Hanyoyi bakwai na sanin yadda mutuwa take

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ganin wani haske kwatsam a cikin wani ramin karkashin kasa kila a ce shi ne abin da aka fi kwatantawa da yadda mutuwa take, to amma kamar yadda Rachel Nuwer ya gano, yanzu akwai rahotanni da ke bayyana

wasu hanyoyin na daban da fahimtar kusan yadda mutuwa take.

A shekara ta 2011, an kai wani mutum mai shekara 57 da ke aikin yi wa jama'a hidima a birnin Landan, babban asibitin Southampton bayan da ya yanke jiki ya fadi yana aiki. Ana kokarin sanya masa wata na'ura da za a yi masa

aiki sai kawai zuciyarsa ta buga.Da aka cire masa na'urar da ke taimaka masa yin numfashi, daga nan kuma kwakwalwarsa ta daina aiki, ya mutu.

To amma duk da haka yana iya tuna abubuwan da suka faru a kansa. A lokacin da ma'aikatan asibitin suka ga ya mutu, nan da nan sai suka dauko wata na'ura da ake amfani da ita wajen farfado da aikin zuciyar mutum.

A lokacin da aka kunna na'urar sai kawai ya ji wata murya daga na'urar tana cewa, jijjiga maras lafiyar, har sau biyu.

A wannan tsakanin sai kawai ya ga wata mata a kuryar dakin kusa da rufin dakin tana kiransa. Sai ya tafi wurinta ya bar gangar jikinsa a nan.

Ya ce, ''ji na yi kamar ta sanni, na ga na amince da ita, kuma na ji kamar akwai dalilin da ya kawo ta, amma ban san ko menene ba.''

Wannan shi ne bayanin da mutumin ya yi na daga abin da zai iya tunawa ya same shi bayan da ya farfado daga halin mutuwar da ya shiga.

Ya kara da cewa, '' daga nan kuma kawai sai na gan ni a inda nake ga ma'aikaciyar jiyya da wani mutum mai sanko suna kallo na.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Bayanan da asibitin ya bayar na binciken da ya yi kan abubuwan da mutumin ya bayyana sun faru da shi a lokacin da ya mutun ko ya samu kansa a wannan hali na mutuwa, sun tabbatar da maganar nan da ya ji

har sau biyu ta na'urar da ke cewa ta jijjiga shi, da kuma bayanin irin mutanen da suke dakin, mutanen da bai taba ganinsu ba kafin hankalinsa ya dauke. Kuma ya ba da bayani dai-dai na abubuwan da suka yi a wannan lokaci

na tsakanin mintina uku, wanda wannan abu ne da muka san cewa bisa iliminmu na halitta, ba zai san yadda suka faru ba.

Wannan labari na wannan mutum, wanda aka rubuta a mujallar harkokin lafiya mai suna Resuscitation, daya ne daga irin rahotannin da ake samu da ke sa shakku ko kalubalantar irin labarai da hanyoyin da aka yadda da su a

baya na halin yadda mutuwa take.

Kafin yanzu, masu binciken kimiyya suna ganin cewa idan zuciya ta daina bugawa kuma ta daina tura jini kwakwalwar mutum, daga nan wannan mutumin zai daina sanin duk wani abu da ke faruwa da shi.

A wannan lokacin a bisa tsarin likitanci wannan mutum ya mutu. To amma yanzu karuwar ilimin da ake samu kan yadda mutuwa take, mun fara fahimtar cewa, a wasu lokutan za a iya shawo kan wannan lamari, a farfado da mutum.

A shekaru da dama, mutanen da suka taba shiga wannan yanayi na mutuwa da ba a san yadda yake ba, kuma suka farfado, su kan iya bayar da bayanin abubuwan da suka faru da su.

Yawancin likitoci sukan yi watsi da irin wadannan bayanai ko sheda da cewa mafarki ne kawai mutum ya yi.

Kuma masu bincike suna dari-darin yin nazari akan lamarin, na yanayin kusa da mutuwa da mutum kan tsinci kansa a ciki, saboda abu ne da ake ganin ba ya tsarin kimiyya, wato abin da za a iya gani a bayyane kirikiri.

Sam Parnia, wani kwararren likitan mutanen da ke halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai kuma darektan bincike a wannan fanni, a Jami'ar Stony Brook da ke New York, tare da wasu abokan aikinsa daga jami'oi 17 a Amurka da Ingila,

sun yi watsi da hasashen abubuwan da suke faruwa da mutum a lokacin da yake bakin mutuwa.

Amma kuma sun yarda cewa abu ne da zai yuwu a iya tattara wasu bayanai na kimiyya game da wannan lokaci ko hali na mutuwa da mutum yake ciki.

Saboda haka wadannan kwararrun masana a harkar lafiya, suka yi shekara hudu, suna nazarin yanayin mutanen da suka gamu da bugun zuciya, wadanda zuciyar ta daina aiki kuma aka ayyana sun mutu a bisa tsarin aikin likita, sama da dubu biyu.

