Ka san wuta ba ta hallaka beguwa?

Hakkin mallakar hoto Fritz Geiser

Gobarar daji babbar barazana ce da ke addabar ƙasar Australiya a ko da yaushe, amma beguwa ta gano wata hanya ta ban mamaki ta tsira daga wannan bala'i na wuta.

Richard Gray ya yi bincike

Wutar daji na iya ratsa tsakar dajin Australiya da gudu na ban mamaki da ta da hankali, tana lakume kusan komai da ta yi karo da shi, ba ta barin komai sai bakin rayi a hamada.

Yawancin dabbobi suna jin tsoron wuta tun asali, abin da ya sa suke gudunta a duk lokacin da ta tunkare su. To sai dai wata halitta tana da wata dabara ta ban mamaki ta fuskantar wuta. Ba wani abu take yi ba.

Abin da ita wannan halitta, beguwa wadda ke yin kwai maimakon haihuwar 'ya'yanta, za ta iya shiga wani yanayi kamar na doguwar suma, yanayin da dabbobi da dama suke shiga wanda ke taimaka musu adana karfin jikinsu.

A lokacin da beguwa ta shiga wannan yanayi, tana rage yawan aikin da jikinta ke yi kuma ta rage yanayin zafin jikinta.

Kamar yadda wani bincike da aka wallafa a watan Afrilu na 2016 ya bayyana, wannan yanayi yake sa ta jure wutar daji. Ana ganin wannan halayya ita ta ba wa asalin wannan halitta ta zamanin da damar jure wa duk wata barzana ta ganin bayanta daga doron kasa.

Hakkin mallakar hoto Julia Nowack
Image caption Gobarar daji a gandun Dryandra Woodlands na Australiya

A cikin shekarar 2013 ne wata gagarumar wutar daji ta ratsa gandun dajin Warrumbungle National Park a gabashin Australiya. Julia Nowack, wadda a da take jami'ar New England a New South Wales ta Australiya ta yi nazarin bannar da wutar ta yi bayan da ta gama ci.

Ita da abokan aikinta sun lura cewa wannan halitta, beguwa na daga 'yan halittun da suka tsira. Hatta a wuraren da ba komai da ya rage sai toka masu binciken sun ga wannan halitta na ta yawo, ba abin da ya same ta.

Beguwa yawanci dai tana gidanta ne a karkashin kasa ko cikin guma-guman bishiya da suka fado, wanda hakan ke kare ta daga wannan zafin wuta.

To gobara dai galibi tana da tasiri ko illa ta tsawon lokaci, Kuma beguwa yawanci tana cin kwari ne ta rayu, kuma a lokacin gobara ko wuta kwari suna guduwa ne ko kuma duk wanda ya tsaya wutar za ta halaka shi.

Wannan ne ya sa Nowack da abokin bincikenta Fritz Geiser, ya sa suke ganin ko ita wannan halitta tana amfani da yanayin nan na doguwar suma su tsira daga illar wutar daji da take kone duk wani kwaro da za ta iya ci ta rayu.

Nowack ta ce, ''yawon farauta lokacin wutar daji zai iya jefa rayuwar dabbobi cikin hadarin konewa ko kuma itatuwa su fado musu, saboda haka shigarsu wannan yanayi na dogon suma zai iya kasancewa wata hanya ta tsira.''

Hakkin mallakar hoto Ingo OelandAlamy Stock Photo
Image caption Gandun dajin Warrumbungle

Domin gano yadda lamarin yake, masu binciken sun yi amfani da wata dama ta shirin kona wani yankin daji a kudu maso gabashin Perth a yammacin Australiya, inda suka ware wasu beguwa guda goma, a ciki da kuma kewayen inda dajin da za a kona.

Ta hanyar wasu abubuwa da suka makala wa kowacce daga cikin beguwar goma, Nowack da abokan aikinta sun samu damar gudanar da nazari a kan beguwar goma tsawon kwanaki 21 zuwa 25 kafin wutar da kuma kwanaki 31 bayan wutar.

