Ko ka san amfanin kwayoyin cutar jima'i?

Hakkin mallakar hoto MedicImageAlamy

Wasu Ĉ™wayoyin da ke shiga jiki a lokacin jima'i ka iya kasancewa masu amfani a garemu, hakan na nufin yawancinmu na asara kenan saboda rashin sani?

Ga nazarin Niki Wilson

A lokacin da na fara balaga, na fara daina wasa da maza a makaranta, mahaifiyata ta tatauna da ni a kan al'amarun da suka shafi jima'i, inda ta ba ni wasu shawarwari da kuma gargadi kan yadda zan kare kaina daga wata illa ko abin takaici a sanadiyyar jima'i.

Wannan ba shakka shawara ce mai kyau, domin hatta hukumar lafiya ta duniya ta ce, a fadin duniya sama da mutane miliyan daya a duk rana suna kamuwa da kwayoyin cuta na jima'i (STD).

Wasu daga cikin wadannan kwayoyin cuta ka iya hana haihuwa, wasu ma ka iya haddasa cutar da ta fi haka. Akwai dalilai da dama da za su sa mu hana wadannan miyagun baki kama wuri a jikinmu.

Miyagu daga cikin irin wadannan kwayoyin cuta na jima'i kila su suke sa ba ma mayar da hankali mu san cewa akwai wasu daga cikin kwayoyin da ke kai- komo a ruwan jima'in masu saduwa, na iya kasancewa masu amfani.

To ya kuma idan a ce a kokarin da muke na kare kanmu daga nau'in wadannan kwayoyi masu cuta da muka sani, muna asarar masu amfani da daga cikin kwayoyin?

Bincike da yawa da aka yi na nuna cewa ya kamata a sake nazari tare da yi wa lamarin kallon tsanaki.

Hakkin mallakar hoto Nano Art LtdSPL

Ba wani sabon labari ba ne cewa kananan kwayoyin halittu, kamar su bakteriya da bairus (bacteria, virus), suna da matukar amfani ga lafiyarmu. A cikin jikin kowannnenmu akwai kwayoyin masu cutarwa da kuma masu amfani. Idan aka samu bambanci kan yadda yawan kowanne ya kamat ya kasance a jikin mutum, to sai a samu matsala.

Misali, akwai kwayar (yeast, candida) da ake samu a farjin mace, wadda wata kwayar halittar ta bakteriya (lactobacillus) take yaki da ita. To idan ya kasance wani abu ya hana wannan kwayar bakteriya aikinta, sai ita waccan halittar ta farko ta mamaye farjin, abin da zai sa mace ta kamu da wata cuta da ke sa kaikayi a farji (yeast).

Muna da tarin kanan halittu a jikinmu

Jikinmu ya samo asali da rayuwa tare da kananan halittu (microbes). Wadannan 'yan mitsi-mitsin kwayoyin halittu (bacteria, fungi, virus) suna jikin fatarmu da hanjinmu da kuma farjinmu.

Duk da cewa ba abu ne da za ka so ka yi tunani ba, yadda wadannan 'yan halittu ke karakaina a cikin hanjinmu ba, amma kuma a kullum muna kara fahimtar cewa wadannan halittu suna taka muhimmiyar rawa a halittar shi kansa jikinmu.

Mataki na farko na fahimtar rawar da su wadannan 'yan halittu suke takawa shi ne a gane su. Duk da cewa ba mu san da yawa daga cikinsu ba zuwa yanzu, akwai misalai masu ban sha'awa da za su karfafa mana guiwa mu mayar da hankali a kansu, in ji Chad Smith masanin kimiyya a jami'ar Texas a Amurka.

Hakkin mallakar hoto Andy SanNPL

Mu dau misalin wani kwaro (pea aphids) da ke tsotse ruwan jikin kayan amfanin gona masu ba wa jikin mutum kayan gina jiki (legumes), kamar wake da gyada da makamantansu.

