Za ka ci abin cin da ya faɗi ƙasa?

Hakkin mallakar hoto OJO Alamy

Abin da aka dauƙa shi ne duk abin cin da ya faɗi ƙasa ba abin da yake samunsa a cikin daƙiƙa biyar, kuma za ka iya cin kayanka domin ba wata cuta a jikinsa. Ko ina gaskiyar wannan magana?

Melissa Hogenboom ta bincika

Wata rana ina rike da alewa ina sha sai kawai ta kubuce ta fadi kasa, ban yi wata-wata ba sai na yi sauri na dauke ta, amma kuma sai zuciyata ta ke raya min, na san yawan kwayoyin cutar da alewar ta kwasa kuwa?

To amma ni ban ga alamar wani datti ko kasa a jikinta ba, saboda haka sai kawai na yi watsi da wannan tunani, na lunkuma alewata a baki kawai na ci gaba da sha.

Ni dai na san dandamalin dakin girkina fes yake domin ban dade da share shi ba, kuma alewar ba ta dade a kasa ba, ba ta kai dakika biyar ba.

Maganar ka'idar cewa idan wani abin ci ya fadi kasa in dai bai wuce dakika biyar ba ba ya dibar wata kwayar cuta abu ne da mutane da dama suka sani.

Saboda haka tun da wannan alewa da ta fadi ba ta kai dakika biyar din ba da faduwa, ina ganin ba ni da wata fargaba da na lakume abata.

To amma kuma ya kamata a ce na dauki alewar na shanye, ko kuma a rashin sani na zuba wa bakina kwayoyin cuta?

Hakkin mallakar hoto StocksolutionsAlamy Stock Photo

Mun mika wannan tambaya ga wasu masu bibiyar wannan shafi na Ingilshi, domin jin abin da za su yi idan su ne alewar ko wani abin cinsu ya fadi kasa.

Adam Harmsworth ya ce wannan ka'ida haka take, duk kananan kwayoyin halitta na bakteriya da masu cutarwa sun san muhimmancin lokaci.

Gary Burch ya ce shi kam maimakon dakika biyar yana amfani da dakika uku ne, kuma hakan ma a bisa wani dalili ne na daban. Ya ce, ''wannan dan lokacin shi ne abin da na yi kiyasi kare zai iya cinye min abincin da ya fadi kafin na farga.''

Babu wasu kwayoyin cuta na bakteriya da ke kasa, suke jiran wani abinci ya fadi su makale masa.

Manuel Rodriguez, ya ce shi kam ba wani dalibi ba ne na kimiyya saboda haka yake bin maganar dakika biyar din nan. Sai dai wasu mutanen sun fi tsanani a lamarin.

Corinne Howard ya ce, ''in dai abu bai kai bakina ba, to sai dai ya kare a kwandon shara.''

''Muna maganar dan kankanin lokacin da kwayar bakteriya za ta hau abincin da ya fadi ba dadewa,'' in ji Jon Bedet. Ya ce, ''Da dai abin da zai fi shi ne a ce lokacin faduwar bai kai ko dakika sifili ba.''

Lane Jasper cewa ta yi, ''ya dogara ga irin abincin da ya fadi kasa da kuma yadda kake jin yunwa.''

To domin kawo karshen muhawarar na mika tambayar ga masana kimiyya wadanda suka kware a kan mitsi-mitsin kwayoyin halittu.

Idan su ne wani abin cinsu ya fadi kasa za su ci musamman ma a ce wani abu ne mai danko?

Hakkin mallakar hoto Steve GschmeissnerSPL
Image caption Hatta dakin da ake tsaftacewa ko da yaushe yana da kwayoyin halittu na bakteriya

To da farko dai mu sani cewa ba wasu kwayoyin halitta masu cutarwa ko marassa cutarwa da suke zube a kasa, suke dakon wani abinci ya fadi su hau jikinsa.

Maimakon hakasu wadannan kwayoyin halitta suna nan a ko'ina ko da kuwa yanzu ka wanke daben dakinka.

Adam Taylor ya ce, ''maganar gaskiya a kimiyyance babu wata ka'ida ta maganar dakika biya (kafin kwayoyin cuta su hau abincin da ya fadi), indai abin ci ya fadi kasa to kwayoyin cuta za su kama shi.''

Jack Gilbert na jami'ar Chicago a Illinois a Amurka, ya ce, ''ai dazarar wani abin ci ya fadi kasa to zai kamu da datti, kuma kwayoyin cuta da ke cikin dattin za su kama shi.''

