Ka san matsalar mutane masu basira?

Hakkin mallakar hoto Jeff Vinnick Getty

Matsalar mutane masu basira da baiwa ita ce yawanci suna ɗaukar kansu sun fi kowa sani da iyawa. Idan za ka ɗauki mutane aiki, ko za ka ciyar da wasu ma'aikata gaba, za ka zaɓi waɗanda suka fi kowa basira ne ko? To tsaya kada ka yi hanzari!

Ga nazarin Sydney Finkelstein

Basira na daya daga cikin abubuwan da ake bukatarsa dan kadan ka dace da aiki. Idan ka wuce haka, ya kasance kana da basira mai yawa to hakan zai iya zama matsala.

Misali ka duba tsohon kamfanin makamashi na Enron da ke Amurka, wanda aka san shi da tarin ma'aikata masu basira sosai. Duk da kwarewar ma'aikatan, sai suka kasance masu izza da girman kai, wadanda suke yin abu kai tsaye, har hakan ya sa kamfanin ya yi asarar biliyoyin dala. Kamfanin ya ma durkushe a 2001.

Shin dole ne ma in hada masu basira a matsayin manajojina?

Matsalar mutane masu basira

Matsalar mutane masu basira ita ce suna daukar kansu sun fi kowa sani. Kila haka ne. Amma kuma wannan ba ya taimaka musu idan suna kokarin shawo kan mutane su sayi duk abin da suke sayarwa.

Misali ina koyar da wata babbar jami'a wadda a ko da yaushe tana gaba da sauran abokan karatun nata a wurin iyawa, ko kuma in ce haka take daukar kanta.

Daya daga cikin manyan kalubalen da ta fuskanta shi ne, ta gano cewa sauran manyan jami'an ba lalle ne suna kallon duniyar nan kamar yadda take ganinta ba.

Wannan na nufin sai ta bata lokaci ta ilmantar da su domin su zama kan hanya daya da ita idan har tana son aikinta ya tafi daidai.

Idan ka san amsar da ta dace, yawanci ba ka yarda cewa wani kuma hankalinsa wani wuri yake tafiya wato bai san wannan amsa ba, ta yadda zai bi hanya ku tafi tare.

Abin takaicin shi ne kamfanoni ba haka suke aiki ba. Musamman idan kana aiki da takwarorinka, wadanda ba ka da iko da su, hanya daya da za ka sa a bi tsarinka ita ce ka yi kokarin shawo kansu. Domin maganar ka nuna musu iko ba ta taso ba, saboda ba za ta yi aiki ba.

Abin mamakin shi ne wani lokacin mutumin da ya fi basira da kwarewa zai iya cike gurbin daya daga cikin manajojin da basu dace ba. Za ka ga misalin irin wannan a wasanni, inda za ka ga kwararrun 'yan wasa da suka yi ritaya sun kasa jagorantar kungiya da kyau saboda a yanzu suna kula da wasu mutane ne wadanda ba su da baiwa da basira irin tasu.

Tsohon kwararren dan wasan kwallon gora na kasar Kanada (Canada) Wayne Gretzky, wanda ya yi ritaya yana da tarihin cin kwallo fiye da duk wani

kwararren dan wasan kwallon gora a tarihi, abin mamaki ya kasa tabuka komai a matsayin mai horas da wasan.

Haka shi ma Michael Jordan, wanda ana ganin kamar babu wani dan kwallon kwando a tarihin duniya da ya kai shi, shi ma ya kasa samun nasarar horarwa ko jagoranta ko kula da wata kungiya ko hukuma ta kwallon kwando.

Kamar yadda za a ce mun bar wadanda suke ganin su ne suka fi kowa basira su je kasuwa da abin da suke gani shi ne ya fi kyau da mutane za su saya. Na tuna lokacin da nake tattaunawa da manajoji a kamfanin Creative Technology da ke Singapore, jim kadan da kamfanin Apple ya bullo da iPod.

Kamfanin na Creative yana da na'urar MP3 wadda ta fi iPod kyau da komai, amma kuma mutane sun fi son iPod, abin da ya ba wa jami'an kamfanin na Creative matukar takaici da mamaki. Sun kasa sanin dalilin da mutane da za su nuna wannan wawanci!

To amma yadda abu yake shi ne ba a ko da yaushe ba ne fasahar da ta fi kyau take fin samun karbuwa ba, kamar yadda ba a ko da yaushe ba ne mutanen da suka fi basira su ke yin nasara ba.

Ba a fannin basira ba ne kadai inda ake samun wannan akasi na wanda ya fi yawa ya kasa yin nasara. Misali , za a iya cewa abu ne mai kyau a rika rage yawan lokacin da jami'an kamfani za su rika sauraren mutanen da ke sayen kayansu da suke bukatar taimako ta waya?

Ina maganar ingancin shawarwarin da jami'an suke bayarwa, ya mutanen suke daukar shawarwarin, ko ma shawara ce mai kyau a ma yi tunanin kara saurin sauraron?

Kamfanin sayar da takalma ta intanet da ke Amurka, Zappos, yana kyautatawa ma'aikatansa da suka dade ta waya suna sauraren kwastomominsu da suka kirawo waya domin su yi wata tambaya a game da takalman da suke son saya

A wurin kamfanin na Zappos, duk yadda kwastoma ya ji an kula da shi ta waya, kamfanin na ganin hakan wani abu ne da zai karfafawa mutum zuciya a kan kayan kamfanin kuma wannan riba ce ga kamfanin.

Idan aka karfafa wa ma'aikata guiwa da su rika kula da kwastomomi ba tare da wani bata lokaci ba, taken nuna muhimmancin masu sayen kayan kamfanin , wanda ake cewa kwastoma shi ne farko da sauransu duk surutu ne da dadin baki da ba su da wani muhimmanci a wurin ma'aikata

Kuma kada mu manta da illar da ke biyo bayan irin wannan al'ada. Ma'aikatan da lalle suka damu da aiki a kan haka sauya wurin aiki suke yi, wannan sai ya sa ma'aikatan da aka karya musu guiwa wadanda suke aiki da kyau su cimma burinsu.

A karshe za ka samu abin da kake so, amma kuma ka rasa saboda tunanin cewa abin da yake da yawa ya fi wanda ba shi da yawa kyau.

Kana iya kiran hakan cimma burin da ba shi ne ba

Neman kari zai iya kasancewa babban burin zamaninmu amma matsalolin da ke tattare da wannan gajeren tunani na bukatar kulawa sosai.

Dogara da wadanda suka fi basira da baiwa da kuma kwarewa domin su jagoranci mutane abu ne da za a ga a manufa ya fi dacewa fiye da a aikace.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The problem with smart people