To yadda kwarin ke cin moriyar rayuwarsu na da alaka da kwayoyi (na cuta) masu amfani da ke shiga jikinsu a lokacin jima'i. Tasirin hakan kuma ya hada da bijire wa kwayoyin cutar da suke kashewa ko hana wanda yake dauke da su haihuwa da jure wa zafin rana sannan kuma da iya rayuwa a kan tsirran da ba wadanda suka saba cin amfaninsu ba, har sai sun samu abinci.

Wannan bai kare ba, domin akwai wasu nau'ukan sauro da suke yada wata kwayar bakteriya a tsakaninsu a lokacin jima'i, kuma wannan kwayar tana mamaye hanjinsu da kwalatansu da kuma jikin kwayayensu.

Ana ganin wannan lillibi na wanna kwaya ta halitta ta bakteriya tana ba dan tayin wannan kwai abinci, abin da ke sa dan tayin (ko tsutsar) ya yi saurin girma kwana biyu zuwa hudu fiye da kwayayen da ba su samu wannan sinadari ba.

A karshe kuma kwayoyin cutar jima'i masu amfani, an gano suna karawa halittar fungi juriyar zafin rana, tare da taimaka wa duk fungi din da take da kwayoyin saurin girma.

To amma kuma ya lamarin yake a mutane? Yanzu dai mun san cewa akwai wani misali da zai sa mu yarda cewa kwayoyin halitun (cutuka) da ke yaduwa a lokacin jima'i na iya amfanar wasunmu.

Wannan kwayar halitta ta bairus ce (GB virus C) kuma an fi saninta da hepatitis G virus (HGV). Kwaya (r cuta) halitta ce da ake yada ta a lokacin jima'i, wadda a karan kanta, babu alamar tana haddasa wata babbar cuta, ko da yake yawanci ana ganinta da wasu kwayoyin cuta na bairus kamar HIV.

Wannan kwayar cuta (GB virus C) za ta iya rage hadarin uwa ta yada wa jariri kwayar cutar kanjamau, wato HIV.

Wani nazari da aka yi na wasu bincike guda shida ya gano cewa kwayar bairus din (GB virus C) tana da alaka da rage kashi 50 cikin dari na rage mutuwar masu dauke da kwayar cutar kanjamau.

Masana kimiyya na ganin kwayar tana yin haka ne ta hanyar rage karfin kwayar HIV na raunana kwayoyin halittar (cells) garkuwar jikinmu. Ana ganin za kuma ta iya kara zaburar da sauran sassan garkuwar jikinmu su yaki kwayoyin cutar ta HIV sosai.

Haka kuma dai ita wanna kawaya mai amfani (GBV-C na iya yaduwa daga uwa zuwa jariri. Wanna kuma ba karamin alheri ba ne domin za ta iya rage hadarin uwa ta yada wa jaririnta kwayoyin cutar mai karya garkuwar jiki.

A baya bayan nan kuma ana ganin kamar ita kwayar GBV-C din tana rage hadarin mutuwar wadanda kwayar cutar Ebola ta kama, inda take rage tasirin kwayar cutar a jikin mutum.

Gano irin wannan amfani na ban mamaki na kwayoyin da ake yadawa a lokacin jima'i, zai sa mu yi mamakin irin asarar da muke yi, in ji Betsy Foxman ta jami'ar Michigan a Amurka.

Ta ce a da mun dauka cewa duk wata kwaya da ake yada wa a lokacin jima'i ta cuta ce kawai. Matakan da muke dauka na kariya daga garesu kila sun sa yanzu ba mu da wasu daga cikin irin masu amfanin a jikinmu.

Mai binciken ta ce, kila ma akwai wasu kwayoyin halittar (microbes) wadanda ke yakar wasu cutukan, mu ba mu sani ba. Idan kuwa haka ne, akwai su to ka ga hakan zai sa mu rage yawan dogaron da muke yi a kan magunguna (antibiotics).

Ta kara da cewa, ''ba shakka wajibi ne a wani lokaci a yi amfani da magunguna domin cetar rayuka, amma zai fi dacewa ka samu wani abin wanda ya fi dacewa, wanda kuma zai je kan kwayoyin cutar ne ya yake su kai tsaye ba tare da yin dan wani abu daban ba (illa).

