Za ka iya yin kuɗi da mota me lantarki?

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai abubuwa da yawa da ake dangantawa da kuma samu daga mota mai amfani da lantarki, to amma za ka iya yin arziki da ita, ganin irin kalubalen da ke tattare da ita?

Richard Taylor ya duba mana

Ba wata tantama ba kuma tababa, kasuwar mota me aiki da lantarki na bunkasa. Duk da cewa yawan irin wadannan motoci masu aiki da lantarki da ke kan tituna bai kai kashi daya cikin dari ba, kasuwarsu a duniya ta tashi zuwa kashi 60 cikin dari.

Wannan farkon alama ce ta bunkasar abin da ya ba wa masu zuba jari da kuma masu kera motoci sha'awa.

Yayin da tallafin gwamnati ke sa mutane rububin sayen motocin, kuma farashi ke ci gaba da faduwa, an yi kiyasin cewa nan da shekara ta 2040 kashi 35 cikin dari na sabbin motoci zai kasance masu amfani da lantarki.

A China kadai gwamnati ta zuba jarin dala biliyan 15 a harkar domin ganin an samu motocin masu lantarki miliyan biyar a kan titunan kasar nan sa shekara ta 2020.

Kamafanonin motoci masu fasaha da kirkire-kirkire irinsu Tesla wanda ya samu gagarumar bunkasa a cikin kasa da shekara goma , wanda kuma ya yi suna da sanfurin motar tasa mai lantarki da ya kira Model 3, duk da cewa kamfanin bai bayyana yawan ribarsa ba har yanzu, su ne suke gudanar da harkar ta samar da motocin masu amfani da lantarki.

Tsofaffin kamfanoni mota wadanda suka yi suna kamar su GM da Nissan su ma sun shiga wannan harka ta kera motoc masu amfani da lantarki.

Haka kuma a bangaren kamfanoni masu kera sassan kayan mota, suna kafa sashen musamman na samar da kayan irin wadannan motoci, wanda hakan zai taimaka wajen sassauta farashin muhimman kayan mota kamar batiri.

Wannan karin dama ce ga masu sha'awa da za su iya samun kudi ta hanyar.

Sai dai kuma in banda yanzu abubuwan da suka danganci motoci masu amfani da lantarki suka da wuyar sha'ani. Saboda haka zuba jari a wannan fanni ba abu ne na mai tsoro ba. Ka san dalili?

Dalilin shi ne kayayyaki ko wuraren chajin motocin ba su da yawa, kuma kasuwarsu ba ta kankama ba sosai kamar yadda ake tsammani.

Sannan a kwanannan faduwar farashin mai a duniya ta kara haifar da koma baya ga bukatarsu (saboda mutane na samun saukin hawa motocinsu masu amfani da mai).

Haka kuma wani kalubalen ga wannan harka ta samar da mota mai amfani da lantarki shi ne, akwai sabbin fasahohi da ake kirkirowa da za su yi gogayya da fasaharta, kamar batiran makamashin hydrogen wadanda babbar barazana ce ga dorewar wannan fasaha ta motar.

Akwai damammaki masu yawa da kuma kalubale da ke tattare da harkar mota mai aiki da lanatarki wadanda za su iya kawo cikas ga zuba jari a fannin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Inglishi latsa nan. The Tesla effect: Can you get rich from electric cars?