Ƙasashen da ake ba maza hutun jego har da kuɗi

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Waɗanne hanyoyi huɗu ne da hutun taya mata jego wanda ake ba wa miji ma'aikaci za su iya sa ma'aurata samun ƙarin kuɗi, kuma a waɗanna ƙasashe ne ake samun hakan?

Angela Henshall ta yi mana nazari

Uwaye maza a Ireland za su dara tare da dokin zuwan ranar Mahaifi ta duniya ta shekara mai zuwa; a watan Satumba ne kasar ta bullo da tsarin ba wa maza hutun taya matansu jego na sati biyu tare da albashi.

A dalilin hakan yanzu zama daya da sauran kasashe kamar Burtaniya da Spaniya da Poland da Venezuela da New Zealand da kuma Australia, lkamar yadda kungiyar kwadago ta duniya ta sanar.

Duk da cewa kasar tana baya a kan takwarorinta na Turai da shekaru gommai a kan tsarin kudin da ake biyan na wannan hutu, inda a Iceland da Finland ake ba wa mazaje sama da albashin wata daya a matsayin kudin hutun.

A bisa sabon tsarin mutumin da matarsa ta haihu a Ireland din yanzu zai karbi dala 258 a duk makodaga gwamnati ko da zaman kanshi yake yi ba da gwamnati ko wani kamfani yake aiki ba.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Uba da jariri suna barci

Kasashe biyu ne kawai a duniya da ba sa ba wa matan da suka haihu hutun haihuwa da albashi idan sun haihu, kasashen su ne Papua New Guinea da Amurka- amma kuma akwai wasu tarin kasashen da ba sa ba mazajen da matan nasu suka haihu wani alawus na hutun haihuwar domin su taimaka wa matan nasu.

A dalilin haka mazaje da dama sukan dauki hutu ba tare da albashi ba domin tallafa wa farkarsu ko budurwarsu (ba su yi aure ba) da ta haihu, kuma 'yan kadan ne daga cikinsu suke daukar sama da sati biyu.

Tsawon shekaru abin da aka fi mayar da hankali a kansa na ganin karin mata na shiga aiki, ya ta'allaka ne a kan hutun haihuwa, amma kwararru da dama na ganin amsar za ta iya kasancewa ta dogara ne ga mayar da hankali kan albashin da iyalan ke dauka da kuma kokarin kara alawus da sauran damarmakin da ke tattare da hutun haihuwa da ake ba miji idan matarsa ta haihu.

A kan haka BBC ta duba hanyoyi hudu wadanda za su sa kudin da iyali ke samu ya karu ta hanyar alawus din da ake ba miji na hutu idan matarsa ta haihu.

Albashin uwa zai karu

Akwai shedar da ke nuna cewa tsare-tsare masu kyau na hutun miji za su iya rage gibin da ake da shi tsakanin maza da mata? Scandinavia, wadda ta fi tsare-tsare na hutun haihuwar wanda ya fi dadi a duk duniya ka iya bayar da wata amsa a nan.

Wani nazari da gwamnatin Sweden ta yi ya nuna a duk wata daya da miji ya samu na hutun, albashin matarsa na shekara zai iya karuwa da kashi bakwai cikin dari.

Rage gibin da ke tsakanin maza da mata a fannin samun albashi ya taimaka wa Sweden zama kasa ta hudu da ake da daidaito tsakanin maza da mata a duniya a fannin ilimi da lafiya da shiga siyasa da ayyukan kwadago da sauran fannoni.

Narrowing the gender wage gap has helped Sweden become the fourth-most gender-equal country in the world in terms of labour force participation, education, health and political empowerment among other measures.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

To amma kafin a kai ga cimma haka a kasashe da dama dole ne sai ma'aikatu da kamfanoni sun sauya dabi'arsu ga mazajen da suke da aure hatta a kasashen da suke da tsare-tsare masu kyau.

Wani bincike na kwanan nan da cibiyar nazarin shugabanci ta Burtaniya ta Institute of Leadership & Management, ta yi, ya nuna cewa karfafa yanayin da maza da mata za su rika daukar dawainiya a lokacin da mata ta haihu (samin hutu da albashi), mataki ne mai muhimmanci da zai tabbatar da mata na samun cigaba zuwa manyan mukamai da karin albashi a ayyukansu.

''Amma kuma duk da haka bincikenmu ya nuna cewa shigayen al'adu na kawo cikas ko tarnaki ga shirin fara aiwatar da hutun sati biyu na haihuwa da ake ma mazajen da matansu suka haihu da kuma karin hutun," in ji babban jiami'in kamfanin ILM Charles Elvin.

Karuwar maza masu kula da yara su kadai

Wani dan karamin bincike da aka yi a Sweden ya nuna cewa iyaye maza da suke aiki a manyan kamfanoni masu zaman kansu, wadanda suke daukar hutun haihuwa mai tsawo suna aikin kula da 'ya'yansu har zuwa shekara 12.

Kuma duk hutun da suka dauka yana da alaka da neman zuwa domin kula da 'ya'yan nasu da kansu, maimakon su dogara ga masu kula da yara da ake biya, matan na ci gaba da zuwa aiki.

Bincike daga Amurka da Burtaniya ya nuna muhimmiyar alaka tsakanin iyaye maza da suke daukar hutun taya matansu jego a daidai lokacin haihuwa da kuma shigarsu harkar kula dajariransu da kuma kananan yara a can gaba.

Misali iyaye maza a Burtaniya, wadanda suke daukar hutu na ka'ida kashi 25 cikin dari za su fi shiga renon jariransu kai tsaye kuma kashi 19 ne cikin ake ganin za su shiga shayar da jariransu 'yan wata 8-12 kuma su tashi su kula da jariran da daddare idan yaran sun farka.Wannan ba shi da alaka da kokarinsu na kula da yara kafin haihuwar jariri.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Amfani ga lafiyar mutum zai iya rage kin zuwa aiki

Idan ya kasance matar da ta haihu tana da lafiya sosai a fannin tunaninta hakan zai iya sa ta koma aiki ta samu kudi. A Burtaniya, abin da ya sa maza ke daukar hutun jego na matansu yana da alaka sosai da lafiyar uwa, wata uku bayan ta haihu.

A Faransa bincike ya nuna cewa hutun jego na iyaye maza zai iya sa jariri ya samu karin kulawa daga uban kuma asanadin hakan da wuya uwar ta gamu da wata matsala ta bayan haihuwa.

A wasu kasashen har ladan kudi ake bayarwa

Wasu kasashen bayan albashin da suke bai wa mazajen da suka shiga hutun jegon har ma karin wasu kudaden gwamnati ke ba su idan har sun tafi hutun domin karfafa musu guiwa a kan su tafi hutun.

Misali a Jamus har tsari aka yi na karfafafa wa maza guiwa don su tafi hutun jegon, ta hanyar biyan iyalan wasu kudade na daban kamar kyauta.

A gaskiya ma Jamus na da daya daga cikin tsare-tsare mda suka fi kyau, inda maza da mata suke da dama daidai da juna ta kula da jariri wajen samun hutun wata 12 zuwa 14 a kan albashi kashi 65 cikin dari na albashin mutum, duk da cewa mazaje kadan ne ke daukar hutun idan aka kwatanta da mata.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Four ways paid paternity leave could boost family income