Yadda za ka daina yaudarar kanka

Hakkin mallakar hoto Getty

Da farko Eleanor Bain wadda aurenta bai daɗe da mutuwa ba ta ɗauka cewa a ƙarshe dai ta dace da mutumin da take fatan samu ya zama mijinta a rayuwa. Amma bayan ta ƙi jin maganar ƙawayenta ta sha mamaki.

Ta koma wani sabon birni ne, tana neman aiki domin ta yi sabuwar rayuwa tare da 'ya'yanta mata biyu, a lokacin da ta fada kogin soyayya, kamar yadda ta dauka.

Duk da cewa suna da inda ra'ayinsu ya zo daya akwai inda suka sha bamban da dama. Wani lokaci sukan shafe sa'o'i masu yawa suna ce-ce-ku-ce da yi wa junansu ihu.

Idan ta waiwayi baya sai ta ce, ta yaudari kanta ne a kan soyayyarta da wannan sabon miji nata a lokacin da suka fara haduwa suke soyayya. Ta ce, ''ba wai ba ka son ganin gaskiyar lamari ba ne, ba ka ganin ainahin yadda abin yake ne a zahiri, domin ka makance.''

Ba za ta saurari kawayenta ba ne sam-sam a lokacin da suke gaya mata gaskiya da ba ta shawara cewa za fa a iya samun matsala idan suka yi wannan aure. Ta ce na dage na yi duk abin da zan iya na shawo kansu cewa mutumin ba shi da matsala, kuma ya dace da irin wanda nake so.''

Me ya sa muke yin haka? Yaudarar kai hanya ce ta kare kai daga gaskiya mai daci. Wannan shi ke sa mu nuna cewa mu gaskiya muke yi, amma kuma duk da haka mu saba ka'ida.

Misali sai mu ce wai muna so mu tara kudi amma kuma sai mu bige da yin kishiyar hakan, ko mu makale mu ci gaba da aiki da wani kamfani ko da an tsallake mu wurin karin girma an yi wa wasu na bayanmu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kana ƙin gaskiya? Za ka iya cewa a'a

Yaudara za ta iya sa mutum ya ji dadin al'amuransa na yau da kullum amma kuma akwai ranar kin dillanci, kamar yadda Cam Caldwell, farfesa a jami'ar Purdue ( North Central) a Indiana da ke Amurka wanda ya yi shekara da shekaru yana bincike a kan al'amuran da suka shafi yaudarar kai.

Ya fassara yaudarar kai a matsayin, ''rike ra'ayi biyu kishiyoyin juna ba tare da yarda da bambanci ko sabanin da ke tsakanin ra'ayoyin ba."

Illar yaudarar kai ta hada da fadawa cikin hadarin wariya, idan ka kasa kulla dangantaka da sauran jama'a saboda ka fi fifita ra'ayinka a kan abin da yake shi ne na gaskiya, kamar yadda Caldwell ya rubuta kenan a wata kasida, yana mai bayar da misalin likitan masu tabin hankali na Amurka, M Scott Peck.

Ga wadanda suke son kin binne kansu a kasa ( rasa kunya beran tanka), ku yi wa kanku wannan tambaya: Wannene mafi illa - dan labari maras dadin ji a kan ainahin halin da kake ciki, ko kuma yadda aka saba yi, a gwama karya da gaskiya, lamarin da zai kai ga rabuwar aurenku da asarar kudinka ko aikinka?

Ya yin da yaki da yaudarar kai ke zama gwagwarmaya idan a kan maganar soyayya ce , amma kuma kin maganin matsalar ka iya shafar duk wasu al'amura na rayuwarka

Ranar kin dillanci

Yawancinmu mun taba yaudarar kanmu a rayuwa. ka duba abin da ya shafi kudadenka. Za ka dauka cewa kudaden da kake da su a rubuce a takarda ba wata tantama kai me kudi ne kana da kwanciyar hankali saboda ka mallaki wannan kudi mai yawa.

Amma idan akwai maganar yaudarar kai da mafarki (misali na zama attajiri ko mai kudi), to sai labari ya sha bamban, in ji Kathleen Gurney, shugabar kamfanin 'Financial Psychology Corporation' da ke Sarasota a Florida a Amurka.

Ita ta ma ga kwararrun masu bayar da shawara kan harkokin kudi da suka kasa ganin gaskiyar lamari, duk da dimbin kwarewar da suke da ita kan kula da kudi.

Ta bayyana wani mai bayar da shawara kan tsimi da tanadi wanda bai iya hangen hadarin rasa gidansa ba, kan rashin biyan kudin gidan nasa. wasu kuma sun kasa ganin illar tara bashi na tsawon shekaru, in ji Gurney.

Gurney ta ce, "yaudarar kai tana da mataki-mataki kuma tana iya yin tsanani." Matakin farko shi ne kin gaskiya saboda dacinta, kamar yawan jinkirin biyan kudin da ake binka kamar na wuta ko ruwa da makamantansu, ko ka tura mutum banki da takardar karbar kudi (cheki) amma a tarar ba kudin.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idan ba ka kallon haram ba ka sauraren haram ba ka kuma faɗin haram, za ka iya gamsar da kanka cewa ba ka da wata matsala?

