Matan Dubai na kece raini a boye

Hakkin mallakar hoto Nadine Rupp Getty

Mata a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wadda ta ƙunshi Dubai, suna kece raini ta hanyar yin ado na ƙasaita, amma kuma ba kowa ba ne ke ganin adon.

Suna sanya abaya ce (doguwar riga baƙa) wadda ke ɓoye adon. Louise Redvers ta yi mana nazari

Jawaher Alyoha na daukar duk abin da ya shafi ado da muhimmanci matuka da gaske. 'Yar shekara 21 Jawaher wadda dalibar aikin jarida ce daga Hadaddiyar Daular Larabawa tana kashe sama da dala 1,000 a wata a kan tufafi da takalma da jaka, kuma da wuya ta bar gida ba tare da ta yi gyaran gashi mai kyau da kwalliyar fuska ba.

Kamar yawancin matan wannan Daula Jawaher tana dora abaya a kan duk kayan da ta sa sannan ta yafa wani bakin gyale da ake kira shailah idan ta ci ado za ta fita.

Wannan na nufin wasu daga cikin kawayenta da danginta ne kawai za su ga irin katyan da ta yi ado da su a ciki, (yawanci a wurin wani biki ko taro na mata kawai), amma kuma wanna bai hana ta sayen kaya masu tsada ba.

Ta ce, ''mu a wurinmu idan muna son mu ji dadi hankalinmu ya kwanta sai mun san cewa mun sa kaya masu kyau a karkashin abayarmu, na tuna wani malaminmu dan kasar waje da ya taba tambayarmu 'wai ko abaya kadai muke sanyawa, sai na ji kamar 'ina fa!'''

Hakkin mallakar hoto Getty Zubin Shroff
Image caption Wasu 'yan mata biyu sanye da abaya da hijabi suna tafiya cikin wani kanti

Kayan da dalibar aikin darijar ta fi son saye har zuwa yanzu su ne tufafin shahararren mai kayan adon nan na Italiya Valentino, abin da ke raba ta da dala 2,177, amma kuma ta ce tana sayen kaya ma a manyan kantuna irin su H&M da Zara.

Haka ita ma wata dalibar wadda take yawan sayayyar Noura Hassan, mai shekara 24 daga garin Sharjah, wadda tun shekara goma baya take sa abaya ta ce: ''ni idan ina da kudi, ji nake kawai iana son kashe su. Kowane mako sai na sayi wani abu sabo wanda a wata sai na kashe sama da dala 816 a kan tufafi da takalma da wasu abubuwan.

Takalma wadanda su ne ke fitowa fili ana gani idan Noura ta yi ado da abaya su ne tafi saya masy tsada. Amma kuma duk da cewa tufafin da take sa wa ba kowa ke gani ba, su ma ba na wasa take saye ba. Ta ce ''sanya kaya masu kyau na sa in ji farin ciki.

Hakkin mallakar hoto Rubina A. KhanGetty Images
Image caption Wasu jakunkuna masu tsada da aka yi gwanjo a Dubai

Matan kasashen Gabas ta tsakiya, kamar su Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudi Arabiya da Qatar kusan suna daga cikin matan da suka fi ado a duniya. Kuma wannan asha'awa tasu ta yin ado na bunkasa ciniki a yankin.

Binciken da wani kamfanin kwararru Chalhoub Group ya yi ya gano cewa yawanci matar wannan yanki na Gabas ta tsakiya na kashe kusan dala 2,400 a

duk wata a kan gyaran jiki da kayan ado da sauran abubuwa na kawa.

Bunkasa yayin

Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ta fi makwabciyarta Saudi Arabiya, wadda ta fi sassauci, ita ce kan gaba wajen bunkasa wannan al'ada ta ado a yankin Gabas ta tsakiya, inda duk mata ke rufe jikinsu.

Ko da yake ba lalle ba ne mata a Hadaddiyar Daular Larabawar su rufe jikinsu baki daya, amma yawanci suna sanya abaya. Amma sabanin abin da iyayensu mata suke sanyawa, yawancin matasan matan Daular suna sanya abaya ce me budadden gaba.

Dubai, wadda ke da manyan kasuwanni iri-iri, wadda ita ce cibiyar kasuwanci a yankin na Gabas ta tsakiya nan ne kuma ake gasar sarauniyar kyau ta shekara-shekara da ta nuna tufafin ado na yankin.

Abin da ke kara wa wannan al'ada ta ado armashi shi ne yadda attajirai 'yan kasashen Rasha da Turai Da China da kuma Amurka ke zuwa manyan otal-otal na Daular, kila wannan shi ya sa matan yankin suke da sha'awar yin ado.

Sabon yayi

Kwararriyar mai yin kayan ado na FMM a Daular Fatma AlMulla, ta ce: "mata a nan sun damu da abin da za su sa. Ba za ki sa duk abin da kika ga dama ba a karkashin abayarki, ya za ki yi idan wani abu ya rike miki ita har ta yage? Dole ne ki yi hankali!''

