Beraye za su iya cetar abokansu a ruwa

Hakkin mallakar hoto Life on white Alamy
Image caption Dan uwa rabin jiki

Idan ruwa zai ci wani bera za ka ga wani ya kai masa dauki ya cece shi, kamar yadda wani bincike ya gano.

Melissa Hogenboom za ta ba mu bayani

Cetar mutumin da ya shiga wani hatsari ko hali na mutuwa abu ne da muke yi ba tare da mun sani ba.

To amma wannan zuciya ta tausayi ba ga dan-adam ta tsaya ba. Birai da yawa su ma suna cetar junansu.

Su ne dabbobin da suka fi kama da mu, saboda ba mamaki halittun farko da suke da irin wannan kamanni sun yi irin wannan dabi'a.

Ma'ana zuciyarmu ta ceto wasu al'ada ce ko dabi'a ta tun asali wadda dan-adam na zamanin nan ya gada.

Wannan dabi'a ba mamaki ta dade a duniya. Dabbobi kamar beraye ba su da dangantaka da mu a kusa-kusa, kuma idan muna da wata dangantaka da su ta asali ta kasance ne watakila miliyoyin shekaru da suka wuce.

Amma kuma duk da haka wani sabon bincike ya nuna cewa beraye suna cetar abokansu daga ruwa(kogi).

Hakkin mallakar hoto Kim Taylor npl
Image caption Beraye na da tausayin juna

Idan ruwa zai ci wani, sai wani beran ya yi sauri ya yi yadda zai sa masa wani abu da zai bi ya je wurin da zai tsira inda ba ruwa.

Suna kuma yin hakan, ta yadda za ka ga sun bar abin da za su taba abinci ya zo musu, sai su kama abin da suka san za su iya turawa abokin nasu ya tsira daga ruwa.

Saboda haka berayen suna da dabi'ar haduwa domin taimakon juna ko da kuwa babu wani lada da za su samu. Cetar dan uwansu bera abu ne mai matukar muhimmaci a wurinsu.

Darasi yana taka muhimmiyar rawa a nan, domin idan beran da zai yi ceton ya taba shiga irin wannan hali ko hadari, to za ka ga aikin ceton ya fi sauri.

A gwajin kimiyyar da aka yi, an gano cewa idan babu wani da ke bukatar taimako ko kuma an maye beran da ke cikin hadarin da wani abu maras rai, berayen sun sani za ka ga ba su danna wannan abin (sanda) na ceto ba.

Hakkin mallakar hoto arco images gmbh alamy
Image caption Muna rayuwa ne da tallafin abokanmu

Binciken wanda aka wallafa a mujallar basirar dabbobi (Animal Cognition) ya nuna cewa kila beraye suna da ilimin sanin halin da wani yake ciki, sannan suna iya gane cewa wani na cikin hadari kuma su so su taimaka masa.

Fahimtar cewa bera yana iya sanin halin da wani ke ciki zai iya bude hanyar yin wadansu bincike-binciken kan dalilin mu'amulla.

''Sanin halin da wani ke ciki na daya daga cikin muhimman dabi'unmu na mu'amulla ko taimakon juna,'' inji jagoran binciken Nobuya Sato na Jami'ar Kwansei Gakuin da ke Japan.

Idan har beraye suna da irin wannan hali na sanin abin da wani yake ciki, za mu iya fara binciken yadda dabi'ar ke aiki a kwakwalwarmu.

Wannan zai taimaka mana fahimtar yadda mu'amulla ta samo asali da kuma yanayin tunanin dan-adam inda wani yake iya kasancewa ba shi da wannan dabi'a.

Sato ya ce wannan dabi'a ta rabu kashi biyu ta tausayi da kuma ta kwakwalwa ku tunani.

Sabon binciken musamman ya nuna cewa beraye suna da wannan dabi'a ce ta tausayi, wato dabi'ar jimamin halin da wani yake ciki.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Rats will save their friends from drowning