Yaudarar kai nau'i na biyu ita ce ta rage girman abu. A wannan matakin, mutum zai yarda da gaskiya amma zai ce ba komai ya nemi yin 'yan dabaru.

Ya ce, ''gaskiya ne (wannan matsala na faruwa), amma tun da dai ina sa isassun kudi a bankina ba wata matsala da za ta faru, a ce ba ni da kudi a asusun.''

Nau'i na uku na yaudarar kai shi ne kin daukar alhakin matsala ko laifi. Wannan shi ne lokacin da ka yarda da matsala amma kuma ka dora alhakinta a kan wani.

Ida za ka ce "na sani, amma ba laifina ba ne saboda ina fama da aiki, kuma ina da ayyuka da yawa…"

A nan shawarar Gurney ita ce: ''Ka tuntubi wani abokinka ko wani kwararre ku yi nazarin abin da ke tafiya daidai a harkokin kudinka da kuma wanda ba ya tafiya daidai, har ku gano bakin zaren al'amura."

Wata shawarar kuma ita ce ka tsaya ka yi karatun ta-natsu ka yi nazarin ainahin matsayin arzikinka domin ka fahimci dabi'arka da kyau.

Sauran dabaru: Ka tsaya ka zayyana a rubuce abubuwan da ka ce kana so da ainahin abin da kake yi, ko kuma kamar yadda Gurney ta ce, ka rubuta abubuwan da kake sha'awa a game da harkokinka na kudi a wasu katuna, ka jera su daya kan daya sanna ka duba ka ga ko kana da wata dabi'a.

Alama ta bayyana

Yaudarar kai ba ta tsaya ba ne ga harkar kudi ko soyayya kawai. Abune da ke iya shafar mutane da dama a duk tsawon rayuwarsu ta aiki. A nan ma abu ne mai sauki ka yi sake mafarkinka ya rufe maka ido ka kasa ganin gaskiya.

Abin da ya faru da wata ma'aikaciya kenan da ta zo neman shawara wurin Nadine Gimbel, kwararriyar mai bayar da shawara ga ma'aikata a Frankfurt da ke Jamus, wadda kuma ita ce babbar jami'ar tallace-tallace a kamfanin RF/F Raum Fuer Fuehrung, kamfanin da ke bai wa kamfanoni da hukumomi shawarwari kan matakan aiwatar da sauye-sauye.

Ta taimaki wata mata da ke matsayin matsakaiciyar babbar jami'a a wani babban bankin Jamus, wadda take korafin kin kara mata girma, duk da yadda take dadewa a wurin aiki da kuma dimbin aikin da take yi.

Matar mai shekara 40 da 'yan kai, ba ta da cikakkiyar masaniya kan inda take son komawa da aiki da kuma dalilin da take son komawa can. Haka kuma tana zaman jiran wani ya lura da ita cewa tana aiki da kyau a bankin. Wannan makantar da ta sanya wa kanta ta dankwafar da aikinta.

Tana yaudarar kanta ne da cewa tana jiran wani ya lura cewa tana da kwazo, in ji Gimbel, wadda ta zauna tare da matar suka yi aikin tsara abin da take so da kuma gaya wa shugabarta lamarin.

''Ta yi hakan kuma shugabar tata ta fahimci halin da take ciki da abin da take bukata."

Shawarar Gimbel ga wadanda suke kokarin kaucewa matsalar da suka gani ta tunkaro su karara a wurin aiki, ita ce da farko sai fara neman ainahin sanin abin da suke bukata.

Daga nan sai ka dauki alhakin yin abin da ya zama wajibi, kamar sanar da abin da kake so, ko barin aikin da ba ka samun biyan bukata.

Gimbel ta ce, ''rayuwa ta kunshi sauyi, kuma mu, mun fi son tsayawa inda muke, wato kan abin da muka saba da shi, saboda muna jin tsoro. Yawanci muna nadamar matakan da ba mu dauka ba ne, ko sauyin da ba mu yi ba. Ba mu san inda za mu iya kasancewa ba ( cigaba) idan da ba ma jin tsoro.''

Neman kwarin guiwa

Ba shakka ka ga gaskiya karara a kanka kuma ka yarda har ka yi aiki da ita abu ne da ke matukar bukatar karfin hali da jajircewa. Bain ta fara ganin alamar matsalarta ne lokacin da ta ga sabon mijinta ya soki lamirin 'ya'yanta mata.

Ta ce, ''ina jin kamar abin nan ne da ake cewa kaikayi koma kan mashekiya, idan kwatsam ka fahimci cewa wannan abin fa ba shi da kyau,'' in ji matar wadda ta kara da cewa, '' ta ji ''tsananin ciwo'' kuma ta ji tana son guduwa domin ''cetar rayuwarta'' lokacin da a karshe ta fahimci gaskiyar da take ki.

''Abin za ka ga kamar kwatsam an yaye labulen da ke gabanka ne, sai ka ga ainahin zahirin gaskiya.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to stop lying to yourself