Soyayya ta fi abinci a wurinsu

Hakkin mallakar hoto rob shennan alamy

Kasancewa tare da juna abu ne mai muhimmanci a wurin wannan nau'in tsuntsayen masu kama da kanari, har ma sun fi son zama tare, ko da da yunwa ne a kan su rabu ko da na dan kankanin lokaci ne.

Melissa Hogenboom ta gano mana cewa wadannan tsuntsayen (great tits) suna daga cikin tsuntsayen da ke da wannan kauna a tsakanin masoya.

Wani ayarin masu bincike ne ya gano hakan a lokacin da ya hana wasu auren wannan nau'in tsuntsaye (mata da mazansu) kiwo a wuri daya.

Tsuntsayen sai suka gwammance su zauna tare a haka ba tare da sun tafi cin abincin ba a ware, duk da yunwar da suke ji.

Sakamakon nazarin wanda aka wallafa a mujallar kimiyya ta 'Current Biology' ya nuna muhimmancin zaman masoya tare a tsakanin wadannan tsuntsaye.

Wadannan tsuntsaye (great tits) sun san cewa nasarar samar da iyali yadda ya dace na bukatar taimakon abokin soyayya.

Hakkin mallakar hoto Nicholl WilliamsAlamy
Image caption Kakar soyayya ta kama

"Shawarar da suka yanke ta gwamma su zauna tare a kan su bazama neman abinci, tana nuna irin tunanin kowane tsuntsu na gajeren lokaci, wanda za a ga kamar ba wani abu ne mai dorewa ba, ya karkata wurin tabbatar da amfanin dangantaka mai dorewa tsakanin tsuntsayen (mata da miji)," In ji jagoran masu binciken Josh Firth, daga jami'ar Oxford da ke Biritaniya.

Ya kara da cewa "saboda haka, ko a tsakanin dabbobin daji, halayyar dabba daya za ta iya kasancewa ta karkata wajen biyan bukatar abokin soyayyarta."

Zaman miji tare da matarsa ko saurayi tare da budurwarsa na nufin hakan zai sa su kara sabawa sosai da sauran tsuntsayen da ke tare da su.

Saboda haka samun wannan dangantaka ko alaka da sauran tsuntsayen wata hanya ce da masoyan za su iya samun abinci, kamar ta hanyar roko ko bashi ko ma dai taimakon juna, kamar yadda masu rahoton suka wallafa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Love is better than food, if you're a pair of great tits