Wace dabba ce ta fi barci a duniya?

Hakkin mallakar hoto Frans Lanting StudioAlamy

Yawancinmu za mu yi tunanin dabbar nan ce malalaciya da ake kira sloth da Ingilishi, ko kuma 'yar lelen kyanwarmu. Amma wadanda suka zama na daya a wannan bajinta ta sharar barci wasu ne da ba za ka yi tsammani ba.

Ella Davies ta yi bincike a kai.

Dabbobi suna barci ta hanyoyi daban-daban. Amma mu mun fi daukar barci a matsayin yanayin da dabba take shiga na rashin katabus ko motsi, idanunta a rufe, kuma jikinta duk ya saki.

Sai dai wannan ba ita ce lallai ka'idar barci ba, domin wasu tsuntsayen da suke gyangyadi za su iya shawagi ko tashi suna barci da rabin kwakwalwarsu.

''Barci wata hanya ce da dabbobi ke samu su girgije, su kara kuzari,'' in ji Dakta Jerome Siegel darektan cibiyar bincike kan barci ta jami'ar California ta Amurka.

Wasu dabbobin sun fi wasu shara barci, amma Siegel ya ce wannan ya dogara ne ga lokacin da suka dauka suna cin abinci.

Ya ce, ''dabbobin da suke cin abinci maras kitse sosai, ba sa barci sosai, ko da yake zai iya kasancewa yadda bukatar dabba take.''

Gaba daya dai, ana ganin dabbobin da suke cin ciyawa ba sa barci kamar dabbobi masu cin nama, saboda su masu cin ciyawa, suna bukatar lokaci mai yawa na cin abinci domin samun karin karfi daga abincin.

An fi ganin hakan ma a kan dabbobi masu ci sosai kamar su rakumin dawa. A shekarun 1970, masana kimiyya sun lura cewa rakumin dawa da ke sake a daji yana barci ne na minti biyar zuwa 30 a duk rana.

Hakkin mallakar hoto SILBERNICUSAlamy
Image caption Rakumin dawa na barci

Rashin barci sosai zai iya kasancewa wani tsari na kariya kamar yadda Dakta John Lesku daga jami'ar La Trobe da ke Melbourne a Australia ya ce.

''Barci na kankanin lokaci a wurin dabbobin da suke da rauni zai iya zama wata hanya ce ta sanya ido a kan masu kawo musu farmaki.'' In ji masanin.

Sabanin haka kuwa, su dabbobin da ke kai farmaki kan wasu dan kankanin lokaci suke dauka na lura da bayansu, musamman a tsakanin masu zamantakewa da 'yan uwa.

An san yadda zaki ya yi suna wajen shafe rana yana kwance, inda yake barcin kusan sa'a 10 zuwa 15 a rana idan a tsare yake misali a gidan namun daji.

Amma maimakon yayi ta shara barci na tsawon lokaci, zaki yana da dabi'ar barci a gutsuttsure, wato ya yi na dan kan kanin lokaci, ya farka sannan ya koma.

Siegel ya ce yana yin hakan ne domin kada ya rasa damar samun abincinsa.

Daktan, ya ce, ''dabbar da ke jin yunwa ba ta bukatar ta yi barci mai tsawo idan da abinci, idan kuma ba abinci sai ta yi barci sosai.''

Ya kara da cewa, ''dabbobin da ba sa daukar matakin da ya dace ba lalle ba ne su yada wannan dabi'a ga jinsinsu.''

Abin lura ne a sani cewa masana kimiyya kadan ne suka yi kokarin za ma, duk tsawon dare su lura da zakin da ke barci, watakila domin kada ya tashi ba su san ya katse barcin ba.

A zahirin gaskiya ma ka iya gano dabbar dajin, na daga cikin kalubalen da ke tattare da fahimtar yanayin barcinsu.

Hakkin mallakar hoto Gabriel RojoNPL
Image caption Nau'in katon damo (giant armadillo) yana barci kamar yadda ya saba

Misali akwai akwai wani nau'in damo katoto (giant armadillos) da aka sanya a jerin dabbobin da suka fi barci, domin yana zama a cikin raminsa tsawon akalla sa'a 18.

Amma kuma babu tabbas cewa yana kwashe duk tsawon wannan lokacin ne yana barci.

Kamar yadda wani nazari da aka yi a Victoria ya nuna, wannan dabba tana barci ne na kusan sa'a 14 da rabi.

''A gaskiya muna ganin suna kuma cin abinci a lokacin da suka kwanta, domin a ko da yaushe za ka ga raminsu yana kusa da ramin kwari, kuma sashen da suke kwanciya na ramin nasu yawanci yana kusa da ramin kwarin ne, '' in ji Dakta Arnaud Desbiez shugaban nazarin rayuwar dabbar a Pantana (yanki mai dausayi na Brazil da Bolivia da Paraguay).

Idan muka sanya ido a kan abin da dabba take yi, lura da yanayin da take shi ne yawanci ke tabbatar mana ko barci take yi ko kuma ba barci take yi ba.

