Ka san shuka mafi guba a duniya?

Hakkin mallakar hoto z

Ana iya ayyana wasu shukokin wadanda ba wata wahalar samu su ke da ita ba, ko a ce ma suna nan a muhallin jama'a a matsayin wadanda suka fi hadari a duniya.

Ella Davies ta duba mana wadannan tsirrai na mutuwa kusa.

Hakkin mallakar hoto WILDLIFE GmbHAlamy
Image caption Monkshood ko Aconitum napellus

A shekara ta 2014 wani mai kula da lambu a wani rukunin gidaje a Biritaniya ya mutu a wani yanayi da aka kasa fahimta sakamakon gazawar kayan cikinsa da dama.

Har yanzu ba a san dalilin mutuwar tasa ba, amma binciken da aka yi ya samu wasu bayanai da sheda da ke nuna cewa kila wata sananniyar shuka ce (buttercups; ranunculus) mai fitar da furanni ta yi sanadin mutuwarsa.

Ita dai wannan shuka mai suna Aconitum da Ingilishi tana da furanni masu fadi da ke yin kama da irin hular nan ta malaman Yahudawa.

Amma kuma shukar tana da wasu sunayen kuma wadanda a ke kiranta da su saboda irin hadarin da ta ke da shi, kamar hular kwanon shedan da sarauniyar guba.

Wadannan sunaye da ake kiranta da su ba hadarinta kadai suke nuna wa ba, domin tana daga cikin shukoki mafiya hadari a duniya.

Saiwoyinta ne suka fi guba, ko da ya ke shi ma ganyenta zai iya yi wa mutum illa.

Dukkaninsu suna dauke ne da wata guba da ke iya shiga jikin mutum ta fata.

Alamun farko-farko na harbuwa da gubarta sun hada da jin kaikayi da kuma mutum ya ji ko an taba shi a wani wuri ba ya ji., idan a jiki a tsaya kenan.

Idan kuwa har an ci ta ne, to tana sa mutum amai da gudawa sosai.

Hakkin mallakar hoto Nigel CattlinAlamy

A shekara ta 2010 an samu wata mata Lakhvir Singh da laifin kashe farkanta bayan da ta sanya wa garin sanya dandano na miyarsa na kori (curry) wannan guba.

Bayan amai da gudawa, gubar tana kuma rage bugawar zuciya, abin da zai iya kashe mutum.

To amma fa ba dukkanin wadanda suka hadu da wannan guba ba ne suka gamu da ajalinsu.

Kamar yadda wani tsohon kwararre kan gubar lambu John Robertson ya bayyana, kyakkyawan tsarin halitta da mutum ya ke da shi na sanya shi amai na iya sa mutum ya tsallake hadarinta.

Mr Robertson ya ce, ''akwai mutanen da ya yi hira da su, wadanda suka taba cinta kuma suka rayu.''

''wasu ma'aurata ne da suka hada da ita a shuke-shuken lambunsu domin ta kawata lambun, inda matar a rashin sani da hada da furen shukar lokacin da ta ke tsinkar furanni da za su ci.

Dukkaninsu sun shiga wani mawuyacin hali har tsawon sa'o'i 24 amma dai a karshe sun tsallake rijiya da baya.''

Abin da masana suke gani ya sa shukar da wasu kamarta su ke da guba shi ne, gubar na matsayin wata kariya ce a wurinsu.

A wasu nau'ukan shukokin wannan kariya ta guba da su ke fitarwa domin yaki da kwari da sauran kwayoyin halitta masu cuta, za ta iya illa ga manyan halittu kamar dabbobi da mutum.

Hakkin mallakar hoto Anthony LeMoignanAlamy
Image caption Ana gargadin mutane da su nisanci wannan bishiyar (Giant hogweed) saboda gubarta

Za a iya zuzuta wannan lamari kamar yadda a ke dangantawa da yadda gubar shuka ko fure idan ta taba fatar mutum kuma ta hadu da hasken rana, sai ta kona fatar mutum.

Akwai katuwar bishiya (hogweed; Heracleum mantegazzianum) da ta yi kaurin suna wurin yin haka.

Amma akwai sauran shukoki da za a iya dauka marassa hadari kamar su karas da lemon tsami da wasu ma wadanda su ma a ke ci, wadanda dukkaninsu za su iya bata fatar jikin mutum a wani yanayi.

Daya daga cikin shukoki da suka yi suna wajen guba, ko da kuwa a wane yanayi ne, ta yi kaurin suna na zama bishiya mafi hadari a duniya.

Wannan bishiya wadda a ke kiranta da suna 'machineel' da Ingilishi (hippomane mancinella), tana fitowa ne a arewacin Latin Amurka har zuwa wani yanki na Florida da kuma Karebiya (caribbean).

A wasu wuraren da ta ke a kan yi mata jan fenti na nuna hadari domin gargadin mutane game da ita.

Ruwan da wannan bishiya ta ke fitarwa mai kamar madara yana dauke da guba mai sa kaikayi sosai.

Kuma ko da dan wucewa ka yi ka dan taba shi zai iya sale maka fata. Sanna idan ka zauna a karkashin bishiyar a lokacin ruwan sama, hakan zai iya yi maka illa matuka ya sa maka kaikayi ko ma kuraje a jiki.

Hatta kona wannan bishiya ma abu ne mai hadari, domin hayakin zai iya makanta mutum na dan lokaci da ya kuma sa mutum ya gamu da matsalar numfashi.

