkedln suka duba- matsalolin da suka kama daga tsallake wa wani abin kunya a wurin aiki zuwa dalilin da sallamarka daga aiki akalla sau daya a rayuwa ka iya zama alheri.

Ga abin da wasu kwararru biyu suka ce.

Sally Krawcheck babbar jami'a a kan harkokin kudi kuma tsohuwar shugabar bankin Amurka

Na tuna lokacin ina matashiyar mai fashin baki a kan bincike-bincike ta wani kamfani, bayan 'yan watanni kadan da fara aikin, a lokacin da nake gabatar da jawabi a wurin taron safe.

''Na tabbata muryata tana karkarwa, kuma ina magana da sauri da sauri, sannan kuma ina gwamutsa kalmomina'', yadda Krawcheck ta rubuta kenan a bayaninta na, 'How to Survive Humiliation at Work' a shafin Linkedln.

Wannan kadai ya isa abin kunya, kamar yadda ta rubuta. ''Daga gabana kadan a hannun dama, babban jami'i ne mai yin fashin baki ne na sashenmu, kuma duk tsawon lokacin da nake wannan jawabi sai gyada kansa yake yi yana rufe fuska, yana nuna alamun gazawarta.

Krawcheck ba kawai ta dauki wannan abin a matsayin wata mugunta ba, abin ya ma wuce haka. ''Duk tsawon shekarun nan bayan nan, har yanzu ina jin kunyar wannan abu,'' ta rubuta.

Kai tsaye Krawcheck ta nufi ofishin wannan jami'i ta tambaye shi abin da za ta yi domin ta gyara kura-kurenta a gaba. Sai kawai ya koreta ba wata-wata, yana mai cewa ba shi ne shugabanta ba.

Ta ce, ''duk da haka kuma sai ya ci gaba da yi min abin da ya saba yi a duk lokacin da nake gabatar da jawabi a wurin taronmu na safe,'' ta rubuta.

Krawcheck ta ce, domin in jure wa wannan mummunar halayya tasa, ta yi abubuwa da yawa:

''Sai na tafi ofishin shugaban domin na ji bayaninsa game da yadda nake jawabin nawa da sauran abubuwa, komai dacin abin da zan ji. Sanna kuma na tambayi sauran ma'aikata su ma su gaya min yadda suke kallon aikin nawa. A duk lokacin da na samu dama ina neman shawara kan yadda zan gyara aikina,'' ta rubuta.

''Na ci gaba da yin jawabi a taron namu na safe. Ban yi watsi da abin da wannan babban jami'i na sashen namu yake yi min ba, na nuna rashin amincewa da yadda nake aiki. Amma abu mafi muhimmanci shi ne na dage da domin na kware na kuma yi nasara a aikin.''

Ko alama ban ji dadi ba, Krawcheck ta rubuta, ''amma hakan ya taimaka min na yi fice a cikin sauran abokan aiki, kuma na tabbata cewa na samu nasara fiye da sauran da wuri, saboda abin da ya faru a kaina.''

Ga bayanin Michelle Mastrobattista, daraktar ayyukan sadarwa a kamfanin Solomon McCown & Co.

Shekaru kadan bayan Mastrobattista, ta gama jami'a, sai ta samu damar daukarta aikin da take buri, ''ta zama babbar akanta a wani kamfanin harkokin nishadantarwa, wanda ke aiki da manyan kamfanoni irin su Fiji Water da Philips da kuma Volkswagen. Aikin ya dace daidai da burina. In matukar sonsa,'' ta rubuta a makalarta mai taken, Why Everyone Should Be Laid Off at Least Once.

''Komai na tafiya daidai sai rana daya kawai, da aka sallame ni daga aiki,'' ta rubuta. ''Wannan shi ne abu mafi muni da na taba ji. Bugu da kari ma, sai shugabana ya dauke ni a motarsa ya kai ni gida, saboda da motar kamfanin na je wurin aiki ranar. Kuma ban dauko mukullayena ba, na tuna yadda na riko jakata bayan na kwashe kayayyakina na tsaya ina kuka.''

To amma ba karshen duniya ba kenan in ji Mastrobattista. A gaskiya ma, abin alheri ne. ''Ina ganin ya kamata kowa ma a kore shi daga aiki akalla sau daya a rayuwarsa,'' ta rubuta.

''Alherin shi ne korata da aka yi daga aikin ta tilasta min na dauki mataki na gabakuma na ci gaba da koyo.'' Ba da jimawa ba sai Mastrobattista ta samu wani aiki, ko da yake bai kai na matsayin da ta rike a baya ba. Amma ta rubuta cewa, shugabanta ya rika kara mata aiki, sai dawainiyarta ta karu.

A gaba kuma sai ayyuka suka rika bullo mata nan da can, tana aikin kafa sashen dandalin zumunta na intanet nawani sabon kamfanin tallata hajoji.

''A karshe dai na samu abin da nake so,''ta rubuta. ''Na samu nasarar da ban taba tsammani ba. Fadi-tashin da na yi ta gamuwa da shi ne ya taimaka min na zama abin da na zama yau. Magana ce kawai ta yadda ka yi amfani da duk yanayin da ka samu kanka a ciki a duk abin da kake yi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Surviving the worst at work