Matan da suka fi maza basira

Hakkin mallakar hoto nottsexminer cc by 2.0

A tsakanin halittu yawanci a kan fifita maza a kan mata idan ana maganar bajinta da basira musamman wajen neman abinci ga iyali, to amma lamarin ya sha bamban ga wani tsuntsu jinsin kanari.

Melissa Hogenboom ta yi nazari kan wannan tsuntsu (great tits).

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Tana lura da inda wata tsuntsuwar ke boye abinci

Idan ba za ka iya samun abinci ba mai zai hana ka satar wanda wasu da suka ci suka koshi suka adana domin gaba?

Dabara ce amma kuma mai kama da cetar kai a wurin wannan jinsin tsuntsu mai kama da kanari.

Kamar yadda ake dauka idan ana maganar samawa iyali abinci walau a tsakanin mutane ko dabbobi, namiji ake kallo da wannan nauyi.

To amma a tsakanin iyali na wannan tsuntsu mata ne a gaba idan ana maganar ceto iyali a lokacin da aka shiga yanayi na kamfar abinci, kamar yadda wani sabon bincike ya gano.

Wannan wani fanni ne da za a iya cewa mata sun dara maza, wadanda suke da iko a cikin iyalin wannan tsuntsu kamar wasu halittu.

Shi wannan tsuntsu (great tits) yana da wasu dangoginsa da suke kama da juna (marsh tits), wadanda suka lakanci tattali da tsimi na abinci.

Su wadannan dangi suna adana abinci ne a lokacin da ake da yalwarsa, domin amfani da shi a lokacin sanyi, lokacin da tsuntsaye ke wahalar samun abinci.

To su wadancan tsuntsayen na farko (great tits) ba su da irin wannan basira ta boye abinci kamar wadannan 'yan uwa nasu.

A maimakon haka abin da suka kware musamman matansu shi ne gano inda wadannan dangi nasu suka boye abinci, su je su sace.

Sabon nazarin da aka yi, wanda aka wallafa a mujallar halayyar dabbobi (Behavioral Ecology and Sociology), ya nuna cewa matan wadannan tsuntsaye sun fi mazansu sosai kwarewa da basira a wannan dabara ta gano inda aka boye abinci.

Masu nazarin sun ce, wannan muhimmin abu ne a wurin matan, domin mazansu wadanda suke iko da iyali su ne suke samo abinci a lokacin da ake da yalwarsa.

To amma a lokacin huturu, lokacin da abinci yake matukar wuya, sai matan kuma su rika amfani da basirarsu wadda su kuma mazan ba su da ita.

Hakkin mallakar hoto blickwinkelAlamy
Image caption Satar abincin wasu lamari ne na ko a mutu ko a yi rai

Cewa matan sun fi mazansu wannan basira abu ne da ya bai wa jagoran wannan bincike Anders Brodin na jami'ar Lund ta Sweden mamaki.

Ya ce, ''abin mamaki ne da ba a saba gani ba a tsakanin mata da maza na tsuntsaye, kuma a ce mace ce ma ta fi namiji.''

A tsakanin dabbobi masu shayar da 'ya'yansu nono abu ne da aka sani cewa maza sun fi matansu basira, amma a cikin tsuntsaye ba kasafai ake ganin bambanci ba tsakanin maza da mata.

''Yadda maza suke da iko kuma suka fi samo abinci, wanda kuma su suka fi cancanta a ce sun gano inda abincin yake, amma kuma sai ga shi a nan mata ne suke iya gano inda suka ga an boye abinci, har kuma su dawo daga baya su dauke,'' kamar yadda Brodin ya kara bayani.

Domin gano wannan dabara ta wadannan tsuntsaye, Brodin da abokin aikinsa, sun kama wadannan tsuntsaye guda 16, maza rabi mata rabi, sanna suka sanya su a wani wurin kiwon tsuntsaye na cikin gida.

Daga nan kuma sai aka sanya kowanne daga cikinsu a cikin keji shi kadai, wanda daga cikinsa za su iya ganin yadda wasu tsuntsayen danginsu wadanda suka iya boye abinci, su 12, a wani wuri mai bishiyoyi kamar na gaske, masu 'yan kofofi da za su iya boye abinci.

Dukkanin wadannan kofofi na boye abinci sun yi kama da juma, saboda haka akwai bukatar basira kafin a iya gane wacce aka boye abinci a cikinta.

Daga nan ne masu binciken suka gano cewa, matan ba ma sun fi mazan basirar gane inda aka boye abinci ba, suna da basira kamar yadda su wadancan dangin nasu suka kware wajen boye abinci.

Brodin ya ce, wannan ma kadai wata basira ce ta a-zo-a-gani.

To amma kuma a dawa fa magana ce ta wayo da natsuwa.

Domin idan ita waccan tsuntsuwar da ta kware waje boye abincin ta ga wannan mai sacewa tana ganinta lokacin da take boyewa, to sai ta sauya wuri, ta wani wajen daban ta boye.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Sneaky female birds outwit males