Biran da ke aikin ungozoma

Hakkin mallakar hoto Bin Yang

Wannan shi ne karon farko da aka ga tamatar irin wannan birin mai hanci a É—age, tana taimaka wa wata a lokacin da take haihuwa da rana.

Ga nazarin Melissa Hogenboom

Ba kasafai ake ganin birai na haihuwa da rana ba. Duhun dare yana taimaka musu wajen kare su daga duk wata babbar dabba da za ta iya kawo musu hari. Saboda haka abu ne da ba a saba gani ba haihuwar biranya a dawa.

A da an dauka cewa yawanci suna haihuwa ne su kadai, ba tare da wani ko wata ba a wuri. To amma yanzu a karon farko masu bincike sun ga tamatar wannan nau'i na biri ta haihu da rana.

Ba wannan ba kadai. Biranya har ungozoma ta samu, wata biranyar da ke wurin wadda kuma ta taimaka mata a lokacin da take nakuda har ta haihu.

Hakkin mallakar hoto Bin Yang
Image caption Sau biyu ungozomar na kokarin jawo jaririn

Lokacin da mai cikin ta fara nuna alamun nakuda, sai mai taimaka matan ta yi sauri ta zo ta fara shirya ta. Bayan nan sai bayanta ya fara budewa, ita kuma ungozomar ta tsaya a kusa.

Da kan jaririn ya fara fitowa sai ungozomar ta yi kokarin jawo shi har sau biyu. Lokacin da kan nasa ya gama fitowa sai uwar ta duka ta rika jawo shi, ita ma ungozomar na taimaka mata har jaririn ya gama fitowa.

Bayan ungozomar ta taimaka wa uwar ta kintsa ta, har uwar ta ba ta jaririn ta rike, tana lashe shi, bayan uwar ta shayar da shi kuma ita ma ta lashe shi.

Hakkin mallakar hoto Bin Yang
Image caption Mai jego jim kadan bayan ta haihu

Ungozomar da wata biranyar da ita ma take wurin sun samu damar rike jaririn, bayan mintina 77 da haihuwar. Wata budurwa da ke kusa da su ita ma ta so uwar ta ba ta jaririn ta dauka amma uwar ta ki.

Uwar tana gama haihuwa,sai ta tsinke mabiyar ta cinyeta, wanda wannan kamar wani abinci ne mai gina jiki.

Hakkin mallakar hoto Bin Yang
Image caption A sa'ar farko da haihuwarta ba wanda ta yarda ya dauki jaririn

Ita kanta haihuwar ta yi ta ne cikin minti hudu da dakika goma. Masu binciken ba su yi tsammanin za su ga wannan haihuwa ba, domin ba a saba ganin birai na haihuwa da rana ba.

Lamarin ya faru ne a yankin Qinling mai tsaunuka na China, kasar da nan ne kadai ake samun nau'in biran wadanda ke fuskantar barazanar karewa a duniya. Bao-Guo Li na jami'ar Northwest a Xi'an da ke China, wanda yana daga cikin masanan da suka wallafa bayanin, ya ce taimaka wa tamatar da ke haihuwa a lokacin nakuda yawanci an dauka dabi'a ce ta dan adam kawai, ba abu ne da aka saba gani tsakanin biran da ke dawa ba.

Hakkin mallakar hoto Bin Yang
Image caption Mai haihuwa da ungozomarta

Ko da yake mun san irin wannan ta taba faruwa a tsakanin wasu nau'ukan biran daban a shekarun 2013 da kuma 2014, a dazukan China.

A saboda haka sai mu ce aikin ungozoma abu ne da za a iya cewa birai suma yinsa ba kamar yadda a da muka dauka wani abu ne da ba su saba yi ba. Sai dai kasancewar ita kanta haihuwar ba abu ne da aka saba gani ba, abu ne mai wuya a iya sanin yawan yadda suke ungozomancin.

Haka kuma ba mu san dalilin da ya sa wasu biran suke haihuwa da taimakon wasu ba, yayin da yawancinsu ke haihuwa su kadai.

Hakkin mallakar hoto Bin Yang
Image caption Kwana shida bayan haihuwa uwa da jaririnta na cikin koshin lafiya

''Samun taimakon ungozoma na da amfani sosai a lokacin haihuwa kama daga kokarin fito da jaririn da debe kewa da kuma kwantar wa da mai haihuwa hankali,'' in ji Li. Kamar yadda aka gani a wannan haihuwar yadda uwar ta samu taimako lokacin haihuwar da kuma bayanta.

Yanzu dai masanan na kokarin daukar hoton bidiyon wata haihuwar ta wata biranyar su ga ko aikin ungozomar abu ne da daman biran suke yi.

Li ya kara da cewa sanin wannan ilimi na taimakon mai haihuwa da wadannan birai ke yi zai iya taimaka mana kara fahimtar asalin aikin ungozoma a tsakanin mutane.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The monkeys that act as midwives