Ga halittun da ke rayuwa a fuskarka

Hakkin mallakar hoto eye of science spl

Kusan dukkaninmu muna da wasu 'yan mitsi-mitsin halittu da ke ci da sha da rayuwa a fuskarmu. Wadannan halittu dai ba masu cutarwa ba ne, sai dai suna nuna yadda tarihin halittar mutum yake.

Lucy Jones ta bincika yadda abin yake.

Ba shakka da gano wannan abu za a iya cewa akwai dabbbobi da suke rayuwa a fuskamu.

Ba zaka iya ganinsu ba amma dai suna nan. 'yan mitsi-mitsin halittu ne masu kafa takwas kamar gizo-gizo, wadanda ido ba ya iya ganinsu ba tare da wata na'ura ba. Kusan kowane mutum yana da su. A fuskarmu suke rayuwarsu gaba daya. Su ci su sha su kuma mutu a nan.

To kafin ka ce ba ri ka sayi wani magani na wanke fuska mai karfi domin kawar da su, ka sani cewa wadannan halittu ba abubuwan da za su tayar maka da hankali ba ne.

Domin kusan a iya cewa gaba dayansu ba masu cutarwa ba ne. Kuma saboda yadda suke kusan a jikin dukkanin dan adam za su iya taimaka wa wajen sanin cikakken tarihin rayuwar dan adam.

Hakkin mallakar hoto Science Picture Co.SPL
Image caption Wannan halitta ce da ke rayuwa a ciki da kan fatar mutum

Wadannan 'yan kananan halittu suna da kafafuwa takwas gajeru wadanda suke kusa da kansu. Jikinsu kuma yana da tsawo kamar na tsutsa.

Idan aka kalle su ta madubin binciken kimiyya (microscope) za a ga kamar suna iyo ko linkaya ne a cikin mai, su ba a can nesa ba kuma ba da sauri ba.

Nau'i biyu ne halittun, wadanda kuma suke zaune a wurare daban-daban.

Akwai wadda ke rayuwa a kofofin fatarmu da na gashi (D folliculorum), dayar kuwa (D. Brevis) tana rayuwa ne can ciki-cikin ramin fatar tamu inda yake da maiko.

Fuskarmu tafi sauran jikinmu manyan kofofi da kuma halittar da ke samar da maiko da sauran sinadaran da gashin jikin mu ke bukata, wanda watakila wannan shi ya sa wadannan kananan halittu suka zabi su zauna a fuskar.

Amma duk da haka ba a fuskar kadai suke rayuwa ba, domin akwai su a wuraren al'aurarmu da kuma jikin nono.

Hakkin mallakar hoto Oleksiy MaksymenkoAlamy
Image caption Kusan a kowace fuska halittun suna nan

Tun da dadewa masana kimiyya sun san cewa akwai halittun da ke rayuwa a fuskar mutum, domin an ga daya daga ciki (D. Follicurlorum) a ruwan kunnen mutum a Faransa a shekarar 1842.

A shekara ta 2014 ne kuma aka gano cewa kusan halittun na nan a kusan ko ina a fuskar da wasu sassan jikin mutum.

Megan Thoemmes ta jami'ar jihar North Carolina University a Raleigh da ke Amurka, tare da abokan aikinta kamar sauran masu binciken kimiyya na baya suka gano cewa kusan kashi 14 cikin dari na mutane suna da wadannan kananan halittu, wadanda ake iya ganinsu a zahiri.

Amma kuma sun gano kwayoyin halittar wasu 'yan kananan halittun (demodex) a fuskar dukkanin mutanen da suka yi binciken da su.

Wannan kenan ya nuna cewa bisa ga dukkan alamu dukkaninmu muna da su kuma da yawa a fuskarmu.

Megan Thoemmes ta ce, ''abu ne mai wuya ka iya yin hasashe ko ka ce ga yawan halittun nan, amma dai mafi karanci a iya cewa sun kai daruruwa.''

''Mafi yawan wadannan halittu kan kai dubbai.'' Ta kara da cewa. Za a iya cewa kusan kana da halittar biyu a jikin duk zirin gashin idonka daya.

