Mutanen da na cin naman 'yan uwansu

Hakkin mallakar hoto JvphotoAlamy

Wasu daga cikin mutanen zamanin da sun rika kashe juna suna cin naman kamar yadda wata sheda ta nuna. Ana ganin binciken ya isa kawar da duk wani shakku a kan ta'adar.

Ga bayanin Melissa Hogenboom

Idan da ana shakku a kan halayyar mutanen zamanin da ta kashewa da cin naman 'yan uwansu mutane, to kamata ya yi a yi watsi da wannan shakku yanzu.

Alamu da shedun da aka tono daga wani wuri na kayan tarihi na da sun tabbatar cewa akwai wasu tarin mutane da aka yayyanka aka cinye su.

Alamun wasu kasusuwa ne na mutane da aka samo daga wani kogo (Gough Cave) a Somerset da ke Ingila, wanda tun a shekara ta 1992 aka tona wurin.

Har yanzu masana kimiyya na ci gaba da gudanar da bincike a kan alamun da suka gani a jikin kasusuwan mutanen.

Hakkin mallakar hoto Natural History Museum
Image caption Alamar yin tsafi da kokon kan mutum a zamanin da

Bincike ya nuna cewa abubuwan da aka gano wadanda suka kunshi kasusuwan mutane da na dabbobi, an ajiye su ne a kogon na wani dan lokaci kusan shekara dubu 15 da ta wuce.

Silvia Bello ta dakin adana kayan tarihi na Landan, ta ce ayarin ma'aikatanta ya gano wasu bayanai wadanda suka fi na da da aka gani.

Ta ce,'' mun gano shedun da ba wata tantama a kansu da suke tabbatar mana da yadda aka rika yayyanka nama da sara kashin mutane da kuma alamar tauna su har da ma fasa kashin domin samun bargo.''

Idan har wadannan ba su tabbatar da hakan ba to akwai kuma alamar da suka gani ta tauna kashi da hakorin mutum.

Hakkin mallakar hoto Natural History Museum

Idan aka tattara wadannan shedu za a ga alamar cewa cin naman mutum wata dabi'a ce ta mutanen zamanin da.

Akwai ma alamar kawata kokon kan mutum bayan ya mutu.

Mutumin da aka wallafa bayanan binciken tare da shi, Simon Parfitt na jam'iar Landan ya ce, ''wani abu da muka gani na wannan zamani da ya ba mu mamaki shi ne, yawan irin yadda ake binne mutane da yadda muke ta samun kasusuwan mutane hade da kayayyakin aikina a wurare da dama.''

Karin nazari da binciken da ake yi sun mayar da hankali ne domin gano yawan yadda ake wannan al'ada ta cin naman mutane a zamanin, da kuma cewa ko ana yayyanka mutanen ne bayan an yi wani bikin tsafi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Our ancestors really were cannibals