"kwalliya na da muhimmanci a nan," in ji Zahra Lyla mai rubuce-rubuce a intanet. Ta ce "idan mace tana sanye da abaya mai budadden gaba, za ta tabbatar a duk lokacin da iska ta daga mana rigar, a ga kayan da ta sanya a ciki masu kyau ne sosai."

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawancin matan kasashen yankin Gabasta tsakiya suna kashe kusan dala 2,400 a wata, a sayen tufafi da kayan ado

Haka kuma duk da cewa yawancin matan Daular suna rufe jikinsu a bainar jama'a, suna yawan halartar bukukuwa na mata zalla, in ji Lyla wadda ita ma 'yar Daular Larabawar ce amma kuma ba ta sanya abaya.

Ta kara da cewa idan matan suka kadaice da kawaye da 'yan uwa, suna son nuna irin adon da suka yi, su nuna irin matsayinsu a kayan adon da ake yayi

Abin alfahari

Abin da mata suke ado da shi, ko suna fito da shi ko boye shi suke abin alfahari ne a wurinsu, kamar yadda Effa Al Dabbagh wadda tana daga cikin wadanda suka kirkiro da abaya mai budadden gaba, wadda kuma tana da shagonta na sayar da tufafi da sauran kayan ado a Dubai ta bayyana.

Ta ce ''matan da suke sanya abaya suna matukar alfahari da kayansu, na san idan na sa kaya masu kyau kuma na ci ado, ina jin dadi, to kaina nake yi wa hakan ba wasu ba

Al Dabbagh, wadda ainahi daga Saudi Arabiya take, ta ce kamar dai a kasashen Yammacin duniya duk abin da mutum ya sa ya dogara ne da yanayi.

Ta ce, ''misali idan 'yan mata suna kallon wani fim na Amurka da kawayensu idan suka rufe kofa suka cire abayarsu za ka ga aabin da suka sa a ciki zai iaya kasancewa kaya ne masu kyau kamar jins me kama jiki da 'yan kanan riguna masu kama jiki.''

Afnan Kazim, dalibar aikin jarida mai shekara 21 daga Dubai, wadda ke kashe kusan dala 1,361) a wata a kan tufafi da sauran kayan ado ta ce, "duk wata yariya tana son ta yi ado ta yi kyau, musamman idan tana tana zuwa yawo da kawaye. 'Yan mata a nan suna son kayan fitattun kamfanoni, yawanci suna sayen kayan saboda sunan ba wai don ko suna son kayan ne ko kuma kayan na da kyau.''

Gasar ɓoye

Briton Vicky, wadda ba ta son bayyana sunanta na ainahi ta fara sanya abaya shekara shida da ta wuce bayan da ta Musulunta kafin aurenta da wani dan Daular Larabawar a Dubai.

Vicky mai shekara 33-year-old, wadda ke tafiyar da wani kamfanin daukar ma'aikata ta ce ba abu ne mai sauki ba ka koyi yadda za ka rika sanya kaya kamar matar auren Hadaddiyar daular Larabawa.

Ta ce, ''zan iya cewa gasa ce ta sirri tsakaninmu kuma wasu matan suna ado ne domin wasu matan su ga abin da suka sa. Ta ce duk dacewa ita za ta iya sanya wasu kayan a gida idan tana tare da 'ya'yanta, kamar tsukakken wando ko Jallabiya, Vicky ta ce ba za ta taba tunanin karbar baki a gidanta ko zuwa gidan wasu ba ba tare da ta yi wa fuskarta kwalliya ba da kuma gyara gashinta. Ta kara da cewa ''mata na cikin matsin lamba a nan su yi ado sosai.''

Gasar karshe

Karshen ado a Hadaddiyar Daular Larabawa, shi ne a wurin bukukuwa, lokacin da gasa tsakanin mata kan ado ke kai wa kokoluwa. A bisa ala'ada maza da mata suna bikin aure ne kowa daban, to a lokacin bikin ne a zaurukan bikin ake cire abaya, inda za ka ga kaya na-gani-na-fada masu tsadar gaske

Bukukuwan kusan lokaci ne na nuna dukiya, inda yawanci za ka ga an gayyaci baki sama da 500, kuma komai ya ji ba karanta ba gajiyawa. Duk da cewa ana yin ado da kayayyakin manya kuma fitattun kamfanon tufafi, amma yawancin mutane suna tsara tufafinsu ne da kansu yadda za a dinka musu da ado yadda suka tsara.

''Biki lokaci ne na nuna kasaita. Mutane 2,000 ne suka halarci nawa, muna da dangi da yawa,'' in ji AlMulla tana dariya . "abin da ka sa na da muhimmanci. Mutane suna son nuna kansu, ba ta wata mummunar hanya ba, suna dai son su nuna cewa dansu ko 'yarsu ta yi aure kuma kowa yana taya su wannan farin ciki da murna."

Vicky ta jkara da cewa: "mutane ba sa ma ko wani dar-dar ko damuwa kan kashe dala 2,177 a kan kaya daya da za su sa ranar biki kawai, kayan da daga wannan rana za a ajiye su ba za a sake sanya su ba. Yadda abin yake kenan kawai."

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The high-end, designer fashion hidden beneath the abaya