Sai dai yawan zai iya bambanta tsakanin mutane, saboda haka za ka iya samun su fiye da makwabcinka ko kuma nasa su fi naka.

Haka kuma zai iya kasancewa sun fi yawa a wani bangaren jikin naka fiye da wani bangaren.

Duk da haka kuma ba mu san abin da suke samu a jikin namu ba. Ko mu ce ba mu san abin takamaimai abin da suke ci ba.

Hakkin mallakar hoto Power and SyredSPL

Thoemmes ta ce, ''wasu mutanen suna ganin suna cin kwayoyin halitta na baktiriya ne da ke fatarmu, yayin da wasu kuma ke ganin suna cin matattun kwayoyin halitta na fatar ne. Wasu kuma suna tunanin suna cin kwayoyin maikon can cikin fatarmu ne.''

A yanzu Thoemmes da abokan aikinta suna gudanar da bincike kan nau'in kwayoyin halittun da ke cikin cikin su halittun na fuskar tamu domin ta haka za a iya gano irin abincin da suke ci.

Haka kuma ba mu san ta yadda suke haihuwa ko yaduwa ba, kamar yadda muka san wasu kananan halittun suna yi ta hanyoyi daban-daban.

Misali, saduwa tsakanin 'yan uwa na kusa ko ta hanyar kashe uwa ko kashe uba, ko kuma mace tana cinye miji kafin saduwa ko lokacin saduwa ko kuma bayan saduwa.

Amma dai ya zuwa yanzu muna ganin su wadannan halittu ba su da kai wannan tsananin ba.

''Ba mu taba sanin suna cinye junansu ba,'' in ji Thoemmes. ''Alamun da muka gani shi ne cewa suna fitowa daddare su sadu sannan su koma cikin ramukansu.''

Abin da muka sani kawai shi ne game da kwansu.

Hakkin mallakar hoto Power and SyredSPL
Image caption Kai da kafar wata halittar ta fuskar mutum

''Mun dauki hoton bidiyon wata daga cikin halittun tana yin kwai.'' In ji Thoemmes.

Matan halittun suna yin kwansu ne a bakin ramin da suke zaune, kuma ga alama ba sa yin da yawa.

''Kwansu yana da girma, domin ya kai kusan daya bisa uku na girman jikinsu, wanda ba shakka abin dubawa ne,'' in ji Thoemmes.

''Yana da girman da za a ce da wuya su iya yin abin da ya wuce daya a lokaci, domin ban ga ta yadda fiye da daya zai iya zama a cikinsu ba.''

Wani abin kuma shi ne su wadannan halittu ba su da dubara.

Hakkin mallakar hoto Power and SyredSPL
Image caption Wata halittar ce ta fuska a na'urar kara ganin girman abu

Duk da haka kuma suna bukatar su yi kashi, abin da ya sa ake ganin kamar suna fashewa ne da kashin a cikinsu a karshen rayuwarsu.

Sai dai Thoemmes ta ce, ''ana ganin wannan kamar an zuzuta yadda rayuwar tasu take ne.''

Lalle kam suna tara kashinsu har zuwa karshen rayuwarsu, domin idan suka mutu, jikinsu yana bushewa, sai duk kashin nasu ya watse a fuskarka.

''Ba wai lalle suna fashewa ba ne, amma dai gaskiya ne kashinsu na taruwa ya dade sai kuma ta fitar da wata halitta ta baktiriya,'' in ji Thoemmes.

Ta ce, ''ba wai fitar bayan gida ba ne kashi-kashi, a'a abu ne da yawa yake fita bayan ya taru.''

Za a ga wannan kamar wani abin tsoro ne amma ba wani abin cutarwa game da halittun nan.

Hakkin mallakar hoto Dr Harout TanielianSPL
Image caption Kwayar halittar Rosacea ta kan kai ga bata fuska

Thoemmes ta ce, ''bana jin suna cutar da mu ta yadda za mu gane,''

Ta kara da cewa, ''idan da suna cutar da mu sosai da mun ga alamun hakan a jikin mutane da yawa.''

Abin da ake dangantawa da su kawai shi ne, wata cutar fata (rosacea), wadda yawanci takan shafi fuskar mutane, inda za ka ga fuskar mutum ta yi dabbare-dabbare na ja, kuma suna jin zafi.

