An gano gawarwakin zakin zamanin da

Hakkin mallakar hoto Academy of Sciences of the Republic of Sakha Yakutia

An gano wasu gawarwakin 'ya'yan zaki biyu da suka kame a cikin kankara a Siberia (yankin arewacin Asia), wanda yake tsakanin yankin Turai na Rasha da Alaska, sama da shekara 12,000.

Kara Segedin ta yi nazari a kai.

Bayan dubban shekaru da suka makale a karkashin kankara, har lokacin da aka gano su fuskokinsu na nan fes da gashi, kusan za ka iya ganin alamun dukkanin sauran halittun jikinsu.

Hakkin mallakar hoto Academy of Sciences of the Republic of Sakha Yakutia

Wadannan 'ya'yan zakuna da aka sanya musu sunan gabar ruwan kogin Siberiya, inda aka gano su, wato Uyan da Dina, su ne cukakkun gawarwakin nau'in zakin kogo da aka taba ganowa.

Za su taimaka wajen sanin yadda jinsinan halittun da suka bace sama da shekara 12,000 suke.

A lokacin bazarar wannan shekara ta 2015 ne ambaliyar da aka yi a kan hanyar kogin Uyandina ta share saman yankin kankarar wurin da gawarwakin zakunan suke a binne.

Wasu ma'aikata 'yan kwangila ne da ke neman hauren irin giwar nan baka suka yi dacen ganinsu.

Wani ma'aikaci mai suna Yakov Androsov, shi ne ya ga alamunsu ta wata tsagar kankara.

Hakkin mallakar hoto Academy of Sciences of the Republic of Sakha Yakutia
Image caption Yakov Androsov wanda ya gano 'ya'yan zakin, a hannun dama

Ganin irin abin da suka gano, nan da nan sai Androsov ya sanya 'ya'yan zakin a cikin kankara domin kada jikinsu ya saki daga daskarewar da ya yi.

Bayan tsawon shekaru da suka yi a daskare cikin tsananin sanyin kankara na Siberia abin mamaki gawarwakin nasu suna cikin yanayi mai kyau.

''Gashin jikinsu, da kafafu da jela da kunne da idanuwa, har ma da gashin bakinsu suna nan,'' in ji Androsov.

Ko da ike dai ba za su iya cewa ga shekarun wadannan 'ya'yan zaki ba, amma Androsov, ya ce binciken wadanda aka taba ganowa a baya, ya nuna alamun sama da shekara 12,000.

''Abin da ake ganin ya yi sanadin mutuwarsu shi ne ruftowar kasar kogon da suke ciki,'' in ji Androsov.

Ga alama suna tsakanin sati biyu da uku ne da haihuwa a lokacin da suka mutu, domin hakoransu na jarirai ba su ma fito ba, kamar yadda Albert Protopopov shugaban sashen nazarin bakar giwa na jami'ar kimiyya ta Jamhuriyar Sakha (yakutia).

'Yan zakunan sun kai girman kosasshiyar kyanwar gida, kuma ya ce ba a san ma ko sun ma bude idanu ba tun a lokacin da aka haife su.

Kafin yanzu duk wani abu da muka sani game da irin wannan nau'i na zakin kogo, mun samu ne daga irin zane-zane da abubuwa na zamanin jahiliyya da kuma kasusuwan tarihi da ake tonowa a karkashin kasa.

Wannan dabba wadda take daya daga cikin manyan dabbobi na zamanin da ta je ta samo asali ne a Turai daga Afrika kusan shekaru 700,000 da suka wuce, inda a hankali a hankali ta yadu zuwa yawancin yankin arewacin Turai da Asiya (eurasia).

Zakin na kogo wanda ya kai girman damisar Siberia ta yau, a da ya kasance yana yawo a ko'ina daga yankin Biritaniya zuwa Yukon da ke Kanada.

Hakkin mallakar hoto Academy of Sciences of the Republic of Sakha Yakutia
Image caption Ana auna tsawon daya daga cikin 'ya'yan zakin

Yanzu dai ana shirin gudanar da wani cikakken bincike a kan wadannan gawarwaki na 'ya'yan zaki, inda masana kimiyya daga sassan duniya daban-daban suke son bayar da gudummawa.

Bayan gano ainahin shekarun zakunan, Protopopov, yana fatan abubuwan da za a gano za su yi karin gaske kan yadda yanayin rayuwarsu yake, da iyalansu da abin da suke ci da kuma asalin nau'in.

Valery Plotnikov na makarantar ta Jamhuriyar Sakha, ya tsara wani shiri na bazara inda za a je wurin da aka gano su domin sake gudanar da karin bincike.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan A pair of cave lion cubs has been found mummified