Shin gaskiya ne muna cin gizo-gizo?

Hakkin mallakar hoto judith holford alamy

Ba wanda ya san ko gaskiya ne lalle muna hadiye gizo-gizo lokacin da muke barci, amma kuma bayanan ma'abota shafin BBC sun nuna abin zai iya faruwa a wani lokaci.

Henry Nicholls ya duba lamari.

Zai iya kasancewa gaskiya? Ko gizo-gizo zai iya shiga bakinmu da daddare a lokacin da muke barci? Idan abin ba zai taba yuwuwa ba, to ta yaya mutane suke ganin maganar kamar gaskiya ce?

BBC ta nemi jin ta bakin ma'abota shafinta na Facebook na bangaren labara na musamman domin ganin ko wannan magana za ta iya kasancewa gaskiya.

Ga abin da wasu suka bayyana.

''Idan muna ci to ba na son ma na sani,'' in ji Margie Williamson, abin da yawancin mutane suka bayyana kenan cikin kyama. '' Ku ce min wannan almara ce kawai ko kuma in rufe bakina da bandeji,'' in ji Claire Jeyes.

An san cewa gizo-gizo yakan shiga kunnen mutane kamar yadda ya faru da wannan matar 'yar kasar Sin, wadda ta je asibiti kunnenta na kaikayi.

Haka ma a shekara ta 2014 mawakiya Katie Melua, ta ce wani gizo-gizo ya shigar mata kunne daga jikin wani abin sauraran sauti irin na sanyawa a kunne.

''Wannan ya tabbatar da cewa gizo-gizo bai wuce shiga cikin mutum ba,'' kamar yadda Juli Marie ta rubuta a shafin Facebook na BBC na labaran musamman da suka shafi halittu.

Hakkin mallakar hoto Phil DeggingerAlamy
Image caption Wannan gizo-gizon ya yi kaurin suna wajen cizon mutane

A rubuce-rubucen da aka kan harkokin lafiya, akwai inda aka samu gizo-gizo ya ciji mutane a lokacin da suke barci.

A nazarin da aka yi kan cizon wani nau'in gizo-gizo mai fara jela a Australia, kusan kowana daya daga cikin mutane uku ya ba da rahoton cewa ya cije shi a lokacin da yake barci.

Akwai nau'ukan gizo-gizon da yawanci suka fi zirga-zirga da daddare, wadanda kuma za su iya yi wa mutum cizon da zai je asibiti.

Nazarin da aka yi kan cizon ya nuna cewa yawanci yana yinsu ne a dan yatsa ko hannu ko kafa, ko da yake akwai lokacin da yake cizon a fuska, wanda ya hada da na wata yarinya 'yar shekara takwas da ya cije ta a fatar kan idonta, a lokacin da take barci.

Wasu daga cikinku kila kun taba gamuwa da irin wannan cizo na gizo-gizo.

''Gizo-gizo ya taba cizo na a fuska a lokacin da nake barci,'' in ji Wendy Marshall.

''Muna zaune a Afrika ta Kudu ne a lokacin. Likitan da ya duba ni ya ce min watakila yana tafiya ne a kan fuskata, na dame shi. Na gode cewa ya yi girma da yawa da bazan iya hadiye shi ba.''

Sue Mazer tana da kawa wadda ta tashi daga barci ''duk fuskarta da cizo kamar na sukar allura a duk fuskarta sakamakon wani kwan gizo-gizon da ya kyankyashe da daddare a sama da gidanta''.

Bayanai irin wadannan tabbatacciyar sheda ce da ke nuna cewa gizo-gizo zai iya hawa fuskar mutumin da yake barci, har ma a wani lokaci ya iya shiga baki.

Mudassirul Waris ya ce a lokacin da wata safiya yana wanke bakinsa da burushi sai ya rika jin wani wari a bakin, sai ya tofar inda ya ga wani abu kamar kafafun gizo-gizo''.

Haka shi ma Paul Dixon ya tuna wani lokaci da yake a zaune a wani wuri budadde a cikin gida. ''Lokacin da na tashi daga barci sai na ji wani abu a bakina tsakanin hakora na na kasa da kuma dadashina, da na sa dan yatsana sai kawai na ga na fito da dan karamin gizo-gizo,'' ya ce. ''Yana faruwa.''

Hakkin mallakar hoto Alamy

Idan wannan labarin yana sanya wa wasunku shakku, to watakila lokaci ne da ya kamata mu gayyato Dave Clarke shugaban sashen kula da kwari da dabbobi marassa kashi a gidan namun daji na Landan.

''Yawancin dabbobi ko halittun da ke kashe wasu ba za su taba takalar duk abin da ya fisu girma ba, saboda karshenta su abin zai cuta,'' in ji Clarke

Gizo-gizo yana da saurin ji da kiyaye duk inda motsi da kuma zafi suke, saboda abu ne mai wuya ya fadawa dan adam ba tare da ya sani ba. '' Ba su da wata sha'awa a kanmu sam-sam,'' ya ce.

'Yar Karen Collins mai shekara takwas ta kara jaddada wannan magana ta kwararru, ta Clarke.

''Gizi-gizo ba wawa ba ne da zai yadda mu cinye shi,'' ta ce. ''Amma dai ko ba komai munshari ma ya isa ya kore shi!''

Duk da yadda wadannan bayanai za su iya kwantar mana da hankali, duk da haka ba za a iya kawar da yuwuwar gizo-gizon ya iya shiga bakin mutum ba bisa tsautsayi, musamman ma idan za mu hada da kamar kiyashi ( in ji Jan Tegner da Sabine Lafazani). To amma sau nawa hakan za ta iya faruwa?

Craig Beattie ya ji cewa akiyasi sau bakawai aka samu wannan hadari inda gizo-gizon ya shiga bakin mutum.

Ann Aylmer ta yarda cewa sau bakwai din ne, amma ta ce wannan shi ne yawan gizo-gizon da muka taba ci a rayuwa.

A'a in ji Sara Winardi da Janelle Loader da Bobbi O'Dwyer da Susie Que da Adalia Kroblen: alkaluman na daidai sau takwas ne a rayuwa.

Amma shi kuwa Jon Parker bai yarda da duk wannan ba, inda ya ce, ''ta yaya za mu sani?''

Hakkin mallakar hoto Ed ZeteraAlamy
Image caption Wannan gizo-gizon mai farar jela wani lokaci yana cizon mutane idan suna barci

A gaskiya kididdigar wadannan alkaluma kamar zargi ne kawai.

Kamar yadda Kenneth Knutsen ya ce, wannan magana ta samo asali ne daga wata kasida da aka wallafa a 1993 inda wata marubuciya Lisa Holst ta hada alkaluma na bogi ta nuna wasikun email da ta samu da ake gaya mata faruwar hakan.

A kan hakan Knutsen ya mai da mata martani da cewa, '' wannan labarin kanzon kurege ya sa bayanin ya zama karyar da aka fi yadawa a intanet.''

To amma wannan martani na Knutsen ba shi ne na karshe ba.

Maganar cewa wannan bayani na shigar gizo-gizon bakin mutane ta samo asali ne daga Lisa Holst an ba da rahotonta a wata kasida a shafin intanet na snopes.com, shafin da aka samar musamman domin tantance duk wani labari da jita-jita da ake yada wa a intanet.

Kuma kasancewar wannan shafi bai kai ga iya tantance gaskiyar cewa wannan labari ya samo asali daga Holst ba ko kuma kasidar da aka ce ta rubuta ba, shi kansa kenan akawai alamar cewa yana bukatar ya duba yadda shi kansa yake.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is it true that we swallow spiders when we sleep?