Gaskiya ne shukarka na jin wakarka?

Hakkin mallakar hoto Radius Alamy
Image caption ''Me kike nufi ba wannan wakar kike so ba?''

Za a iya daukar yi wa shuka magana kamar wani sakarci, kuma maganar cewa tana amsa kira wani abin dariya ne shi kuma. To amma za ka sha mamaki idan ka yi bincike.

Mun san cewa bishiyoyi ko shuke-shuke suna bin haske da inda ya fi karkata kasa (maganadisun da ke jan abubuwa kasa) da kuma inda aka taba su. To amma akwai wani amfani na yi musu waka?

Tambayar da BBC ta mika ga wasu daga cikin masu bibbiyar shafinta na Facebook na halittu ke nan.

Wasu daga cikin wadanda suka bayyana ra'ayinsu kusan sun nuna cewa lalle kam yi wa shukoki waka na da amfani da kuma tasiri.

''Ina da wata shuka (yucca), mai ganye kamar na kaba, wadda nake wanke ganyen nata sau daya a mako, kuma ina mata waka a lokacin da nake mata wankan,'' in ji Heather Louise Goodall.

''A cikin 'yan shekaru sai ta kara girma daga kusan kafa biyu zuwa kafa bakwai. A karshe ma dai sai ta kai ta yi girman da ta fi karfin gidan.

David Micheal Goeke ya ce, ''baban babban abokina shi ne mutumin da na san ya fi kowa shuka furanni.

Ya tabbatar min da cewa shakka babu abu ne mai kyau da muhimmanci ka rika yi musu waka. Amma kuma bai yi min bayanin dalilin hakan ba.''

Da yawa daga cikinku kun san muhimmanci da amfanin yi wa shuka waka.

Hakkin mallakar hoto david cook blue shift studio alamy

Chelsea Garcia Ortega ta ce, ''waka ko ma magana na sa mutum ya rika fitar da iskar nan mai dumi (carbon dioxide) daga hanci da bakinsa,''

kamar yadda wani masani David Souther ya bayyana. '' Bishiyoyi na sauya wannan iska mai dumi zuwa mai sanyi wadda mutane ke shaka (oxygen) ko da hakan ba shi da amfani ga ita bishiya ko shuka, kai za ka iya amfana daga iskar mai sanyi wadda ita kake shaka.''

Marshal Huang ya ce, to ai abin ya ma fi maganar kara yawan wannan iska mai dumi.

Christie Ley, ita cewa ta yi ai dirin sautin zai iya motsa shukokin da kyau. Ta ce, ''a shekarun 1970 dan wata kawata ya gwada abin a zahiri a kan wasu shukoki, inda ya rika sanya wa shukokin wakoki na da (masu kida a hankali maras rugugi) da kuma na zamani (masu rugugin kida da karfi),''

Kamar yadda ta yi bayani. Ta ce, ''wadanda yaron yake sanya wa kidan maras karfi, na natsuwa sai suka girma, su kuwa wadanda yake sanya wa daya kidan mai rugugi sai suka mutu''

Caroline Wall tana da wani bayani na wani nazari mai sauki. Babu bukatar a danganta lamarin ga wani sauti sam-sam.

Maimakon haka zai dai fi kyau a ce mutanen da ke yi wa furanni ko shukoki ko bishiyoyinsu waka, suna kaunarsu matuka, saboda haka zai kasance suna kula da su yadda ya dace.

Ta ce, '' za ka fi tunawa ka ba shukarka ruwa da kula da ita, idan ta kwanta maka a rai, har ma ka ga wata matsala da wuri wadda ba lalle ka ganta ba idan da ba ka damu da shukar ba sosai.''

Duk da yadda wannan lamari ke da wuyar fahimta, akalla mun kama hanyar fahimtar kimiyyar da ke tattare da shi. Me hakan yake nuna mana?

