Dajin da halittu suka zama duwatsu

Hakkin mallakar hoto Javier Etcheverry Alamy Stock

Patagonia yanki ne maras yawan jama'a da ke ƙuryar kudancin Latin Amurka, a yankin ƙasashen Argentina da Chile, wanda yake da dazuka masu tarin abubuwa na ban mamaki na halittun zamanin da, da suka zama duwatsu.

Michelle Douglass ta ziyarci yankin.

Lardin Chubutu a kudancin Argentina, da ke wannan yanki, wuri ne da yake da tarin duwatsu wadanda wasu halittu ne da suka rayu shekaru miliyan 65 baya, suka rikide suka zama duwatsun. Lardi ne da ya kunshi irin wadannan dazuka inda halitta (mai rai) ta juye ta zama dutse.

Dakta Peter Wilf na jami'ar Penn State ta Amurka ya ce, ''yawancin mutane suna daukar wurin a matsayin mai ban tsoro, amma ni a guna wuri ne mai ban sha'awa da mamaki.''

Hakkin mallakar hoto Javier Etcheverry Alamy Stock
Image caption Bishiyoyin da suka rayu shekara miliyan 65 baya ne suka yi dajin Jose Ormachea, inda suka zama duwatsu

Dakta Wilf ya kara da cewa, ''kusan babu wata bishiya ko ciyawa ko tsuro irin na zamanin nan, wuri ne da yake a bushe karau, kuma ga iska mai tsananin karfi. Duk da kasancewata kato amma iskar ta kan nemi ta dauke ni.''

Wadannan siffofi dai sun samu ne sakamakon abin da masana kimiyya ke bayyanawa da yanayin yadda jikin halittu, dabbobi ko tsirrai ke juyewa ya zama dutse. Sai dai halittar za ta zama karama daga yadda aka santa, amma kuma da siffarta yadda take a da.

Daktan da shi da wasu masu binciken daga Amurka da kuma Argentina sun yi shekara 16 suna gudanar da bincike a dazukan.

Hakkin mallakar hoto Dr. Peter Wilf
Image caption Wani tsohon gungumen bishiyar da ta rayu shekaru miliayan 65, wanda ya zama dutse a dajin Ormachea Park a Argentina

A wannan lardi na Chubut akwai surori ( na dutse) na halittu iri daban-daban masu wata irin halitta ta daban, kama daga na dabbobi da bishiyoyi da furanni da 'ya'yan itatuwa na kusan duk wani karni.

Amma watakila abubuwan da suka fi daukar hankali a dazukan su ne manya-manyan guma-guman bishiyoyi na zamanin da, wadanda su ma sun zama duwatsu.

Dakta Wilt ya ce, yana ganin wadannan bishiyoyi ba a nan suka girma ba. Ruwa ne ya kawo su wurin, daga gabar tekun Atalantika ta kudu inda suke, sakamakon ambaliya. Ruwan ya kawo su nan ya binne a cikin kasa, bayan tsawon lokaci kuma suka zama duwatsu.

Hakkin mallakar hoto Krystyna Szulecka Photography Alamy Stock
Image caption Dajin Cerro Cuadrado na ɗaya daga cikin dazuka masu abubuwan mamaki a duniya

Dakta Wilt ya ce, ''bayan wani lokaci mai tsawo ne kuma sai zaizayar kasa ta sa suka fito waje ake ganinsu haka da kyau.''

Kowane daji a wannan yaki yana da wani abu na daban mai ban mamaki.

Can cikin bangaren kudanci akwai wani yanki da ake kira Cerro Cuadrado, wanda yake da manya-manyan bishiyo na ban mamaki, da suka zama duwatsu, wadanda kuma har yanzu suke a wurin da suka fito.

Mai binciken ya ce, ''ba kamar bishiyoyin yankin Ormachea Park ba, shi wannan yankin (Cerro Cuadrado), ruftawar dagwalon talgen sinadaran da ke samar da dutse ta bannata bishiyoyin wurin, har kuma suka zama yadda suke a yanzu.''

Masanin ya kara da cewa, akwai abubuwa da dama masu matukar ban sha'awa da mamaki wadanda suke cikin siffarsu ta ainahi, wadanda kuma suke da matukar amfani ga kimiyya, kuma an sayar da su ta kasuwar bayan fage. Ya ce ko da yake yanzu an kare wannan daji, amma har yanzu ana sayar da wasu abubuwan ta haramtacciyar hanya.

Hakkin mallakar hoto Dr. Peter Wilf
Image caption Alamar wani ƙaton kututturen bishiya da ya zama dutse a kan wani tsauni a kusa da dajin Ormachea Park

Bayan wannan daji da ke Argentina, akwai fitattun dazuka masu irin wadannan abubuwa na mamaki da suka hada da tsibirin Lesbos da ke Girka da kuma wasu a Arizona da Wyoming a Amurka.

Wadannan abubuwa na mamaki na dajin na Patagonia, su suka sa Dakta Wilt zama a wannan yanki, kamar yadda yake cewa, ''wurare irin wadannan ne, inda ake da tarin abubuwa na alamar halittun zamanin da, ke bayyana labarin rayuwa a doron duniyar nan.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The land where life has turned to stone