A ko da yaushe akwai'yan kananan halittu da ido ba ya iya gani kusan 9,000 boye a cikin kura a gidajenmu, wadanda sun hada da kwayoyin halittu na bakteriya daban-daban kusan 7,000, wadanda yawancinsu ba masu cutarwa ba ne, kamar yadda wani nazari na 2015 ya nuna.

Wadannan halittu suna nan a ko'ina kuma a ko da yaushe; a hannunka ne da fuska, da kuma gidanka. Muna fitar da kwayoyin bakteriya a ko da yaushe ta jikin fatarmu ne da kuma ta numfashinmu.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Kwayoyin halittu na bakteriya suna nan a ko'ina hatta a jikin fatarmu

Gilbert ya ce, ''ba za ka iya boye kanka daga kwayoyin halittun nan ba. Wannan ita ce gaskiyar lamari. A takaice kana rayuwa ne da ma shaka da fitar da dimbin kwayoyin halittun bakteriya.''

Masu bincike ma sun bayyana cewa ko wane mutum yana fitar da kwayoyin halitta na bakteriya kusan miliyan 38 daga jikinsa a duk sa'a daya, kamar yadda bincike ya nuna.

Amma kuma duk da wannan, in ji Gilbert, sama da shekara 100 ana gaya mana cewa wadannan kwayoyin halitta hadari ne kuma ya kamata mu rika kashe su duka.''

''Muna dari-dari ko ma gudun datti amma kuma ba mu san ainahin yadda za mu iya kamuwa da kwayoyin cuta daga dattin da muke gudu ba, '' in ji Gilbert.

Ba shakka shi kam Gilbert zai ci abin cin da ya fadi kasa, indai har wurin da ya fadi yana da tsafta. Ya ce, ''amma fa idan a ramin shara ya fadi, to ba zan dauke shi ba.''

Ya ma kara da cewa. Yawancin lokaci, hatta lasar daben dakinka ko bakin salgarka ba lalle ba ne ya sa maka cuta.

Hakkin mallakar hoto Big Cheese Photo LLCAlamy Stock Photo
Image caption Kare na shan ruwan salga

Sai dai ya ce bai kamata ba ka yi wannan kasada idan akwai wani maras lafiya a gidanka ko kuma ba a tsafta sosai a kasar da kake.

Ba shakka akwai kwayoyin halittu masu yada cuta idan akwai wadda ke labe a daben daki ko gidanka, za ta iya kasancewa a wani sakon na gidan naka, kila a dakin dafa abincinka ko kuma a hannun kofarka. Za ka iya kamuwa da rashin lafiya ko da ka ci abincin da ya fadi kasa ko ba ka ci ba.

Maganar ita ce, idan dai har ka yi rashin sa'a akwai wata kwayar halitta ta bakteriya da ake kira Salmonella a daben gidanka, in dai kaci abin cin da ya fadi kasa ya kamu da ita ko ya kai tsawon dakika biyar ko bai kai ba, to za ka kamu da cuta.

Sai dai wani bincike da aka yi a 2006 ya nuna cewa da wuya wannan kwayar halitta Salmonella ta kama abin ci a cikin dakika biyar sai dai ko minti daya, amma dai ko ma yaya ne wannan hadari na nan.

Hakkin mallakar hoto usdasciencephotolibrary
Image caption Kawayar halittar bakteriya ta Salmonella

Masana kimiyya kamar Katherine Amato ta jami'ar Northwest ta Illinois a Amurka ta ce ai haduwa da wadannan kwayoyin halittu abu ne mai kyau, saboda gaba dayan rayuwarmu mun taso ne da su, kuma sun taka muhimmiyar rawa a kasancewarmu mutane.

Masaniyar ta ce ai kasancewar kwayoyin halittu a kan abincinmu na taimakawa wajen gina garkuwar jikinmu, idan muka duba yadda mutum lokacin da yake yaro yake ta'ammali da abubuwa masu datti ciki har da abinci.

''Kawai ka ci abinka.'' In ji Amato. Ita ma Natalie Henning ta yarda da hakan inda ta kara da cewa, '' ai ba ta yadda za ka gina garkuwar jiki idan kana kyamar kwayoyin cuta ba.''

A takaice maganar kin cin abin cin da ya fadi kasa sama da dakika biyar ko cin wanda bai kai dakika biayr din ba a kasa shirme ne kawai.

Idan dai har akwai wata kwayar halitta mai yada cuta, kiyayewa da wannan ka'ida ba za ta hana ka kamuwa da rashin lafiya ba. Kuma a wani lokacin ma cin abincin da ya fadi kasa abu ne mai kyau.

Ban dai tabbatar ba amma ina son in jarraba lasar bakin salga (masan Bature ta tangaran).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What really happens to food when you drop it on the floor?