Kwaro mafi kara a duniya

Hakkin mallakar hoto visuals unlimited npl

Wace halitta ce mai kafa shida take kuka mafi kara a duniya?

Nick Fleming ya bincika.

Hakkin mallakar hoto FLPA Alamy
Image caption Gyaren Turai

Kukan gyare na daya daga cikin fitattun kara a duniya kamar yadda aka ayyana. Wannan dan kwaro mai kama da fara, yana kara mai tsanani da ke ruda wuri.

Namijin gyare yana yin karar ce ta hanyar motsa wasu sassan jikinsa na baya masu kama da ganga, bayan nasa da kusan holoko ne, abin da ke sa karar ta yi tsanani.

Manyan maza sukan yi kara mafi karfi wanda da haka suke jan hankalin mace fiye da wanda kararsa ba ta da karfi sosai.

To amma wannan ita ce karar da ta fi ta duk wani kwaro? John Petti, wanda a da yake jami'ar Florida, ya shirya bincike a kai.

Masanin ya bincika bayanan da aka taba wallafa wa sannan kuma ya tambayi masana ilimin kwari kamarsa a kan wannene kwaron da suka sani mafi kara a duniya.

An gabatar masa da sunayen kwari dama da suka kunshi nau'in gyre da fara daban-daban.

Nau'ukan sun hada da wani babban gyare da ake samu a Malaysia da wani na Turai da kuma wasu fari iri-iri.

Na karshe daga jerin wadanda aka gabatar shi ne ya fi kara, inda yake kara mai yawan lamba 96 a ma'aunin kara wato decibels (96 decibels) wanda ake ji daga nisan santimita 50 (50 cm).

Hakkin mallakar hoto Jeff B CC by 2.0
Image caption Wannan farar ta Amurka da tana daga wadanda kukansu ya fi kara

Amma duk da haka akwai wasu nau'ukan gyaren da yawa da aka gano sun fi kara. Wanda aka gano ya fi kara shi ne mai lamba 108.9 a ma'aunin kara (108.9 decibels), kuma ana samunsa ne a nahiyar Amurka ta Arewa.

Sai dai farfesa Petti yana ganin gyaren da ya fi kara shi ne wanda ake kira T. Walkeri wanda yake kara da ya kai lamba 105.9 a ma'aunin sauti na decibels (105.9db) wanda ake ji daga tazarar santimita 50 (50cm).

To amma wannan fa bai kai wani gyaren da ake kira Brevisana brevis na, wanda nau'i ne da yake a Afrika, wanda shi kuma yake karar da ta kai lamba 106.7 a ma'aunin sauti na decibels (106.7db).

Duk da cewa a wurin mutane duk karar da gyare ke yi daya ce babu wani bambanci, to amma lamarin ba haka yake ba a wurin kwaron, domin karar da namiji ke yi domin jawo hankalin tamata daban yake da wanda yake yi domin ankarar da 'yan uwansa idan akwai wata barazana garesu.

Wani bincike ya nuna cewa karar da nau'in gyaren da ake kira 'desert cicada' (diceroprocta apache) yake yi wadda ta kasa ta nau'in wanda ya fi kara da lamba 0.5 (0.5db), ta rage kaifin hare-haren da bera ( southern grasshopper mouse) ke kai musu.

Hakkin mallakar hoto F. Martinez Clavel Alamy

Ba lalle ba ne wannan gyaren mai suna 'B. Brevis' ya zama wanda ya fi kara na dindindin. A wani bincike da aka yi a 1995, masana kwari sun auna karfin karar neman mace da wasu nau'ukan gyaren har guda 30 suke yi da kuma karar gargadi ta wasu nau'ukan 59 dukkaninsu a nahiyar Amurka ta Arewa.

Masanan suna ganin karar da kwarin suke yi ta danganta da nauyin jikinsu ne.

Yayin da B, brevis yake da nauyin giram 0.3 (0.3g) idan ya bushe, shi kuwa katon gyaren da ake kira 'Empress' wanda ake samu a kudu maso gabashin Asiya, mai tsawon fukafuki santimita 18 zuwa 20 (18-20cm) ya kai nauyin giram biyu (2g).

Shedar da ake da ita wadda ba wata tabbatacciya ba ce, tana nuna cewa 'Empress' din na da kara matuka, kuma rashin wani kokari na auna kararsa ne a kimiyyance kawai ya hana shi zama, kwaron da ya fi kara mai karfi a duniya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The loudest insect in the world