Magenka za ta iya sanin halin da kake ciki

Hakkin mallakar hoto alena borozova alamy stock photo

Ba kamar yadda kake tunani ba, kyanwarka tana da hankalin da za ta iya sanin yanayin farin-ciki ko damuwa da kake ciki.

Bisa ga dukkan alamu suna lura da yanayin da muke ciki, kamar yadda Robin Wylie ya gano.

Idan ka dade kana amfani da intanet, za ka san akalla wani abu daya; abin shi ne mutane suna kaunar kyanwa.

Sai dai yadda ita kuma kyanwar take daukarmu a zuciyarta shi ne ba mu fahimta ba sosai.

Idan muka kwatanta yadda karnukanmu, da ke binmu sau da kafa, sai mu ga kamar ita mage ba ta damu da lamarin mutum ba.

To amma ga alama, lamarin ba haka yake ba, domin kusan kyanwa ta san halin da muke ciki, fiye da yadda muke dauka.

Bisa ga dukkan alamu suna iya ganewa idan muna cikin farin-ciki.

Wani sabon bincike da aka yi, ya gano kwakkwarar shedar da ke tabbatar da cewa kyanwa tana sanin irin yanayin halin da mutum ke ciki.

Hakkin mallakar hoto Tambako the Jaguar
Image caption Kyanwa ka iya nazarin yanayin fuskarmu

Moriah Galvan da Jennifer Vonk na jami'ar Oakland a Rochester da ke Michigan a Amurka sun yi nazari a kan wasu maguna 12 da masu su.

A binciken sun gano cewa yanayin yadda magunan suke kusantar masu su ya kan bambanta idan suka ga masu su suna murmushi da kuma lokacin da suke murtuke fuska.

Idan magunan suka ga masu su, suna murmushi, za ka ga sun fi sakin jikinsu da haba-haba da mutanen, suna goga jikinsu a jikin mutumin da hawa cinyarsu da yin dan gurnani na jin dadi.

Kuma za ka ga suna son zama kusa da masu su, idan mutanen suna murmushi, ba kamar yadda idan suka lura masu su din suna bata rai ba.

Yanayin gaba daya ya sauya, lokacin da aka hada magunan 12 da bakin mutane, maimakon wadanda suke da su.

A wannan tsarin, sun saki jikinsu kamar yadda suke yi da masu su, ba tare da la'akari da ko wadannan bakin mutanen suna murmushi ko bata rai ba.

Hakkin mallakar hoto Jimmy B cc by 2.0
Image caption Muna daukar mage a matsayin dabba mai son kanta

Da dadewa mun san cewa karnuka sun iya sanin yanayin da mutum yake ciki daga fuskarsa.

Amma wannan ita ce sheda da farko da ke tabbatar da cewa maguna ma suna da irin wannan baiwa.

Kafin wannan nazarin, bincike daya kawai aka yi na kokarin sanin ko kyanwa tana iya sanin yanayin da mutum yake ciki daga fuskarsa.

Sakamakon binciken da aka wallafa a watan Janairu na shekara ta 2015, ya bayar da ma'ana daban-daban.

Sakamakon nazarin Galvan da Vonk ya nuna cewa kyanwa tana sanin halin da mutum yake ciki fiye da yadda muke tunani.

Sai dai wannan ba yana nufin suna taya mutum jimamin halin da yake ciki ba ne fa.

Watakila dai kawai sun koyi danganta murmushin masu su ne da samun wani lada (wani abu na jin dadi daga mutumin, misali ya rika shafar magen ko daukarta a jikinsa ko ba ta abinci).

Saboda mutane za su fi kula da mage, ma'ana su ba ta abinci ko shasshafa ta ji dadi, idan mutum yana cikin farin-ciki.

Duk da haka, ko da ace magunan ba sa iya fahimtar yanayinmu, binciken ya nuna cewa za su iya sanin dan sauyin yanayin fuskarmu.

Hakkin mallakar hoto Zoonar GmbH Alamy Stock
Image caption Mussa na matukar son dadi

Nazarin ya kuma nuna wani abu mai muhimmanci, wanda shi ne maguna na sonmu

Vonk ta ce, ''mutane sun damu su san ko lalle maguna suna fahimta tare da damuwa da halin da masu su suke ciki,''

''Aikinmu ya nuna ga alama, ba kamar yadda mutane ke zargin mage cewa, ba ta damu da halin da mai ita yake ciki ba, a'a, ta damu.''

Za a iya daukar lokaci mai yawa kafin a gano basirar mage a kan yadda take daukar yanayin da mutum ke ciki, saboda ba ta nuna alamu masu yawa a nazarin.

Bayan yanayin da ita magen ke nunawa na jin dadi kamar dan gurnanin nan da shafar jikin mutum, Galvan da Vonk, sun lura da yadda magen ke yi da jikinta, hadi da motsa kunne da jela, wadanda duka ke nuna jin dadinta da kuma gamsuwa, idan mai ita yana murmushi.

Sabanin hakan, shekara da shekaru masana kimiyya sun san cewa yadda karnuka suke fuskantar mutum idan yana murmushi da kuma bacin-rai ya bambanta.

An gane hakan ne, saboda akalla ta wani fannin ana ganin yadda suke yi a zahiri idan sun ga mutum a yanyin da yake.

Wani nazari da aka yia 2011 ya nuna karara yadda karnuka ke kokarin kauce wa mutumin da suka ga yana cikin bacin-rai, maimakon sauya yanayin jikinsu kawai.

Hakkin mallakar hoto Tambako the Jaguar
Image caption Wannan dadar ta san tunaninka

An dade da mayar da kare dabbar gida, domin kamar yadda wani bincike na kwayar halitta da aka yi a wannan shekara ta 2015 ya nuna, tun sama da shekara 30,000 aka fara hakan.

Sabanin hakan, ita kyanwa an fara mayar da ita dabbar gida ne kusan shekaru 10,000 da suka gabata, watakila a gabas ta tsakiya.

Yadda kare yake nuna sanin yanayin da muke ciki karara fiye da kyanwa, zai iya kasancewa saboda ya dade da sabawa da rayuwar mutane ne.

Amma dai a yanzu, ya yi wuri a zartar da wata magana a kai, tun da akwai nazari da yawa da ake yi yanzu na fahimtar yadda zuciya ko tunanin kare yake.

Ita ma kuma kyanwa nazarin da aka yi kan yadda take yi sakamakon yanayin da mutumin da take tare da shi yake ciki ba wani mai yawa ba ne.

Duk da cewa mage kusan ita ce dabbar da muka fi son zamantakewa ta kut-da-kut da ita, har yanzu akwai tarin abubuwa da za mu koya a kanta.

Ba mu ma san mai ya sa take dan wannan gurnani ba. Amma dai wannan binciken zai iya taimakawa wajen kawar da mummunar fahimtar da ake yi mata cewa ba ta damu da halin da mutum ke ciki ba (na damuwa).

Zai iya kasancewa ita dai kyanwa ba ta nuna damuwarta a kanmu ne kawai kamar yadda kare yake nuna mana karara.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Your cat can pick up on how you are feeling