Hakkin mallakar hoto Stefano PaternaAlamy
Image caption Dan itacen bishiya mai tsananin guba (manchineel tree)

Duk da cewa bishiyar na da hadari kuma idan wani abu nata ya taba fadarka ta sa maka kaikayi ko kuraje, babban hadarin na tattare da cin 'ya'yanta.

Sunan da a ka fi kiran 'ya'yan masu ban sha'awa a ido, a harshen Supaniyanci na nufin karamar tuffar mutuwa.

Cin 'ya'yan nata hadari ne domin mutum za su iya jawo wa mutum amai da gudawa sosai, har ruwan jikinsa ya kare ya mutu.

Idan kuma ana maganar tsiran da ba za ka ci ba ne, akwai shuka daya da ta kere duk wani tsiro a illa, kuma za ta iya kasancewa a kusa da iyakar kasarka a yanzun nan.

Wannan tsiro (ricinus communis) kamar kaya ya ke, wanda kuma a ke yabonsa saboda kawata lambu da ya ke yi da fure mai ban sha'awa amma fa a ido, a lokacin bazara.

Tsiron yana da fure mai launin kore da da algashi (purple) da ganye mai siffar tafin hannu da kuma kwayoyi masu tsini kamar na kafso.

Ana samar da wani mai (castor ) da a ke amfani da shi wajen maganin kurji a cikin sauri, daga kwayoyin wannan tsiro.

Amma ga duk wani mai karatu da ke da fargaba da tsoro zai iya gano wata kalma mai ban tsaro a sunan wannan shuka na harshen Latin, wanna kalma kuwa ita ce , ''ricin''.

Wannan shi ne abin da ya sa shukar da a ke samun wannan mai na maganin maruru ko kurji ta yi kaurin suna na kasancewa wadda ta fi guma mai illa a duk duniya.

Hakkin mallakar hoto Chris BottAlamy
Image caption Gargadin mutane a kan hadarin gubar wannan bishiya (Manchineel)

Bayan tatse wannan mai mai amfani daga jikinta, saurin abin da ya rage na dauke da wannan guba da a ke samun ''ricin''.

Ita wannan guba ''ricin mai kisa tana hallaka mutum ne idan burbushinta ya shiga cikin jikin mutum.

Wanda ya gamu da ita zai iya yin fama da matsaloli na amai da gudawa da suma har tsawon mako daya kafin ya mutu.

An yi maganganu a game da wannan muguwar guba a littafin labarin kirkira na Agatha Christie mai suna ''The House of Lurking Death'' , zuwa fina-finai irin su ''Breaking Bad''.

To ganin irin hadarin da wannan shuka ke da shi ta yaya mu ke har mu shuka ta a lambunmu?

''Akwai bambanci tsakanin abin da ya ke guba da mai hadari ko cutarwa. Za ka iya cewa wacce shuka ce mafi guba, idan ka duba irin nau'in gubar da ke cikinta da kuma abin da gubar za ta iya yi,'' in ji John Robertson.

''Amma kuma ko ita wannan shuka tana cutarwa, magana ce ta ko za ka iya cinta a bisa kuskure ko hadari, da saukin yadda za ka iya shiga hadarin cinta da sauransu.''

Hakkin mallakar hoto INSADCO PhotographyAlamy
Image caption Ana gargadin mutane kada su ci wadannan kwayoyin wake masu guba

Jikin kwanson wani nau'in wake (castor) yana da kwari sosai, wanda ko da an hadiye shi zai iya ratsa cikin mutum ya fito ba tare da ya yi masa illa ba.

Kafin ya yi wa babban mutum illa har sai ya tauna kuma ya hadiye kwayar waken guda biyar, ko da ya ke guda daya ma zai iya yi wa yaro illa.

Amma ita kuwa kwayar ''ricin' idan aka gyara gubarta aka kuma yada wa mutum, kamar yadda aka hallaka wani tsohon jami'in gwamnatin Bulgaria da ita, bayan da ya bijire ya gudu a 1978.

Wata gubar mai kama da wannan (abrin) ana samunta amma kuma da gargadi a jikin abin da aka sanya ta ciki.

Kwayoyinta suna da daukar hankali saboda suna da kyau a ido, wadanda yawanci jajaye ne da dan bakin ido a jikinsu.

A kan yi amfani da su a inda a ke shukarsu, wajen yin abin adon wuya na mata da na hannu ko kuma a yi ado da su a jikin wasu kayayyakin.

An ma yi amfani da su a wurin baje kolin kayan kawa na Biritaniya a 2011.

Wannan guba ''abrin'' daya ta ke da ''ricin'' amma ana cewa ta ma fi ''ricin'' karfi idan ba a sarrafa ta ba.

Sai dai dadin abin shi ne kwayar waken da ta ke ciki yana da kwari sosai, wanda hakan ya sa ba ta iya ratsowa ta shiga cikin jikin mutum.

A wani lokaci sau daya da gubar ta taba samun wani mutum, matakan gaggawa da aka dauka na yi masa magani sun sa ya samu lafiya.

Hakkin mallakar hoto StocksnapperAlamy

Haka kuma wani abin jin dadin mutuwa a sanadin kamuwa da gubar shuka abu ne mai wuyar faruwa a wannan zamani na ci gaban kimiyya, saboda saurin ganowa da kuma magani.

Kuma yawancin gubar da a ke samu daga tsirrai sai an sarrafa su su ke zama masu hadarin gaske.

Saboda haka ba lalle ba ne tsirran su je har wurinka, amma sanin yadda lambunka ya ke ka iya kare rayuwarka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Earth's most poisonous plants