Hakkin mallakar hoto DPA Picture Alliance ArchiveAlamy Stock Photo
Image caption Har yanzu ba a san yadda tsirrai suke yi da waka ba

''Wannan kusan wani batu ne mai wuyar fahimta ga yawancin mutanen in ba 'yan kalilan ba da ke da ilimi da sha'awa a kai,'' in ji Wolfgang Stuppy, jagoran masu bincike a kan halittar iri (na shuka) a lambun Kew (kew Gardens) da ke Landan.

Ya ce, '' dan binciken kimiyya kalilan aka yi a kan lamarin, kuma shakka babu, ba wata shedar kimiyya ta tabbatar da cewa shukoki za su iya amfana daga wata waka ta wani.''

Amma kuma Stuppy bai kawar da yuwuwar hakan ba, inda ya ce, ''wannan ba yana nufin ba abu ne da ba zai taba yuwuwa ba.''

Shi ma Charles Darwin bai kawar da tsammanin samun hakan ba domin ya taba nuna cewa motsin teburin da ake dora tukunyar shuka na tasiri a kan shukar. Ma'ana shukar na bin wannan motsi.

Yadda abin ya ba shi mamaki, sai ya bayar da shawarar jarraba abin da ya kira, ''gwajin wawa'', domin a ga ko sauti na tasiri a kan shukoki.

''Hankalina ba zai taba kwantawa ba sai na jarraba,'' abin da ya gaya wa dansa Francis kenan.

Amma lokacin da dan Darwin din Francis ya rika yi wa shukoki sarewa (a matsayin gwaji) abin da ake son ganiun bai tabbata ba.

A baya-bayan nan wata sheda ta nuna cewa wasu sautuka za su iya kawo sauyi a wasu shukokin a wani mataki na rayuwar tsirran.

Hakkin mallakar hoto Tetra Alamy
Image caption Ba lalle ba ne wannan bishiyar tana jin wani abu daga wannan runguma

Sautin da ke da kara sosai, zai iya sa iri ya tsira. Gwajin da aka yi a kan wasu furanni (chrysanthemums) ya nuna alamun cewa sautin da ake iya ji sosai zai iya bunkasa girman kwayoyin halitta da ke sa furannin girma.

Kari a kan wannan kuma shi ne an gano cewa saiwar tsiron masara tana karkata inda wani sauti da ya kai wani yawa (frequency) yake fitowa.

Masu bincike a Koriya su ma sun gano cewa idan sauti ya kai wani mataki ya kan bunkasa wasu kwayoyin halitta.

Wasu gwaje-gwaje na dabara da aka yi da 'yan kananan shukokin barkono sun nuna tsirran suna sanin akwai wata shuka a kusa da su har ma da kamanni ko irinta, ta wata hanya daban wadda ba a saba amfani da ita ba, da kuma wani abu da ba a gane ba. Motsi zai iya taka rawa a nan.

Hakkin mallakar hoto mito alamy
Image caption Idan ka yi wa shukarka magana, tana jinka?

''Wasu shukokin ma su kan fitar da wani mai domin korar kwari, idan aka sanya musu karan wani kwaro yana cin ganye,'' in ji Matthew Portelli. Za a dauka kamar wani hauka ne wannan amma kuma mai binciken ya yi gaskiya.

A shekara ta 2014 masana kimiyya sun bayar da rahoto cewa jin sautin taunar tsutsa (tana cin ganye) kawai, ya isa ya sanya wasu furanni (thale cress plants) fitar da wani sinadari ko gubar kariya daga tsutsar.

Saboda haka maganar cewa shuka za ta iya jin waka har ma ta yi wani abu a dalilin jinta, ba shirme ba ne kamar yadda za a iya daukar maganar.

To amma kuma maganar cewa ko jin sautin waka na taimaka wa shukar girma wannan wata magana ce kuma ta daban gaba daya.

Denise Howess (mai rubutu a shafin intanet) ta ce, ''duk shukar da na yi wa waka za ta kanannade ta mutu.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can your plants really hear you if you sing to them?