Abin da ya sa ba ka tsoron maciji kana yaro

Hakkin mallakar hoto Ephotocorp alamy

Macizai da yawa suna da hadarin gaske, wannan shi ya sa kusan muke jin tsoronsu. Amma wasu gwaje-gwaje da aka yi sun nuna cewa 'yan kananan yara ba sa jin tsoron macizai.

Melissa Hogenboom ta yi nazari a kai.

Idan a ce ka ajiye dan kankanin yaro a daki da maciji da kuma gizo-gizo. Zai yi wasa da wadannan halittu ne kake gani ko kuma zai kyale su?

Wannan ba tambaya ba ce ta neman sanin ra'ayi ko wasa kwakwalwa ba. Tuni masu nazari a kan abin da tsoro ya kunsa suka dukufa domin gano amsarta.

Abu ne da aka riga aka sani cewa 'yan kananan yara sun fi sha'awar dabbobi masu rai a kan marassa rai.

Bincike ya gano cewa yaran suna da wannan sha'awa ko da kuwa dabbobin nan macizai ne da gizo-gizo.

Bincike irin wannan yana sa a gano wasu abubuwan a game da shi kansa tsoron yadda yake, da lokaci da kuma yadda ake samunsa.

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Yawanci ana jin tsoron maciji

Tsoron maciji yana daya daga cikin abin da aka fi yi kuma wanda ya fi tsanani a duniya, kamar yadda mai bincike a kan tsoro Judy DeLoache ta jami'ar Virginia da ke Charlottesville, wadda ba ta cikin wannan sabon nazari ta ce.

Abu mai sauki da ake gani, wanda kuma mutane da dama suke dauka haka yake shi ne, muna da tsoron maciji a ranmu daman.

Dalilin shi ne, saboda wadansu macizan suna da hadarin gaske, saboda haka muke tsoron kowane maciji.

A kan haka ne, aka jarraba wasu jarirai 'yan watann 11, inda aka nuna musu hotunan maciji hadi da wata kara mai ban tsoro ko kuma mai dadi (ta farin ciki).

Jariran sun rika kallon macizan na tsawon lokaci lokacin da aka hada da karar mai ban tsoro fiye da lokacin da aka nuna musu macijin aka hada da karar mai dadi.

A wani nazarin da aka yi, shi ma an ga irin wannan sakamako, inda aka hada fuskoki na ban tsoro da kuma na farin-ciki, abin yake nuna cewa, 'yan kananan yarasuna danganta tsoro da macizai.

Hakkin mallakar hoto carlos diaz cc 2.0
Image caption Jin tsoron wasu macizan masu dafi ba laifi ba ne

Sai dai wadannan bincike ko nazari suna da wuyar tabbatarwa, kuma ba za mu iya tambayar jarirai ko da gaske suna jin tsoron macizai ba.

Wani sabon nazari ya sake duba yadda 'yan kananan yara suke yi ko suke ji idan sun ga macizai.

Masu nazarin suna kokarin kawar da tunani ko maganar da ake yi ne cewa, jarirai ko yara da kuma mu (mutane) muna da tsaron macizai daman a ranmu.

Masu binciken sun lura tare da auna yanayin yadda 'yan kananan yaran suke ji ko suke yi da jikinsu yayin da suke kallon hoton bidiyon macizai da giwaye, da aka hada da muryoyin tsoro da kuma na farin-ciki.

Daga nan kuma sai suka shirya bai wa 'yan yaran tsoro, domin su ga yadda za su yi.

Sai suka hada musu abin da zai nuna idan sun ji tsoro, inda wata fitila za ta yi haske kwatasam da zarar sun ji tsoro yayin da suke kallon bidiyon.

Hakkin mallakar hoto josh henderson cc 2.0
Image caption Ba kowane maciji ba ne yake da dafi

Tsorata kamar wannan za ta fi yawa idan a ce jariran daman sun tsorata, kamar dai yadda idan muna kaloon fim din ban tsoro, sai mu kara firgita idan muka ga wani abin mafi ban tsoro.

''Abin da muka gano shi ne firgitarsu ba ta da yawa ko girma a lokacin da suke kallon bidiyon maciji, hatta lokacin da aka hada da murya mai ban tsoro,'' in ji Vanessa LoBue ta jami'ar Rutgers da ke New Jersey a Amurka.

An wallafa sakamakon wannan bincike ne a mujallar kimiyyar tunanin yara ta Journal of Experimental Child Psychology.

Sakamkon ya nuna jariran ba su nuna wata fargaba ba sosai. Gabansu bai fadi ba sosai, abin da ya kara tabbatar da cewa ba su ji tsoro ba.

Wato dai duk da cewa 'yan yaran sun mayar da hankali sosai a kan macizan, hakan bai sa sun ji tsoro ba.

Hakkin mallakar hoto Ephotocorp alamy
Image caption Da ganin wannan ka san mugun maciji ne

LoBue ta yi tsammanin ganin haka daman, domin an san 'yan jariran mutum da na biri da sha'awar macizai fiye da wasu dabbobi, abin da ke nuna cewa macizai abubuwa ne na musamman a wurinsu.

To wannan sha'awar mai yawa a kan macizai, ita ce ake ganin cikin sauki za ta iya juyawa ta zama tsoro a wani yanayin.

DeLoache ta yarda yara a zuciyarsu ba su da tsoron macizai. ''Sai dai maimakon haka suna da baiwar gani da kuma daukar matakin gaggawa a kan maciji.''

Misali, bincike da dama sun nuna kananan yara suna saurin gane maciji a hoto a cikin sauran hotuna marassa maciji a cikinsu.

Hakkin mallakar hoto Tambako The JaguarCC by 2.0
Image caption Wani macijin yana da ban sha'awa

LoBoue ta gano cewa wannan tsoro ba wai abu ne da yake a zuciya ba, tsoro ne da ya zama jiki sakamakon yanayi na al'ada ta yau da kullum.

Ta ce,''yadda muka ga yanayi daban-daban na yadda ake ji idan an ga maciji can a baya a lokacin mutum yana dan kararrami, abin da ke nuna cewa maciji abu ne na musamman, hakan ba yana nufin wannan ne ke sanya wa mutum ya fara jin tsoro ba tun a lokacin''.

''Abu ne da zai iya yuwuwa mayar da hankali sosai kan wani abu zai iya sa mutum ya koyi tsoro cikin sauki a can gaba. Hakan na saukaka koyon jin tsoro.''

LoBue ta ce abu ne mai kyau tsoron wasu abubuwa ba su za ma a zuciyarmu ba tun ainahi.

''Ba abu ne na gado ba ya kasance akwai tsoron wani abu a zuciya,'' ta ce, saboda hakan zai takaita burin jariri ko dan kankanin yaro na kokarin sanin sabbin abubuwa.

A maimakon haka muna saurin koyon yadda za mu ji tsoron wani abu idan yana da hadari.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan When you were a baby, you were not scared of snakes