Misali rakumin dawa yana dora kansa ne a duwawunsa. Ita kuwa wata 'yar karamar dabba mai girma kamar kyanwa da ake kira koala da Ingilishi wadda kuma ana samunta ta ne a kasar Australiya, ana cewa tana zama a farke ne tsawon sa'oi biyu kawai a rana.

Hakkin mallakar hoto imageBROKERAlamy
Image caption Wani jinsin damo mai gashi (hairy armadillo)

Kamar yadda wani bincike a kan dabbar (koala) da aka yi a Victoria ya nuna, tana barci ne na kusan sa'a 14 da rabi sannan kuma ta yi wasu sa'oin kusan biyar tana hutawa, domin abincin da take ci wanda ganye ne yana dadewa kafin ya narke kuma ba ya ba ta wani kuzari sosai.

A wani nazari da aka yi a 2013, an sanya wa irin wannan dabbar ta kola ta daji wata na'ura domin tantance aikinta na kullum, amma sai ya kasance na'urar ba ta iya tantance yanayin barci da na hutu.

A bisa wannan dalilin cikakkun bayanan da aka samu kan barcin dabbobi an same shi ne daga wadanda aka kama ko ake tsare da su.

Dakta Lesku ya ce, dabbobin da a yanzu aka san sun fi tsawon barci su ne, wani babban damo mai gashi (armadillo) wanda yake barcin sa'a 20 da minti 24.

Sai kuma wani dan mitsitsin bera (little pocket mouse) wanda shi kuwa yake barcin sa'a 20 da minti shida.

Lesku ya ce, ''ko wannan ma abu ne da ya kamata a yi hattara da shi, domin wadannan fa dabbobin dawa ne da aka kamo aka sanya su a wani sabon muhalli, na dakin binciken kimiyya tare da abinci.''

Hakkin mallakar hoto All Canada PhotosAlamy
Image caption Karamin jan jemage

Misali, an yi nazari a kan wani dan karamin jan jemage ta irin wannan hanya a 1969, kuma ya kasance wanda ya fi dogon barci, inda ya samu sa'o'i 19 da minti 54 yana barci a cikin sa'o'i 24.

Amma kuma an makala shi ne a jikin kwamfuta maimakon a barci a irin wurin da ya saba makalewa yana reto, sannan kuma an sauya yanayin zafi da sanyi na wurin.

A kan haka ne Lesku, ya ce, ''a gani na wannan dabbace da aka sauya mata yanayin da ta saba rayuwa wanda kuma ba zai sa ta zama wakiliyar sauran 'yan uwanta da ke dawa ba.''

Watkila ma ba barci take yi ba sam-sam, kila ma ta yi lamo ne kawai.

Dabbobi da yawa sukan shiga irin wannan yanayi na lamo, domin tattalin kuzarinsu.

Jemage yakan yi hakan a lokacin sanyi da kuma lokacin zafi, sanna kuma wasu dabbobin ma sukan yi hakan a kowace rana.

Hakkin mallakar hoto Frans Lanting StudioAlamy
Image caption Malalaci (sloth), ko sarkin barci

Akwai wata dabba mai girma kamar kyanwa da ake kira American badger da Ingilishi, da kuma wani bera mai jela mai kauri kamar kurege (fat-tailed mouse possum), wadanda dukkansu sukan kai tsawon sa'a 14 suna wannan yanayi mai kamar barci, kamar yadda wani bincike na shekara ta 2014 ya nuna

Shi wannan yanayi na lamo ya bambanta da barci, yanayi ne da kusan jiki gaba daya yake rage aiki domin tattalin kuzari ko karfinsa.

Domin gwada ainahin tsawon lokacin da dabbobi ke barci a daji masana kimiyya sun fara gwaji a kan dabbar da ta yi fice wajen dogon barci, wadda ta yi kama da biri kuma tana da zako-zakon farata, ana kiranta 'sloth' da Ingilishi.

Idan ba a daji inda ta saba take ba, wato idan an tsare ta ne, misali a gidan namun daji ko wuri na binciken kimiyya an lura tana barci na sama da sa'a 15, amma kuma a wani bincike da aka yi a 2008 masu binciken sun gano wadda take a dawa ba ta dogon barci kamar ta tsare.

Da aka sanya wa dabbar na'ura a gwajin da aka yi a Panama an gano tana barcin kasa da sa'a goma.

Kusan tsawon barcinsu daya da zaki kuma ba ta kai waccan dabbar da ake kira kaola ko ma duk dabbar da ba a daji take ba, wato watta ake tsare da ita.

Amma duk da haka shafe kashi 40 cikin dari na rana ana barci, ba karamin abu ba ne, musamman ma ga dabbar (sloth) da take cin 'ya'yan itatuwa da ganye wadda kuma kyanwa da mikiya za su iya kamawa.

Wani dalili kuma zai iya kasancewa dabbar tana iya sauya launi ne ta saje da inda take, wanda wannan dabi'a ce ta yaudara domin kare kai daga makiya.

Idan haka abin yake to sai a ce ba za a karbe mata kambun da take rike da shi ba na kasancewa dabbar da ta fi dogon barci, duk da cewa hakan ba adalci ba ne.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What is the sleepiest animal on Earth?