Bincike ya nuna cewa mutanen da suke da wannan cuta, suna da wadannan halittu da yawa a fuskarsu.

Maimakon daya ko biyu a fadin murabba'in santimita daya na fatar, yawansu sai ya kai goma zuwa ashirin.

Amma wannan ba yana nufin za su haddasa wa mutum wata matsala ba ne.

Hakkin mallakar hoto Sheila TerrySPL
Image caption Kasan fatar mutum da maikon cikinta da kofofin gashi

''Su dai wadannan kwari ana damawa da su a wannan cuta amma ba su ne suke haddasa ta ba,'' in ji Kevin Kavanagh na jamia'r Maynooth ta Ireland,a wani nazari da aka wallafa sakamakonsa a 2012, inda ya ce abin da yake jawo cutar sauyi ne a jikin fatar mutane.

Fatar takan sauya bayan wani lokaci saboda tsufa ko shiga wani sauyin yanayi (sanyi ko zafi), inda fatar za ta iya bushewa ko makamancin hakan.

Wannan ne yake sa sinadarin da yake sa fatarmu ta kasance da maiko ya tabu.

Ana ganin su wadannan 'yan kananan halittu ko kwari suna cin wannan sinadari neidan aka samu wannan yanayi, daga nan kuma sai a samu karuwar su halittun sosai.

''Wannan sai ya sa a rika jin kaikayi ko zafi a fuskar saboda an samu karuwar halittun da yawa,'' in ji Kavanagh.

Kusan akawi dangantaka tsakanin alamun wannan cuta (rosacea) da tarin baktiriyar da halittun suke fitarwa idan suka mutu.

Kavanagh ya ce, ''idan halittun suka mutu, sai duk abin da ke cikinsu ya fice. Kuma wannan yana kunshe da tarin halittar baktiriya da dagwalo da ke haddasa kaikayi da zafi a fuskar mutum.''

Za kuma a iya samun alaka tsakanin garkuwar jikin mutum, wadda ke kare mu daga cutuka.

Thoemmes ta ce an gano cewa wadannan halitttu suna da yawa a jikin mutanen da suke dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS ko SIDA) ko kuma cutar daji.

Ba a san irin alakar da ke tsakanin jikinmu ba da wadannan halittu. Amma dai mun tabbata cewa ba ma su cutarwa ba ne.

Za ma su iya kasancewa masu amfani ga jikin namu, kamar misali za su kawar da fatar da ta mutu daga fuskarmu ko kuma su cinye kwayar baktiriya ta fata mai cutarwa.

To amma idan kuma kana son ka raba kanka da su fa. Za ka iya?

Hakkin mallakar hoto David ScharfSPL

Duk da cewa akwai yadda za mu iya kashe wadannan kwari da ke fuskarmu, to amma fa ba za mu iya raba kanmu da su ba gaba daya har abada.

Bayan sati shida suke sake dawowa in ji Kavanagh. ''Muna daukarsu ne daga mutanen da muke mu'amulla da su.

Sannan kuma muna daukarsu daga zanin gado da matashin kai da kuma tawul.

Akwai kuma kyakkyawar shedar da ke nuna muna yada su a tsakaninmu.''

Abin dai kamar akwai wani abu na musamman ne da suke so a fuskarmu, domin ko da ka kashe su, za su sake dawowa saboda kusan suna nan a ko'ina kuma suna son zama a fuskarka ne.

Ga alama ma tun muna jarirai muke kamuwa da wadannan kwari, domin kamar yadda Thoemmes ta ce, ''an ga alamunsu a cikin tsokar jiki da ke samar da nono ta uwa.''

Saboda haka take ganin za su iya yaduwa daga jikin uwa zuwa jariri, kila ta hanyar shayarwa ko lokacin lokacin haihuwa.

Daga nan kuma sai mu samu karinsu daga mutanen da muke tare da su yayin da muke girma.

Thoemmes ta gano cewa akwai wadannan halittu da yawa a jikin mutumin da ya wuce shekara 18 fiye da dan 18 din.

