Yadda za a fi saninka a wurin aiki

Hakkin mallakar hoto iStock

Akwai hanyoyi da dama da za a san ka a wurin aiki a yau. Wasu za su sa ka farin jini wasu kuwa za su sa ka yi ƙaurin suna ne ko ma ka gamu da fushin shugabanka ko waɗanda suka ɗauke ka aiki.

Wasu ma'aikatan ma bisa kuskure ne kawai ake saninsu.

Wannan batu na yadda za a san mutum a wurin aiki shi ne abin da fitattu a shafin intanet na mua'mullar ma'aikata Linkedln suka tattauna a kai a kwanan nan, abin da ya kama daga munanan dabi'un masu neman aiki har zuwa ga hanyoyin da suka fi dacewa a ce shugabn wurin aikinku ya san da kai.

Ga wasu daga cikin abubuwan da suka ce

Michael Fertik, babban jami'in kamfanin Reputation.com a rubutansa ya ce, ''a duniyar da masu daukar ma'aikata suke kara kusantar masu neman aiki, Fertik ya yi tambaya ne cewa ko mutanen da ke neman aiki sun saba da wannan tsari na wannan zamani na tattalin arziki?

Ya gabatar da hanyoyi uku da masu neman aiki ke nuna dabi'unsu ta hanyar da ba za su jawo hankalin masu daukar mutane aiki ba ko kuma masu daukar hayar mutane a aiki. Daga cikinsu akwai:

''Yadda da na'ura. Sanya takardarka ta neman aiki a shafin intanet na kamfanin ka ce hakan ya isa babban kuskure ne. Kana bukatar aika wa kamfanin takardar neman aiki ta wata hanyar bayan ta intanet, domin dogaro da intanet din kamar ka sanya kwandalarka ne cikin wani bakin rami, ka zo kana nemanta.'' kamar yadda ya rubuta.

''Sakarci a shafukan sada zumunta da muhawara na intanet. Sama da kashi 90 cikin dari na masu daukar mutane aiki suna ziyartar shafin sada zumunta na mai neman aiki a wurinsu. Yana da kyau a matsayinka na mai neman aiki ya kasance kana mu'amulla da shafukan sada zumunta, sai dai idan kana abubuwan da ba su dace ba a cikinsu. Kuma kada ka taba dauka cewa hakan ba zai faru a kanka ba a'a zai iya faruwa,'' in ji Fertik.

James Caan, babban jami'in kamfanin Hamilton Bradshaw Ltd

Ya ce, "dukkaninmu muna son cigaba a rayuwarmu, mu samu cigaba a aikinmu cikin sauri, wanda hakan na nufin mutum ya tashi tsaye, ya zarta sa'a

Amma a irin wannan lokaci na gogayya wannan abu ne mai wuya sosai ba kamar yadda ake gani ba," Caan ya ce a kasidarsa mai taken 'matakai biyar da za ka sa shugaban wurin aikinka ya san da kai idan kana ganin aikinka ba ya cigaba.

Mataki na farko: "ka rika nuna kwazo a aikinka. Kowane shugaba yana son ya ga ma'aikacin da yake dagewa a aikinsa tare da sadaukar da kansa, ba wai mutumin da kawai zai yi mafi karancin aiki ba.

Wannan ba wai lalle yana nufin dadewa fiye da kowa a ofis ba, abin da hakan ke nufi ka dade din idan bukatar hakan ta taso. Ka tabbatar duk aikin da aka ba ka ka kammala shi a kan lokaci kuma yadda ya dace, idan ma za ka iya ka yi fiye da yadda ake sa rai," Caan ya ce.

Abu na gaba kuma? "ka zama mai azama. Daukar aikinka da muhimmanci zai sa a san da kai sosai a wurin aikinku. Ba manajan da zai ji dadi ko alama a ce sai ya rika tunatar da ma'aikatansa cewa akwai aikin da ba su gama ba ko wanda lokacinsa ya wuce.

Ya rubuta cewa, ''idan ka dauki aikinka da muhimmanci ba kai kadai abin zai shafa ba hatta sauran abokan aikinka ma zai yi tasiri a kansu domin za ka ga ana walwala aiki na gudana a ofishin naku."

Sauran matakan da Caan ya bayar da shawara sun hada da zama mai kirkira, ka rika bayyana burinka kuma ka rika nuna juriya da sabo da duk wani wuri da aka tura ka aiki kamar daman a nan kake.

Sauran abubuwan da masanan suka yi rubutu a kai:

John Taft, babban jami'in kamfanin RBC Wealth Management, a rubutunsa a kan muhimmin mataki da iyaye maza za su dauka, ya yi mamakin shawarar da Hunter Mahan, dan wasan kwallon lambu (golf), wanda ke kan gaba a wata fafatawa wadda zakaranta zai ci sama da dala miliyan daya, amma kwatsam ya yi watsi da wasan ya tafi wajen matarsa a asibiti wadda za ta haifi dansu na farko.

Matakin da Mahan ya dauka kamar yadda Taft ya rubuta, ''ya dauki hankalin mutane da dama saboda a lokacin yana kan hanyarsa ta cin wannan gasa wadda ke da wannan kyauta ta makudan kudade wadda 'yan wasa kadan ne suka taba cinta.

Dalilinsa na yin wannan abu ya nuna akalla a wurina, cewa muna mamakin yadda mutum zai ba iyalinsa muhimmanci a kan sana'arsa.''

Mark Tercek, shugaban kamfanin Nature Conservancy kuma tsohon ma'aikacin Goldman Sachs ya yi magana ne kan wani muhimmin darasi da zai iya samar da shugabanci na gari a harkar kasuwanci da bunkasa aikin ma'aikata.

Abin kuwa shi ne na wasikar email wadda za ka ga akwatin mutum yana cika yana batsewa. Jeff Weiner, ya bayar da shawarwari bakwai kan yadda za ka kula da email dinka ba tare da ka samu matsala ba, abin da ya hada da sanya wani lokaci na duba wasikun, da rage yawan email din da kake aikawa da kuma takaita bayanan duk wasikar da za ka rubuta ba tare da ka cika ta da rubutun ba gaira ba dalili ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The right way to get noticed in your career