Gizo-gizo goma masu layar-zana

Hakkin mallakar hoto blickwinkel alamy

Galibi gizo-gizo ba abu ne da ke nuna kansa ba sosai a duk inda yake, amma wasu nau'in suna da wani launi a jikinsu da suke layar-zana domin kama kwarin da suke ci.

Robin Wylie ya duba guda goma daga cikin ire-iren wannan halitta da ke da wannan baiwa ta siddabaru.

Hakkin mallakar hoto beatrice tiberi cc 2.0

1. Zanen launin dorawar da ke bangaren kasa na jikin wannan gizo-gizon shi ne abin da yake amfani da shi wajen batar da kama, ya yaudari kwari su shigo yanarsa ya kamasu.

Ana ganin yana saje wadan nan wurare na jikinsa ne da ke da launin na rawaya da wasu furanni idan ya hau kansu, wanda hakan zai sa kwari ba za su gane ba, sai su dauka jikin furan ne, idan suka biyo ta wurin sai kawai su fada tarkonsa.

Hakkin mallakar hoto visuals Unlimited npl
Image caption Gizo-gizo mai kama da garkuwa

2.Wannan nau'in shi kuwa yana da baya ne mai zane mai kyau wanda yake daukar ido da launin jikinsa mai siffar garkuwa. Da wannan ne yake dabarar janyo hankalin kwari su fada tarkon yanarsa.

Yana karkata garkuwar ce ta fuskanci wurin da ke da duhu, a lokacin da yake farauta, wannan sai ya sa kwari su dauka wani tsakani ne a jikin bishiyar da suke kai, sai su ratso ba tare da sun gane ba. Sun fada tarko kenan.

Hakkin mallakar hoto gailhampshire cc

3. Irin wannan ana samunsa ne a wurare masu dumi a nahiyar Asiya da Afrika da kuma Australasia.

Matan irin wannan na daga cikin gizo-gizon da suka fi girma a duniya, domin tsawon kafarsu yakan kai inci takwas, wato kusan tsawon daga wuyan hannun mutum zuwa karshen yatsansa na tsakiya.

Launin jikinsu yana jan hankalin kwari. Wani nazari da aka yi a 2002 ya nuna cewa bangaren jikinsu na baya yana da launi mai haske da ke daukar ido, abin da kwari suke so, domin haka furanni suke.

Haka ne zai sa kwarin su dauka fure ne idan suka ga wannan launi mai haske da daukar ido.

Hakkin mallakar hoto louise murray spl
Image caption Gizo-gizo mai gashin baki

4.Shi kuwa irin wannan gizo-gizon wanda ake danganta sunansa da katuwar kaguwa saboda kamanninsa da kaguwar, yana da wani makami na daban, wanda yake farauta da shi.

Yana da wani farin zane-zane ko kuma kamar yadda ake masa lakabi gashin baki a karkashin idanuwansa.

Wannan farin zane-zane yana da daukar ido ko haske, yadda ko da daddare yana da hasken da zai jawo hankalin kwari su zo wurin gizo-gizon.

Yawanci kwari ne abincin wannan gizo-gizo, amma kuma hatta jemagu da kunama ma an ga yana ci.

Hakkin mallakar hoto dinesh rao cc by 2.0

5.Wannan gizo-gizon mai kama da fatalwa kamar yadda ake cewa, yana kama kwarin da yake ci ne daga bangare biyu.

Bayansa mai launin azurfa da kuma cikinsa mai ratsi-ratsin ruwan dorawa, dukkaninsu tarko ne da ke batar da kama da jawo hankalin kwari.

Bangaren cikin nasa mai ratsi-ratsin launin dorawar, da daddare ya ma fi tasiri, inda launin yake zama kamar wani fure da kwarin suke ci. Da sun zo sai tarkon yanarsa ya kama su.

Hakkin mallakar hoto aviplot cc by 2.0

6.Akwai nau'in gizo-gizo mai kama da kaguwa da yawa, amma irin wannan daban suke.