Hakkin mallakar hoto eye of science spl
Image caption Halittun da ke fuskarmu ta na'urar kara ganin girman abu

Sannan kuma Thoemmes tana ganin wadannan kwari sun kasance da mu tun shekara 20,000, tun da mun samo asali ne daga kakanninmu na zamanin da.

Haka kuma za ta iya kasancewa mun same su ne daga wasu dabbobin domin wata daga cikinsu (musamman D. Brevis) ta yi kama da wadda ke jikin kare.

Dangantakar dan adam da kare da karen daji (kerkeci) ta dade, kuma Thoemmes tana ganin ai kakanninmu sun dade tare da wadannan dabbobi, inda suke farauta da su, kuma kila daga nan ne suka debi kwarin.

Bayan dangantakarmu da wasu dabbobi, wadannan halittu za su iya bayyana da yawa daga cikin dangantakarmu da su, domin kwayoyin halittarsu suna dauke da wata lama ta tarihinmu.

Hakkin mallakar hoto Christina GandolfoAlamy
Image caption Kila karnuka ne suka yada mana halittun na fuska

Lokacin da Thoemmes ta yi nazari a kan kwayoyin halittar kwarin (DNA), ta gano cewa kwarin da ta debo daga mutanen Sin (china) sun bambanta sosai da wadanda ta samo daga mutanen nahiyar Amurka ta kudu da ta arewa.

Saboda wannan bambanci, idan aka yi bincike a kan halittun za a iya gane yadda kakanninmu na zamanin da can suka yi hijira a duniya, sannan kuma za a iya sanin a cikin al'ummomin zamanin nan wadanda suka fi dangantaka da juna.

''Watakila za mu iya gano dangantakar mutane, wadda ba mu iya ganowa ba a da,'' in ji Thoemmes.

Mai binciken ta fi ma sha'awar samun bayani game da mulkin mallaka na Amurka ta tsakiya (latin) da kuma ta kudu.

Ta ce, ''akwai rade-radi da shaci-fadi a game da ainahin mutanen da suka yi wa Brazil mulkin mallaka suka kuma yi auratayya da su.''

Hakkin mallakar hoto Steve GschmeissnerSPL
Image caption Halittar da ke zama a jikin silin gashin ido

Halittun za kuma su ba mu damar waiwayar baya, mu bincika yadda mutum ya faro (halitta).

Idan sun dade tare da mu, zai iya kasancewa garkuwar jikinmu ta sauya saboda haka, wato kenan sun taimaka wajen yadda muke yakar cutuka.

''Ba shakka suna da tasiri a jikinmu kamar yadda muke da shi a kansu,'' in ji Thoemmes.

Domin, ''zai iya kasancewa akwai wani abu da garkuwar jikinmu ke yi saboda su, wanda sakamakon hakan kuma yake da wani tasiri a kan lafiyarmu da garkuwar tamu.''

Zuwa yanzu dai wannan hasashe ne kawai, amma ko da ba wanda ya tabbata gaskiya, labarin wadannan halittu ko kwari da ke rayuwa a fuskarmu, tuni ne cewa, mu mutane gida ne ko matattara ta tarin jinsin halittu daban-daban.

Hakkin mallakar hoto Steve GschmeissnerSPL
Image caption Kwayar halittar baktiriya a fatarmu

Wasu halittun kamar kwarkwatar kai da kuma sukan bayyana a jikin mutane daga lokaci zuwa lokaci ko kuma a ce suna rayuwa a jikin wasu mutane.

Amma sauran kwari kamar wadanda ke fuskar mutane (demodex) da 'yan kananan halittun da ke cikin cikinmu suna tare da mu duk tsawon rayuwarmu.

A takaice ma kusan su ne mu, domin sune kashi 90 cikin dari na kwayoyin halittar da suka yi jikinmu.

Anan akwai darasi mai sauki da za mu fahimta. Darasin shi ne;

ka sani cewa ba fa kai kadai ba ne tsuranka kamar yadda kake daukar kanka.

Kai wata al'umma ce sukutuk wadda ke tafiya da magana, duniyar halittu ce gaba daya a cikin jiki daya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan These microscopic mites live on your face