Ta yaya ake samun shugaba na gari?

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugabanci. Menene ma shugabanci? Menene jigon shugabanci? Kuma me ya sa yake da wuya a samu shugabanni na gari?

Wannan shi ne abin da kwararru a shafin intanet na harkokin da suka shafi ma'aikata, LinkedIn suka tattauna a wani lokaci a 2014.

Daga cikin kwararrun akwai babban jami'in kamfanin JP Morgan Chase & Co, Jamie Dimon - wanda ya yi nasarar cigaba da rike mukaminsa na babban jami'i a bankin, da mai kamfanin Microsoft Bill Gates.

Sauran su ne Anand Chandrasekaran na kamfanin Yahoo, da kuma babban jami'in asibitin Johns Hopkins Medicine International, Steven Thomson.

Kowanne daga cikin wadannan mutanen ya gabatar da yadda yake ganin shugabanci yake, abin da ya hada da dabi'un shugabanni da koyar da ilimin da suka koya daga ayyukan sa kai da suka yi da kuma watsa ilimi da kwarewa daga wasu daga cikin fitattun masu zuba jari na duniya.

Yadda shugabanci yake a wurin mutanen da suka yi shi suka kuma yi nasara

Jamie Dimon, babban jami'in bankin JP Morgan Chase & Co, ya ce, ''Shugabanci girmamawa ne, da samun dama da kuma babbar dawainiya".Idan shugabanni suka yi kuskure, mutane da dama za su iya cutuwa.

Mutum ya zama mai gaskiya a kan kansa sannan ya guji yaudarar kansa, wadannan abubuwa ne da ke da muhimmanci kamar yadda za a ce shugaba yana da mutane na gari masu ba shi shawara mai kyau idan bukatar hakan ta taso, kamar yadda Dimon ya rubuta.

Ya kara da cewa ina ganin basirar mu'amulla da mutane da tausayi suna da muhimmanci wurin tafiyar da shugabanci.

Sauran abubuwan da Dimon ya jaddada muhimmancinsu ga shugabanci na gari sun hada da; da'a da inganci da yarda da gaskiya komai dacinta, da nuna gaskiya ba tare da wani boye-boye ba, da karfafa wa jama'a guiwa, da biyayya, da bin cancanta tare da aiki tare da jama'a, da yakana.

Sannan kuma akwai abin da Dimon ya kira bangarorin da ke tattare da kalubale ko matsaloli na shugabanci, wadanda kowa zai iya yi musu fassara yadda ya fahimce su.

Wannan fanni ne da ya shafi kalubalen da shugabanni da kuma wadanda suke shugabanta suke fuskanta, daga cikinsu akwai; masu karfafa guiwa da sakayya da kuma kokari.

Sai bayanin Bill Gates, shugaban kamfanin Microsoft da kuma jagorancin asusun Bill and Melinda Gates Foundation

A farkon rubutunsa da ya yi a shafin, Mista Gates, ya bayyana abubuwan abin da ya koya daga fitaccen dan kasuwa kuma babban jami'in kamfanin Berkshire Hathaway, Warren Buffett.

Gates ya ce hanyar da Buffett yake kallon shugabanci ba a harkokin gina kasuwanci kadai ta tsaya ba. ''Ba abu ne na harkar zuba jari ba kawai, abu ne da ya kunshi duk wani abu da ya shafi tunanin kasuwanci wanda ke da karfi sosai.

Ya ce dole ne mai hannun jari ya yi aiki kamar shi ne ya mallaki harkar kasuwancin gaba daya, ya duba yadda ribar kamfanin za ta iya kasancewa a gaba domin ya dauki matakin da ya dace.

Ya ce, ''yi amfani da abin da kake da shi. A shirye yake ya yi magana ta gaskiya ya kuma soki duk abin da ya gani wanda bai yi masa ba game da zabin hannun jari da hanyoyin da ake ganin za su kawo kudi a mujallar kamfaninsa.

Ba ya tsoron daukar matsaya, misali matsayarsa a kan kara wa masu hali haraji, wanda abu ne da ya saba da ra'ayinsa.''

''Ka san yadda lokacinka yake da muhimmanci. Sa'o'i 24 ne kawai a cikin ranar kowa. Warren yana sane da wannan sosai, saboda haka ba ya tara wa kansa taruka marassa amfani.

Amma kuma yana ba wa mutanen da yadda da su lokacin da ya dace. Yana ba wa masu ba shi shawara na kusa lambar wayarsa, kuma idan sun kirawo shi yana amsa musu kai tsaye.

Anand Chandrasekaran, babban jami'in kula da abubuwan da kamfanin Yahoo ke samarwa ya ce, ''aikinmu mafi kyau yana samuwa ne a lokacin da dalili da sha'awa da kuma riba suka hadu.

Sai dai kuma lokacin da za ka ji wadannan abubuwa uku sun hadu suna zuwa tare kadan ne kuma suna dadewa kafin su zo kuma sai sun dade sosai kafin su kara zuwa.''

Abubuwan koyo sun hada da:

''Dadewar matsala. Daya daga cikin abubuwa na farko shi ne duk wata matsala da kake kokarin magancewa daman ta dade tsawon gomman shekaru, idan ma ba a ce karni ba.

Idan mutum yana kokarin shawo kan wata matsala da ta dade, to hakan na nufin yana horar da zuciyarsa a kan dadewa.''

''Yin kyakkyawan kudiri. Dukkannninmu mun saba da hakan, wato hashashen niyyar mutum. Kawance tsakanin bangarorin sa kai abu ne da yarda da kuma akida daya ke tabbatarwa.

Abu ne da zai ba ka mamaki matuka irin nasarar da za ka gani a lokacin da ka dauka cewa abokan hadakarka suna da niyya mai kyau a duk wata mu'amulla taku."

''Matsaloli na gaba daya. Matsaloli 'yan kalilan ne a yau za a iya cewa mutum zai iya maganinsu shi kadai. Saboda haka hadin kai ba wani abu ne na nishadi ko sha'awa ba, abu ne da ya zama wajibi.''

Sauran kwararrun da suka bayar da gudummawarsu a kan batun na shugabanci sun hada da Steven Thomson: babban jami'in Johns Hopkins Medicine International Baltimore, da ke Maryland a Amurka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The keys to inspired leadership