Ko ka san kyankyaso na shayar da nono?

Hakkin mallakar hoto Stephen Tobe

Ba uwayen mutane ne kadai suke shayar da jariransu nono ba. Akwai wasu dabbobin da ba za ka taba tsammanin cewa su ma suna shayarwa ba.

Ga bayanin Shreya Dasgupta.

Mun san yadda madara ko nono ke da amfani ga jarirai. Hadi ne na abubuwan gina jiki da kuma sinadaran kariya wadanda jariri yake bukata domin girmansa.

A tarin halittar dabbobi rukuni daya ne kawai ke samar wa 'ya'yansu madara, su ne masu shayarwa (mammals), rukunin da muke ciki.

Madarar wadannan dabbobi da mu mutane muke ajinsu, ana ce mata madarar gaskiya.

To sai dai akwai wasu dabbobin 'yan kadan wadanda suke samar da wani nau'in ruwa ga jariransu wanda ya yi kama da madara.

Wannan madara wadda ita kuma ake kiranta madarar bogi, ba ta yi kama da madarar da muka sani ba a ido ta shanu ko ta mutane, kuma ba ta irin hanya daya ake samar da ita ba.

Amma amfaninta daya da madarar da muka sani, na shayarwa da ciyar da jarirai har su iya kula da kansu.

PIC 1

Hakkin mallakar hoto blickwinkel alamy
Image caption Kurciya na shayar da danta nono

Kurciya ko Tattabara

Tattabara tana da kokari sosai wajen raba reno tsakanin miji da mata. Ba kamar dabbobi da aka sani masu shayarwa ba (ciki da har da mutane), su tattabaru da sauran tsuntsaye na jinsinsu (kurciya da hazbiya), maza da mata suna yin wannan ruwa (crop milk) mai kamar madara domin jariransu.

Tattabarun da sauran tsuntsaye jinsin nata suna da wata halitta a can kasan wuyansu daga ciki, wadda suke amfani da ita wajen sarrafa abinci ya yi laushi kafin ya bi jikinsu.

Kwana biyu kafin tattabarar ta kyankyashe kwayayenta mata da mijin sai su cika wannan halitta da ke wuyan nasu da wasu kwayoyin halitta masu ruwa.

Wannan ruwa ne mai sinadari tattabarun suke dura wa a bakin 'ya'yan nasu, kuma shi za su yi ta ba wa 'yan shilan tsawon kwanaki bayan kyankyasarsu.

Wannan madara ko ruwan na tattabarun yana cike da sinadaran gina jiki, kuma wani bincike da aka yi a 1952 ya nuna cewa girman 'yan shilan yana karuwa da kashi 38 cikin dari idan ana ba su shi.

Akwai wasu nau'in tsuntsayen su ma kamar zalbe da suke da wannan tsarin shayarwa.

Hakkin mallakar hoto Stephen Tobe

Kyankyaso

Wasu nau'ukan kyankyaso suna shayar da 'ya'yansu wata nau'in madara. Daya daga cikin irin wannan kyankyaso shi ne wanda ake da shi a yankin Pacific (pacific beetle cockroach).

Yawancin matan kyankyasai suna yin kwai ne a cikin wani abu mai kama da jaka, wanda suke fitarwa daga jikinsu a lokacin da kwan ya kusa kyankyashewa.

Bayan 'ya'yan sun kyankyashe ne sai fito su bazama neman abinci.

Amma ita matar wannan nau'in kyankyason mai shayarwa (na Pacific),tsarinta na kula da 'ya'ya daban yake.

Maimakon ta yi kwai, jaririn ne yake girma a wata jaka a cikinta wadda ke matsayin kamar mahaifarta.

Dazarar halittar 'ya'yan ta gama cika sai su fara shan nono, a cikin wannan mahaifa, kuma nan da nan sai su girma.

Saboda wannan nono da suke sha a cikin wannan jaka ta cikinta wadda ke matsayin kamar mahaifa, sukan girma su kosa kafin ta haife su.

Hakkin mallakar hoto blickwinkel alamy

Kunamar karya ko Kunamar Littafi

Wannan wata halitta ce mai kama da kunama (pseudoscorpions), sai dai ba ta da karin harbi irin na kunama kawai. Matar kamar ta wancan kyankyason tana yin irin wannan ruwa mai kama da madara.

Matar tana da kwayayenta ne a wani abu mai kama da jaka da yake jikin cikinta.

Dazarar 'ya'yan nata sun kyankyashe sai su zauna a wannan jaka suna shan nonon uwar.

Ko da sun fito daga wurin sun fara tafiya, sukan ci gaba da hawa bayanta tana tafiya da su har sai sun isa dogaro da kansu.

Ita wannan nau'in kunama kamar yadda na ce ba ta harbi domin ba ta da kari, ana samunta te a wurin da ake da littafai da suka yi kura, saboda haka ne ma wasu ke kiranta kunamar littafi.

Hakkin mallakar hoto Nature ProductionNPL
Image caption Matar kifi tana shayar da 'ya'yanta nono

Kifi

Ita nau'in madarar wannan kifi da ake kira discus a Ingilishi ba ta da kamanni irin na madara sam-sam. Tana kama ne da majina wadda matar da mijin duka suke yaba ta a jikinsu, kuma tana dauke da sinadarai masu gina jiki da kariya.

Kwanaki kadan bayan kwayayen kifin sun kyankyashe, sai 'ya'yan su je wurin iyayen nasu, su rika shan wannan ruwa mai kama da majina na jikin iyayen.

A sati biyu na farko iyayen sukan dauki yawancin lokacinsu suna shayar da 'ya'yan abin da kan dauki kusan minti biyar zuwa goma, wanda daga nan kuma sai daya daga cikin iyayen ya bar wa daya 'ya'yan.

Daga sati na uku zuwa gaba, iyayen sai su yaye 'ay'ayn, su kaurace musu na wani lokaci abin da zai tilasta wa 'ya'yan su nemi wani abinci da kansu.

Wannan tsari ya yi kama da yadda dabbobi masu shayarwa da mutane ke yaye 'ya'yansu a hankali bayan sun shayar da su da farko.

Hakkin mallakar hoto Milvus CC by 3.0

Tsutsa

Wannan irin tsutsa tana rukunin dabbobi ne kamar su kwado amma kuma ba ta da kafafuwa. Yawancin nau'inta suna tsare kwayayensu har sai sun kyankyashe sannan su tafi su bar su.

Ita wannan dabba wadda ake samu a kudu maso gabashin Kenya tana da wani tsarin shayar da 'ya'yanta na daban.

A lokacin da kwayayen suka kyankyashe, 'ya'yan ba su da kwari saboda haka suna dogaro ne gaba daya a kan uwarsu.

Domin shayar da 'ya'yan uwar, sai ta sauya fatar jikinta ta sama ta zama kamar wani ruwa-ruwa mai sinadaran abinci masu gina jiki.

'Ya'yan za su rika kankarar wannan fata ne da wani hakori nasu suna sha, cikin sati daya sai su kara tsawo da kusan kashi 11 cikin dari.

Wannan yana sa uwar ta rame sosai, inda bayan sati daya tana shayar da 'ya'yan ta wannan hanya, tana rasa kusan kashi 14 na nauyinta.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Five animals you never knew make milk for their babies