Yadda tsuntsaye suke iya ganin gabansu

Hakkin mallakar hoto Swallowtail Garden Seeds cc by 2.0

Manyan agwagwi (swan) suna kada fuka-fukansu har sau biyar cikin dakika daya kacal amma kuma duk da haka kansu na tsayuwa wuri daya. Ko ya hakan ke iya kasancewa?

Melissa Hogenboom ta bincika.

Ka san yadda abin yake ka tashi a cikin iska jikinka na fuffuka ko'ina hakan na sa kanka na jijjigawa Ba ta yadda za ka iya ganin inda ka dosa. Za ka ga komai ya daburce maka.

Abu ne mai tayar da hankali matuka idan da za mu iya tashi.

Ko alama lamarin ba haka yake ba a wurin tsuntsaye masu tashi. Suna kada fuka-fukansu wasu da gudun tsiya kuma ba tare da wata matsala ba ta ganin inda suka dosa.

Ba su da wata matsala ko kadan wajen ganin inda suka tunkara kuma ba tare da wani kuskure ba inda suka nufa nan suke zuwa, saboda ta wani bangaren akwai kyakkyawan tsarin gudanarwa tsare tsakanin ido da kai.

''A takaice suna tsari ne wanda tashinsu yake dacewa daidai da kadawar kowanne motsin fuka-fukinsu,'' in ji David Lentink na Jami'ar Stanford da ke California a Amurka.

Ana iya ganin wannan sosai musamman a wurin tsuntsaye masu dogon wuya kamar manyan agwagwi (swan ko geese).

Agwagwa nau'in giz (geese) ta fi nuna wannan alama, domin za ka ga idan ta zo sauka za ta juya jikinta har sai ta kai tana tashi sauka a juye (sama a kasa). Kuma a wannan yanayin za ta juya kanta ta yadda idonta zai iya gani gabanta kai tsaye.

A yanzu masana kimiyya sun dukufa domin gano yadda tsuntsaye irin wadannan manyan agwagwi suke iya gani sosai a yayin da suke tafe.

Abin mamaki, Lentink, ya bayyana cewa ba wani abu mai yawa aka sani ganme da yadda tsntsaye suke motsa kansu ba idan suna shawagi.

Za a ga wannan kamar wata tambaya ce mai sauki, amma idan ka duba za ka ga ba karamin aiki muke ba idan muna son tsayar da kanmu a lokacin da muke gudu. Dole ne sai mun yi hakan idan dai har muna son idonmu ya gani da kyau.

''Hakan yana da muhimmanci ko ma dai a ce wajibi idan har ana zilliya ko kakkaucewa cikin sauri, tsuntsaye su ne babban misali na wannan,'' in ji masanin.

Da suka kwaikwayi yadda agwagwa nau'in swan take yi yayin da take shawagi a kogi, Lentink da abokan aikinsa sun fahinci cewa agwagwar tana amfani da wuyanta ne ta tsayar da kanta kamar yadda tsarin mota na sufirin chokzoba (shock absorber da Ingilishi) da sauran abubuwan da motar ke zaune a kansu da ke daidaita motsinta suke yi, haka ita ma take amfani da wuyanta.

Yanayin yadda wuyan manyan agwagwin yake ne ya sa suke iya tsayar da kansu ba tare da yana kadawa ba yadda za su kasa gani da kyau.

Masu binciken sun wallafa sakamakon wannan bincike ne a mujallar kimiyya ta Royal Society Interface.

Yawancin tsuntsaye suna da linki uku na yawan kashin bayan da mutum yake da shi, kuma agwagwa nau'in swan tana da jijiyoyi 200 a kwane bangare ba wuyanta.

Masanan suna ganin za a iya amfani da irin wannan tsari na halitta a kirar jirgin sama maras matuki ta yadda duk na'urar daukar hoton da aka makala masa za ta iya daukar hoton kasa ba tare da wata matsala ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How birds see straight