Karnuka na iya shakuwa da mutum kamar jarirai

Hakkin mallakar hoto mikako mikura

Kallon kare a ido kai tsaye ba tare da kaucewa ba, abu ne da zai iya haifar da shakuwar da ake samu tsakanin uwa da danta.

Zoe Guough ya duba yadda wannan alaka take ginuwa.

Hada ido tsakanin uwa da jaririnta na karfafa dangon kauna ta hanyar zaburar da kwayar halittar da ke sa kauna (oxytocin) wadda ke kwakwalwar uwar.

Wannan na kara shakuwa tsakanin iyaye da 'ya'ya ta kara tabbatar da dabi'un sabo da kuma mu'amulla da juna.

Bincike ya nuna cewa shafar jiki ko hada ido da kare zai iya jawo irin wadannan kwayoyin halitta na kauna a kwakwalwar mutum.

A yanzu wasu masana kimiyya a Japan sun gano cewa irin wannan hada ido tsakanin kare da mai shi zai iya kaiwa ga shakuwar da ake samu tsakanin uwa da danta, inda mutum zai ji yana kaunar karen nasa kamar yadda yake ji a kan iyalansa, wanda hakan kan kusantar da dabbar kusa da mutum sosai.

Hakkin mallakar hoto Mikako Mikura

An wallafa rahoton binciken ne a mujallar kimiyya ta Science, wanda kuma ya nuna cewa kerkeci (karen dawa) ba shi da irin wannan hali.

Wadanda suka hada rahoton suna ganin wannan na nufin hanyar shakuwar watakila ta samo asali ne a tsakanin halittun biyu (mutum da kare) a sanadiyyar dawo da kare cikin mutane daga daji.

''Za a iya cewa karnuka sun iya zama tare da mutane saboda sun iya sabawa da matakin da ke kulla dangantaka da mutane,'' in ji jagoran masu binciken Dakta Miho Nagasawa na makarantar likitocin dabbobi ta jami'ar Azabu da ke Japan.

''Tun da farko karnuka suna da irin wannan mataki ko yanayi da sauran nau'ukan karnuka, to amma kuma sai shi ma mutum ya samu damar ratsa irin wannan mataki inda ya samu wannan dabi'a ta kulla kauna da wasu dabbobin, su ne karnuka.''

An yi nazarin karnuka tsawon minti 30 a cikin daki tare da masu su, yawan lokacin da karnuka ke hada ido da masu su, shi ake amfani da shi a sa karnukan cikin rukuni biyu: rukunin dogon kallo da kuma na gajeren kallo.

Karnuka sun bambanta:

karnukan da suke kallon masu su sosai sun samu karuwar yawan kwayoyin halittar da ke kulla so da kauna bayan gwajin, haka kuma wannan kallon juna ya jawo karin wadannan kwayoyin halitta na kauna a kwakwalwar masu karnukan su ma.

A gwaji na biyu an shakawa wasu karnuka sinadarin kwayoyin halittar da ke sa kauna (oxytocin) a hancinsu, kafin a sa su a daki tare da mai su da kuma wasu bakin mutane biyu, har tsawon minti 30 ba tare da mutanen sun yi wata mu'amulla ko kallon karnukan ba.

Masu nazarin san ga cewa matan karnukan sun fi dadewa suna kallon masu su, kuma masu karnukan sun samu karin yawan kwayoyin sa kauna a kwakwalwarsu.

Hakkin mallakar hoto Catherine Walker

Masu binciken sun ce abin da ya sa wannan sinadari da aka shaka a hancin karnukan bai yi tasiri a kan mazan karnukan ba, shi ne bambancin jinsi

Masu binciken suna ganin wannan sakamako ya nuna cewa za a rika samun karuwar kauna tsakanin mutane da karnuka wadda wannan sinadari zai rika haifarwa.

Idan kare ya kalli mai shi a ido hakan yana sa jikin mutumin ya tura sinadarin kwakwalwarsa, wanda hakan ke sa mai karen kara son ya yi mu'amulla da karen, hakan kuma sai ya sa shi ma jikin karen ya tura karin wannan sinadari na kauna kwakwalwar karen (kauna kan kauna kenan).

Lokacin da aka maimata irin gwajin farko da aka yi da kerkeci, wadanda mutane suka rene su, masu rahoton ba su ga alamar irin wannan shauki na kauna ba, abin da ke nuna ga alama kerkeci ba sa amfani da hanyar sadarwa iri daya da mutane kamar yadda kare yake yi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Dogs can bond like babies