Kare ya san mayaudari

Hakkin mallakar hoto

Ba a dadewa ana yaudarar kare, kuma yana dena yarda da mutumin da ba shi da tabbas.

Ga bayanin Melissa Hogenboom

Za a ga cewa karnuka ba su da wayo idan suna bin jelarsu suna kokarin kama ta, amma duk da haka dabbobi ne da suke da wayo. Dabbobi ne da suka san mu'amulla da mutane da kuma 'yan uwansu.

Bincike da dama da aka yi ya nuna cewa suna iya gane yanayin da mutum yake ciki ko na damuwa ko farin ciki kamar yadda wani bincike da aka yi kwanan nan ya nuna, kuma suna iya nuna kishi ma.

Yanzu an gano cewa ga alama suna iya sanin idan wani mutum ba abin yarda ba ne.

Da zarar kare ya gane mutum ba abin yarda ba ne sai ya daina bin umarnin da yake ba shi.

Hakkin mallakar hoto Victoria Standent
Image caption Karnuka suna yarda da masu su

Da dadewa ansan cewa kare yana fahimtar abin da ake nufi idan mutum ya nuna masa wani abu.

Idan mai kare ya nuna wa kare wajen da kwallo take ko sanda ko abinci, karen zai yi yaje wurin ya duba.

Wannan binciken na kwanan nan ya nuna cewa karnuka suna da saurin fahimta idan wannan nuni da mutum ke masa na yaudara ne.

A nazarin da aka wallafa a mujallar tunanin dabbobi (animal Cognition), wani ayarin masu bincike karkashin jagorancin Akko Takaoka ta Jami'ar Kyoto da ke Japan, sun gabatarwa karnuka 34 nuni-nuni har kashi uku.

Ma'ana suna nuna musu su je wani wuri domin dauka ko ganin wani abu.

A zagayen farko gwajin da ake yi na nunin ana nuna musu inda aka boye abinci a cikin wani misali kwano.

Amma a zagaye na biyu idan aka nuna musu wuri suka je sai su ga ba abinci, ba komaia cikin kwanon.

A zagaye na uku na nunin, shi wannan mai gwajin yana nuna musu su je wurin kwanon da yake da abinci.

To amma a wannan karon karen ya yi watsi da nunin da mutumin yayi masa na ya je wurin.

Wannan yana nuna kenan kamar yadda Takaoka ta ce karnukan suna iya fahimta daga yaudararsu da aka yi da suka je a zagaye na biyu ba su ga komai ba, cewa idan mutumin abin a yarda da shi ne ko a'a.

Bayan wannan zagayen gwajin, sai kuma wani mutumin (mai gwaji) ya sake maimaita zagayen farko na nunin, wanda suke ganin abinci idan sun ce wurin, karnukan sai suka je wurin cikin farin ciki.

Hakkin mallakar hoto M01229 cc2.0

Takaoka ta ce ta yi mamakin yadda kare ya yi saurin daina yarda da mutum haka.

''Karnuka suna da basirar mu'amulla sosai fiye da yadda muke tunani. Kuma wannan basira tana kara bunkasa daga tsawon tarihin rayuwarsu da mutane.''

Mataki na gaba, ta kara da cewa, shi ne jarraba dabbobin da suke kusa da karen a halitta kamar kerkeci. Wannan zai nuna tasirin girke kare a gida akan basirar mu'amullarsa.

Nazarin ya nuna karnuka na son abu ya kasance wanda za a iya yin hasashen yadda yake., inji John Bradshaw na Jami'ar Bristol a Burtaniya, wanda ba ya cikin binciken.

Da zarar abu ya zama ba shi da tabbas ko ya zama daban-daban, ma'ana yanzu ga yadda yake idan an jima kuma sai ya zaman daban, to sai ka ga kare ya nemi zabi.

Misali a gwajin da aka yi musu, a lokaci daya an nuna musu wuri sun je sun ga abinci, a wani lokacin kuma an nuna musu wannan wurin sun je amma kuma ba su ga abinci ba, saboda haka ne da aka kara nuna musu su je wurin sai suka ki yarda su je.

To haka kuma idan abu ya ci gaba da wakana ta yadda ba su san abin da zai faru ba, sai su damu, su zama mafadadata ku su rika jin tsoro, inji masanin.

''Karnukan da masu su ba su tsaya musu a kan abu daya ba, wato suna nuna wa karnukan rashin tabbas a kai a kai, karnukan sukan kasance da matsala a halinsu.''

Za a iya bayanin wannan gwajin na karshe ta hanyar dadin da kare yake ji da duk wani sabon abu.

Hakkin mallakar hoto Victoria Standen
Image caption karya Cassie ba ta yarda da bakin da ba su da tabbas

Abin da aka gano a nazarin bai ba wa Victoria Standen mamaki ba. Tana da karyar da ake ganin irinta na daga wadanda suka fi basira a karnuka.

Idan suka fita tattaki, sai ya tsaya a mahada ya ga inda za su nufa. ''Na saba nuna inda za mu nufa idan karyar ta duba wannan hanya, sai ka kalle ni ta ga idan ya kamata ka tafi,'' inji Standen.

Wani abu kuma, idan ta ga wani bako ba abin yarda ba ne ( ba mai ba da abinci ba ne) ba lalle ba ne karyar ta yarda da shi.

Bradshaw ya ce, tana kara tabbata karnuka suna da basira sosai fiye da yadda a da aka dauka, amma basirarsu ta bambanta da tamu.

''Karnuka suna lura da halin mutum sosai amma suna da dan saurin yanke hukunci a kan abu wato su dauka ga yadda yake tun kafin ta tabbata hakan yake saboda sabo,'' ya ce.

''Suna dasa tunaninsu ne a kan abin da yake a yanzu ba sa waiwayen baya ko kuma su yi shiri domin gaba.''

Kuma idan suka gamu da wani yanayi, ya ce, sai su aikata abu kamar yadda yanayin da ake da shi a lokacin yake, ''maimakon a ce sun yi tunani mai zurfi kan abin da haka ya kunsa.''

Hakkin mallakar hoto lynn m stone npl
Image caption Idan ka yaudare ta, ba za ta yarda da kai ba

Karnuka kenan suna lura da mu idan muka yi musu ishara kamar yadda wannan nazari ya nuna, inji Brian Hare baban jami'in kimiyya a cibiyar nazarin tunani da basirar kare.

''Suna duba bayanin da muke ba su ta yadda hakan zai iya taimaka musu wajen cimma burinsu.

Karnukan gida da dama za su yi watsi da isharar da ka yi musu ko abin da ka nuna musu, idan ba ka nuna daidai ba, su yi amfani da kwakwalwarsu su gano abin da aka boye,'' inji Hare.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Dogs can tell if you're untrustworthy