Biyar daga cikin beguwar suna cikin da aka tayar da wutar sauran biyar din kuma ba sa cikin inda aka tayar da wutar. A cikin kwanakin kafin tayar da wutar, beguwar sun rika shiga wannan yanayi na doguwar suma ta dan lokaci kusan a kullum.

A daren da za a tayar da wutar, wadanda suke yankin sai suka shiga yanayi na doguwar suma, abin da ya sa yanayin zafin jikinsu ya ragu da maki 20 na ma'aunin celcius a cikin kwanaki 31 kasa sosai da yadda suke kafin gobarar. Wannan ya ci gaba da kasancewa akalla har makonni uku bayan wutar.

Su ma wadanda ba sa yankin da aka tayar da wutar sun cigaba da yyanayin sumar da suke shiga kafin wutar har bayanta.

Hakkin mallakar hoto Julia Nowack
Image caption Bayan gobarar daji

Nowack ta ce, ''bayan gobarar yanayin zafin jikin beguwar da ke wurin da aka kone yawancinsu kasa yake da na wadanda suke a yankin da ke waje da inda aka tayar da gobarar.''

Yin kasa da yanayin zafin jikin nasu ta wannan hanya zai iya taimaka musu jure yanayin zafi, kasancewar yankin zai ci gaba da dan cin wuta bayan wutar.

''Wutar tana haifar da hayaki mai yawa, kuma saboda babu abubuwa masu yawa a kasa da za su kare wutar, sai ta shafi yawanci dajin da guma-gumai da bishiyoyi, abin da ke sa bishiyoyi su fadi, kuma guma-gumai su yi ta cin wuta tsawon makonni bayan wutar,'' in ji Nowack. Ta ce ''bishiyoyi sun ci gaba da cin wuta har zuwa karshen kwana 31 bayan wutar.

Amma ana ganin beguwar na yin haka ne ta yadda za ta iya jure tsawon kwana da kwanaki bayan wutar har zuwa lokacin da abincinsu, wato kwari za su fara bayyana, inda suke tattalin kuzarinsu.

Shiga wannan yanayi kenan wata dabara ce, ta yadda za su dade a boye cikin tsaro ba tare da sun galabaita ba.

Hakkin mallakar hoto Fritz Geiser
Image caption 'Yar karamar beguwa

Wannan wata dabara ce da kananan dabbobi masu shayar da nono (mammals), kamar jemage da kurege da bera (kanana) da wasu tsuntsaye, suk yi ta tsawon sa'o'i zuwa makonni.

Sai dai yawancin wannan doguwar suma ga alama na faruwa ne domin taimaka wa dabbobin su jure wa rayuwa a lokacin tsananin sanyi. Saboda a lokacin tsananin sanyi, abinci na karanci, kuma hakan yana sa jiki ya yi amfani da makamashin jiki (karfi) mai yawa domin dorewar dimin jiki.

Nowack da Geiser na ganin wannan dabara ta doguwar suma kila ita ke taka rawa wajen taimaka wa dabbobi su tsira a lokacin gobara ko wani bala'i.

Duk da cewa wannan dabara ta doguwar suma a yayin gobarar daji tana iya ba wa beguwa kariya, to ba a ko da yaushe take amfani ba.

A lokacin bincikensu ayarin Nowack sun gano beguwa uku da wutar ta kone. Daya daga cikinsu na daga wadanda suka makala wa na'ura suke bin diddiginsu, wadda bisa ga alamu ta yi wannan doguwar sumar ne a cikin wani kwaure da wuta ta kama

Hakkin mallakar hoto Shane PedersenAlamy Stock Photo

Wani bincike na baya ya nuna cewa beguwa tana iya farfadowa daga duguwar suma ta gudu idan ta ji hayakin wuta ya dame ta. Hasali ma wata beguwa da ke cikin wannan yanayi a cikin wannan gungume tare da waccan da ta kone, ta farfado ta gudu, amma 'yar uwarta ba ta yi sa'a ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. When confronted with a raging wildfire, echidnas go to sleep