Hakkin mallakar hoto HipersyntezaSPL

Ba mu da tabbas kan wace kwayar halitta ce da ake yadawa a lokacin jima'i take da amfani, amma dai Foxman tana ganin Lactobacillus, wato bakteriyar da ake samu a madarar yogot (yoghurt), wadda kuma daman akwai ta a jikin dan adam, tana daya daga cikinsu.Ta ce kila ma akwai wasu masu amfanin wadanda ba a kai ga gano su ba.

Akwai riba ko babu?

Wannan duka kamar wani labari ne mai dadin ji, ko? Zai iya kasancewa akwai wasu tarin kwayoyin da ake yadawa a lokacin jim'ai masu amfani ga lafiyarmu, wadanda ba musan su ba sosai.

To akwai dai wata matsala daya kacal. Matsalar ita ce idan har ta jima'i za mu samu wadannan kwayoyi, to hakan zai kai mu ga samun kishiyoyinsu wato masu yada cutuka kenan.

Kila a nan gaba za a iya samun wasu hanyoyin na daban da mutum zai iya samunsu a jikinsa. Da zarar an gano wata kwayar halitta mai amfani wadda ke yaduwa ta jima'i, masana kimiyya da ke aiki a asibitoci za su iya kokarin bulo da wasu hanyoyi marassa hadari da za su sanya wa mutane kwayoyin, ko kuma su lalubo hanyoyin da za su iya haifar da aikinsu ba tare da mutum ya jefa kansa cikin hadarin yin jima'i ba.

Hakkin mallakar hoto PremaphotosAlamy

Yawancin kwayoyin cutakan jima'i da suka hada da na ciwon sanyi ba sa kashe wanda suka shiga jikinsa. Galibi su ma suna neman wajen zama ne da za su rayu kawai, in ji Foxman.

Kananan kwayoyin halitta da ke yada cutukan jima'i na bukatar su san cewa za su iya yaduwa ne daga mutum zuwa mutum. Saboda haka wannan yaduwa za yta tabbata ne idan mutumin da yake dauke da kwayoyin yana da lafiya, in ji masaniyar kimiyyar.

Ta ce, ''idan mutum ba wanda za a iya cewa mai cikakkiyar lafiya ba ne to ba lalle a samu wannan yaduwa ba.''

Za ta iya kasancewa a zamanin da can, kafin zuwan kororon roba, wani lokaci ana daukar amfanin samun wadannan kwayoyi masu amfani ya fi hadarin yin jima'in ba tare da kariya ba, in ji Smith.

Masanin kimiyar halittu, Micheal Lombardo, ya ce shi yana ganin ma, mutanen da suke dauke da kwayoyin masu amfani, za su iya nuna cewa suna dauke da su ba tare da sun san suna nuna hakan ba, wanda hakan zai iya sa wasu su fi son yin jima'i da su.

Hakkin mallakar hoto z

Abin yana da sarkakiya da yawa. Amfanin wadannan kwayoyi ba lalle ya tsaya ga amfaninsu kamar kariya daga cutuka ba da juriyar zafin rana. Wadannan kwayoyi za ma su iya tasiri kan halayyar mutumin da ke dauke da su. Ta wata hanya mai kyau.

Sai dai wannan wani fanni ne na binciken kimiyya da kusan za a iya cewa sabo, wanda kuma zai iya bayyana wasu abubuwan masu amfani sosai. Misali wasu kwayoyin halittun bakteriya da suke rayuwa a cikin hanji ana ganin suna shafar kwakwalwar matashin bera, inda suke rage masa yanayin damuwa.

Wadannan 'yan kananan kwaypoyin halittu za kuma su iya sauya yanayin sinadarin da halittu (mutane da sauran dabbobi; kwari da tsuntsaye) ke da shi a jiki (kanshinsa ko wari), in ji Smith.