Da yawa daga cikin irin wannan suna tarewa ne a kan furanni, su rika kama kwarin da ke zuwa kan furannin.

Wasu nau'in nasa ma suna sauya launin jikinsu ya zama daya da na furannin. Za a ga wannan kamar wata hanya ce ta sauya launi kawai, to amma a zahiri tarko ne na kama kwari.

Gizo-gizon yana sa jikinsa ya yi launi mai haske da zai sa furen da yake kai ya kara kyau da ban sha'awa ga kwari ta yadda za su zo wurin.

Hakkin mallakar hoto premaphotos npl
Image caption Gizo-gizo mai kama da kaguwa na Brazil

7.Shi wannan nau'in na gizo-gizon mai kama da kaguwa, kusan ya fi sauran danginsa sauya kamannin, ya juye ya zama kamar fure.

Iri ne da ke da ban sha'awa, wanda kuma ana samunsa da launin fari da ruwan dorawa ko rawaya da ruwan hoda da kuma ruwan kasa, dukkaninsu, suna zama launin da suke ne domin su yi kama da wani fure.

Wannan bad da kama da gizo-gizon ke yi, na taimaka musu kama kudan zuma da sauran kwari da ke hawa furanni, sannan kuma suna bace wa dabbobi masu cinsu.

Hakkin mallakar hoto premaphotos npl

8.Gizo-gizo ba da jikinsu kadai suke yin tarkon kama kwarin da suke ci ba. Da yawa daga cikinsu, kamar wannan da ake gani a hoton nan na sama (cyclosa insulana) suna wata saka mai yau da jan hankali a yanarsu.

Wannan saka da suke yi a gidan nasu, tana yaudara tare da jawo hankalin kwari masu tashi.

Suna sa sakar ta rika haske mai ban sha'awa ga kwari da daddare, wadda ta hakan ne kwarin suke zuwa su shiga tarko, kamar na wasu da muka bayyana a baya.

Hakkin mallakar hoto graham wise cc by 2.0
Image caption Gizo-gizo mai kama da dawisu

9.Wadannan su ba maganar layar-zana da bad da kama domin kama kwari ba ce ta sa suka yi fice a cikin nau'ukan gizo-gizo ba.

Shi wannan da ake danganta sunansa da dawisu yana wani salo ne na juyi mai ban sha'awa a lokacin da yake bukatar saduwa da tamata (matarsa).

A wannan lokacin da maza suke neman mata za ka ga suna jan hankalin matan ne da wata rawa da suke yi da bangaren jikinsu na baya.

Suna da manyan idanuwa wadanda suke ganin nesa sosai, kuma yadda inaduwan suke ganin launi iri daban-daban da kyau sun fi namu (mutane).

Saboda haka a wurin tamatar irin wannan gizo-gizo, wadannan abubuwa ne da ke jan hankalinta.

Hakkin mallakar hoto gerry pearce alamy

10.Gizo-gizon da ake kira Bolas da Ingilishi yana da dabaru masu wuyar fahimta na jan hankalin kwari su fada tarkonsa a tsakanin dabbobi na duniya.

Shi wannan nau'i ba saka gida ko tarko yake yi ba wanda kwaro zai fada, a'a, shi yana kama kwari ne ta hanyar makala layi daya (kamar igiyar shanya) na zaren yanarsa mai kyalli, kuma ya sa digon wani ruwa mai danko a karshen zaren.

Wani nau'in wannan gizo-gizon (mastophora hutchisoni) shi ma yana da wani makami na sirri wanda ba ya ganuwa.

Da daddare suna fitar da wani ruwan sinadari ( na yaudara) mai kama da wani ruwan jan hankali domin a yi jima'i, na tamatar wasu kwari nau'in malam-buda-mana-littafi.

Wannan ruwan sai ya ja hankalin mazan wadannan kwari su zo wurin, suna taba shi sai danko ya rike su.

Irin wadan nan gizo-gizo suna kwaikwayon ruwan nau'i biyu ne na kwarin na malam-buda-mana-littafi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Ten spiders that are surprisingly beautiful