An hallaka sananniyar zakanya a Kenya

Hakkin mallakar hoto aditya dicky singh alamy

An sanya wa daya daga cikin fitattun garken zakuna na duniya guba, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla daya daga cikin manyan matan garken a kasar Kenya.

Ba a san wanda ya sanya wa zakunan gubar ba, amma a baya manoman sukan sanya musu guba domin kare dabbobinsu daga hare-haren namun dajin.

Zakunan na daga cikin wadanda BBC ke nuna su shekara da shekaru a shirye-shiryenta na talabijin na dabbobin dawa.

Daga cikin matan garken wadda ake kira Bibi ita ce aka samu ta mutu bayan ta ci guba.

Hakkin mallakar hoto BBCSimon Blakeny
Image caption Bibi ta dauko wani daga cikin 'ya'yanta a watan Yuni na wannan shekara

A ranar Litinin bakwai ga watan nan na Disamba ne aka gano Bibi ta mutu a yankin gandun daji na Masai Mara na kasar ta Kenya.

Masu dauko rahotanni kan namun daji na BBC, wadanda suke wurin, sun ce an ga zakanyar ne kwance kumfa na zuba daga bakinta tana haki da kakari.

Daya daga cikin masu daukar hotunan dabbobin ya ce, ''ba a ga zakanyar a cikin sauran garken ba ranar Lahadi shida ga watan na Disamba, kuma muna ganin ba wanda ya san inda take har sai lokacin da take gargarar mutuwa.''

Rahoton ya ce ana kyautata zaton akalla wasu zakunan guda shida a cikin garken su ma sun ci gubar.

Samun labarin ke da wuya aka sanar da jami'an asusun da ke kula da namun daji na kasar, David Sheldrick Wildlife Trust, cewa, ''an ga zakunan suna wani yanayi na daban, tare da faduwa da kakari da haki kuma kumfa na fati daga bakinsu,'' wadanda su kuma nan da nan suka garzaya wurin.

Jami'an sun bayyana cewa har zuwa lokacin da aka turo da wannan rahoto ba a ga wata daga cikin matan garken ba mai suna Sienna.

Danta mai shekara biyu shi ma ya ci gubar, amma yana samun sauki daga maganin da ake yi masa.

Hakkin mallakar hoto

Mai daukar hoton namun daji na BBC Mark MacEwan yana wanda yake wurin ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewa,'' daya daga cikin abubuwa mafiya muni da na taba gani a aikina da safiyar nan, a daren jiya an sanya wa daya daga cikin garken zakunan da ke dajin Mara guba.''

BBC ba ta tabbatar da wanda ya sanya wa zakunan gubar ba.

Amma kuma hukumar kula da namun daji ta Kenya ta kama mutane uku, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci dauri mai tsanani ko kuma ma daurin rai da rai a kurkuku.

Wannan ba shi ne karon farko da ake sanya wa namun dajin guba ba, domin mutanen da ke zaune a kauyuka da makiyaya sukan sanya musu nama mai guba.

Kuma yawanci sukan yi hakan ne domin ramuwa kan dabbobinsu da zakunan na dajin Mara ke cinyewa, inda kusan duk dare dabbobin mutanen sukan bi ta gandun dajin.

''Wata jami'a ta asusun kula da namun dajin Paula Kahumbu ta ce, ''wasu zakunan biyar suna cikin mawuyacin hali sakamakon cin gubar.

Sanya wa zakunan na dajin Mara guba abin kunya ne ga dukkanin 'yan Kenya, kuma babban laifi ne.''

Hakkin mallakar hoto Getty

A farkon shekaran nan wani mafarauci ya kashe wani sanannen zaki a kasar wanda ake kira Cecil, abin da ya jawo koke da suka daga sassan duniya ta shafukan sada zumunta da muhawara na intanet.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Famous lion found poisoned