An samu biranya ungozoma

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

A wani abu mai ban mamaki da ba a saba gani ba, wata biranya ta yi aikin ungozoma, inda ta karbi haihuwar wata biranyar wadda ke haihuwa a karon farko a rayuwarta.

Matt Walker na da bayani

Haihuwar jariri ka iya zama wani abin mamaki na birgewa da kuma alfahari da godiya ta tabbatar cika ko kaiwa wani mataki da cimma wani buri a rayuwa.

Amma wata biranya da za a iya cewa ta daban ta wuce duk wannan, inda ta yi wa wata yarinyar uwa ungozoma, ta taimake ta wajen haihuwa.

Wannan wani sabon abu ne wanda ba a taba ganinsa ba dalla-dalla ko daukar hotonsa ko kuma bidiyonsa.

Abin mamaki ne domin, abu ne wanda ba a saba gani ba, saboda a ka'ida an san dabbobi sukan yi nakuda su haihu ne su kadai ba tare da wani taimako ba.

Matan dabbobi yadda aka sani su kanm haihu ne a wani kebabben wuri, su kadai galibi.

Taimakon da matar dan adam ta ke samu, na kasancewa a kusa da ita da kuma ba ta agaji idan hakan ta kama a lokacin haihuwa domin a tabbatar komai ya tafi daidai, dabbobi ba sa cin wannan gajiya.

To amma a wani yanayi na daban, masana kimiyya sun ga yadda wata biranya ta samu irin wannan kulawa daidai da yadda mutane suke yi wa matansu.

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

Sau daya kawai aka taba ganin wata biranya ta yi wa wata ungozoma kafin wannan na yanzu.

A shekara ta 2013 ne wasu masana kimiyya suka ga yadda wata biranya ta taimaka wa wata a lokacin haihuwa.

Amma kuma 'yan bayanai kadan aka wallafa game da yadda abin ya faru, sannan ba a adana wani cikakken bayani game da yadda biran suka yi ba a lokacin.

Sabanin wancan, a wannan masana kimiyyar sun iya tattara duk wani bayani daki-daki na yadda abin ya faru har bayan haihuwar.

Meng Yao, mataimakiyar farfesa a jami'ar Peking da ke Beijing tare da abokan aikinta, suna gudanar da bincike ne a kan wasu birai a wani daji a China.

Ko da ya ke sun zama kusan wata matsala a kasar, amma nau'in biran ba su da yawa, domin ba su wuce 800 ba a dazukan kasar, abin da ya sa suka zama cikin biran da ke cikin hadarin bata daga doron kasa.

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

Malamar jami'ar ta ce,''mun ga haihuwar wadannan birai sau da dama a kuma a cikin wannan garken a kowane lokaci kuma mukan ga yadda suke taimakawa, amma abin bai kai kamar yadda muak ga wannan ba.

Jariran mutane musamman ma a tsakanin dabbobi masu shayarwa, ba sa fuskantar uwa a lokacin da ake haihuwarsu.

Amma wannan da kuma musamman saboda girman jaririn, ya sa kusan da a ce ba ta yadda uwa za ta iya dukawa ta taimakwa kanta ta hanyar jawao jaririn waje.

A tsakanin wasu halittun da suka hada da birai, ana haihuwar jariri ne yana fuskantar uwa wadda galibi za ta iya taimaka wa kanta ta hanyar jawo jaririn waje.

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

''A ko da yaushe uwa da kanta take taimaka wa kanta ta janyo dan a yayin fitowarsa, sai bayan ta haihun ne sauran biran za su iya karbar dan sa'o'i bayan haihuwar.'' In ji farfesar.

Sai dai a wannan lokacin sai abin ya zama daban da yadda aka saba gani.

A mujallar ''Primates'' Farfesa Yao da abokan aikinta sun bayyana abin da ya faru a tsaunukan Nongguan da ke Guangxi a China.

Suka ce a tsakanin tarin biran maza da mata, akwai wata mai shekara biyar wadda ta shiga nakuda a karon farko.

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

A lokacin da take kokarin haihuwa, sai wata tamatar da zo tana taimakonta. Ita wadda ta kawo mata agajin shekararta 14 kuma ta haihu har sai biyar a baya, hadi da haihuwar da ta yi a wannan rana kafin wannan lokacin.

Ganin wata biranya tana taimaka wa wata yayin haihuwa, tana mata aikin ungozoma wani abin mamaki ne sosai a wurin masana kimiyyar da suka zuba ido suna kallon wannan abu.

''Ko alama wannan ba abu ne da za ka taba tsammani ba,'' in ji Farfesa Yao. ''Daya tamatar ta je ne kai tsaye wajen mai haihuwar ta kama aikin fito da jaririn.

Nan da nan ita ma uwar ta yadda ba ta nuna wata tirjiya ko kin yarda ba.''

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

''Aikin ungozoma ba abu ne da aka taba ji ba a tsakanin halittun da ba mutane ba.'' Malamar ta kara da cewa.

Masu binciken sun yi nazari tare da tattara bayani gaba daya kan yadda aka yi haihuwar.

Da bayani dalla-dalla na yadda uwar ta yi da kuma ita ungozomar tsawon lokacin haihuwar da kuma yadda suka yi bayan haihuwar.

Da farko ita ungozomar ta tsaya ne tana kallon sabuwar mai haihuwar tana ta fama, har ta yi yunkuri sama da 70.

Bayan da ta ga kan jaririn da kafadarsa sun fara fitowa sai ta je kusa.

Hakkin mallakar hoto Tieliu Gu

Sai ta tsaya da kafafunta ta kama jaririn da hannuwanta tana jawo shi, kuma cikin dakika 18 ta yi nasarar fito da shi.

Tana fito da shi sai (ita wadda ta yi taimakon) ta kama lashe shi.

Daga karshe sai ita mai haihuwar ta karbi abinta, ungozomar ta kuma ba ta ba tare da wani musu ko tirjiya ba, sannan ta dan zauna na dan lokacin tare da uwar da jaririn kafin ta tafi.

Masana kimiyya za su iya hasashe ne kawai akan wannan dabi'a, amma ba su da masaniya a kanta.

''Aikin ungozoma al'ada ce da kusan dukkanin mutane suke yi. Amma ana ganin dabi'a ce da dan adam kadai ke yinta,'' in ji Farfesa Yao.

Ta ce za ta iya kasancewa wani jinsin na halitta ya fi yinta fiye da wani ba kamar yadda aka yi tsammani ba.

Amma ana ganin za ta iya kasancewa ne kawai a tsakanin halittun da matansu ba su da wani bambancin matsayi ko kuma ba sa hamayya da juna.

Misali a tsakanin wasu nau'ukan biran kamar goggon biri, su sai dai ma a ce za su saci jariran junansu maimakon wata tamata ta taimaki wata ta haihu.

Haihuwar biran a daji kadan aka tattara bayanai akai, kuma ba wadda aka taba g anin an yi ungozoma, in ba wannan ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. The monkey that became a midwife