An gano hakan ne a wani bincike da aka yi a kan kuda (wanda ke cin 'ya'yan itatuwa) wanda ke samun kwayoyin bakteriya daga 'ya'yan itacen da yake ci daban-daban. Ka san sakamakon hakan?

To shi wannan nau'in kuda ya fi sun yin jima'i da tamatar da take da irin wadannan kwayoyin bakteriya da yake da su a cikinsa. Haka ita ma tamatar da take da kwayoyin ta fi son ta sadu da namijin da yake da kwayoyin.

Smith ya ce, ''wadanda suke da abokan jima'i fiye da daya, za su fi samun wadannan kwayoyi masu amfani.'' ya kara da cewa, to in kuwa haka lamarin yake, to wannan shi ne dalilin da ya sa halittu ke san saduwa da fiye da abokin jima'i daya.

Hakkin mallakar hoto SCIENCE PHOTO LIBRARY

Misali a tsakanin kadangaru, matan da suke saduwa da namiji fiye da daya, an gano cewa suna da wadanna kwayoyin halittu na bakteriya da sauransu da yawa fiye da wadda ba ta saduwa da namiji fiye da daya.

Masana kimiyyar da suka yi nazari a kansu, suna ganin wannan shi ne ke sa wadda ke saduwa da kadangare fiye da daya ta fi wadda ba ta yi lafiya.

Lombardo na ganin wasu matan tsuntsaye da suke jima'i akai akai da namiji daya, ko kuma da namiji fiye da daya, ka iya samun amfanin wadannan kwayoyi na bakteriya da sauransu ta hanyar samun kwayoyin bairus da ke hallaka bakteriya mai cutarwa, ko kuma ta hanyar samun kwayoyin bakteriyar da ba sa cutarwa sosai.

Haka kuma bakteriyar da ke samar da sinadarin da ke kashe bakteriya da sauran kwayoyin halittu makamantanta ka iya taimaka wa wajen yaki da cutuka. Wannan shi ne daya daga cikin bayanan da masu bincike ke gabatarwa a matsayin dalilin da ya sa tsuntsaye ke neman wasu bayan wadanda suka yi aure da su.

Foxman ta ce, ita tana ganin akwai ma wasu kwayoyin da ake yadawa ta jima'in wadanda za su sa mutum ya rika yin jima'i akai akai. ''Ya za ka ji idan a ce akwai wata kwayar halitta ta bakteriya da ke sa ka ji dadin yin jima'i?

Hakkin mallakar hoto pa

Foxman ta ce a tsakanin maza da mata duka akwai abubuwan da ke haddasa musu matsalar jima'i, amma kuma ba a san abin da ke jawo su ba. Saboda haka gano kwayoyin halitta na bakteriya ko bairus ko dai wata halitta masu amfani da ake samu ta jima'i zai iya magance wadannan matsaloli, wanda hakan zai inganta lafiyarsu ta jima'i. Saboda haka wannan abu ne da za a iya dubawa, in ji farfesar.

''Mu halittu ne da muke yin jima'i. Domin haka duk abubuwan da za su sa mutane jin dadin jima'insu da kyau, yana sa su jin dadi gaba daya.''

Yadda lamari yake shi ne ko kai kwaro ne ko kadangare ko kuma mutum, da wuya a ce kai kadai ne kawai da abokiyar jima'inka. Watakila akwai dubban mitsi-mitsin halittu, wadanda ke jiran saduwarku domin su yi amfani da wannan dama su yi kai-komo tsakaninku, kila ma kuma su yadu a tsakanin al'umma.

Kila nan gaba kadan za mu san karin wasunsu. Smith ta ce, ''yadda ake da sha'awa da zakwadin bincike kan kananan halittun da ke cikin jikin mutum, yanzu akwai sabbin hanyoyi da dabaru na dubawa da kuma tantance yawa da irin aikin wadannan halittu, hanyoyin da shekaru goma baya ba mu da su.''

Amma dai a yanzu a yi taka tsantsan.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Surprising benefits of sexually transmitted infections