Daga cikin irin wadannan marassa lafiyar da ka ayyana sun mutu, likitoci sun yi kokarin farfado da kashi 16 cikin dari.

Kuma Dakta Pania da abokan aikinsa sun tattauna da 101 daga cikinsu, domin kokarin sani ko fahimtar wasu abubuwa, wadanda farko shi ne yanayin hankali da tunanin halin mutuwa da mutum kan shiga.

Dakta Pania ya ce, ''mun yi hakan ne domin mu ga idan akwai wadanda suka yi ikirarin cewa sun ji wata magana ko sun ga wani abu a lokacin da suka shiga wannan yanayi na mutuwa, mu ga idan har lalle sun san abin da ke faruwa da su a lokacin.''

Dandanon mutuwa bakwai

Bincike ya nuna cewa wannan mutumin na birnin Landan da muka yi maganarsa a baya, da ya bayar da bayani akan yanayin mutuwa da ya shiga kuma ya farfado, ba shi kadai ba ne maras lafiyar da ya iya tuna abubuwan da suka faru da shi na lokacin mutuwa.

Kusan kashi 50 cikin dari na wadanda aka gudanar da bincike a kansu, sun iya tuna wani abu.

To amma in ban da mutumin na Landan da wata mata daya wadda ita kuma ba a iya tantance abubuwan da ta fada ba a zahiri, bayanan da sauran marassa lafiyar suka bayar, kamar ba su danganci ainahin abubuwan da suka faru da su ba a lokacin da suke yanayin na mutuwa.

A maimakon haka sun bayar da bayanai ne da suka yi kama da mafarki, wadanda Dakta Pania da sauran abokan bincikensa suka kasa zuwa gida bakwai.

Daktan ya ce, ''yawancin wadannan abubuwa ba su zo daidai da abin da ake kira yanayi na kusan mutuwa ba.''

Ya kara da cewa, '' ga alama yanayin halin da mutane kan shiga na kusan mutuwa ya wuce yadda a baya aka dauka.''

Dandanon mutuwa bakwai da likitocin suka kasa su ne;

1 Tsoro 2 Ganin dabbobi ko tsirrai 3 Haske 4Tashin hankali da cin zarafi 5Ganin wani dan uwa ko iyali 6Tunawa wani abu da ya faru kafin zuciya ta daina aiki 7 Jin cewa abin da ya faru da kai daman ya taba samunka.

Duka wadannan yanayi ko tunani da mutum zai iya samun kansa a ciki sukan iya ksancewa masu dadi ko kuma masu ban tsoro.

Akwai wadanda suka bayar da bayanin jin tsoro wani abu na tayar da hankali zai same su. Misali wani maras lafiyar, ya iya tuna cewa, ya ga zai je wani taro inda za a kona shi.

Wani kuma ya ce, ''a kwai mutane hudu da suke tare da shi kuma duk wanda ya yi karya a cikinsu zai mutu.'' Wani ya ce, ''na ga mutane a cikin akwatin gawa ana binne su a tsaye''

Yayin da shi kuma wani maras lafiyar ya ce ya iya tuna cewa, '' na ga yadda ake ja na a kasa ta cikin wani kogi mai zurfi.''

Haka shi kuma wani cewa ya yi,''an gaya min cewa zan mutu kuma hanya mafi sauri ita ce in fadi kalmata ta karshe da zan iya tunawa.''

Sauran marassa lafiyar kuwa abubuwan da suka ce sun iya tunawa a lokacin da suka shiga yanayin na mutuwa kusan kishiyoyin na wadancan na baya ne, inda kashi 22 cikin dari suka bayar da bayanan abubuwa masu dadi da kwanciyar hankali.

Wasu sun ga abubuwa masu rai, inda wani ya ce, ''na ga tsirrai gaba daya ba furanni'' ko ''zakuna da damusoshi''.

Wasu kuwa cewa suke sun wani haske mai yawa ko kuma sun gamu da iyalansu.

Wasu marassa lafiyar kuwa ji suke sun ji yanayi na sanin abin da wasu mutane za su yi tun kafin su aikata abin.

Abubwa daban-daban dai mutane su kan bayyana sun iya tunawa a lokacin da suka shiga yanayin na gargara.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Dakta Parnia, ya ce, ''duk da cewa lalle mutane suna iya bayar da bayanin wasu abubuwa da suka faru da su a lokacin da suka shiga yanayi na mutuwa, to amma fassararsu ta dogara ne ga airin rayuwar da suka

taso a ciki da kuma abin da suka yi imani da shi a baya.''

Ya ce, ''wani da ya fito daga India zai iya farfadowa daga mutuwar da ya yi, ya ce, ya ga Krishna, yayin da wani kuma daga yankin tsakiyar yammacin Amurka, wanda irin wannan abin ya faru da shi, ya ce, ya ga Yesu.''

Dakta Pania ya kara da cewa, ''idan wani Uba a yankin tsakiyar yammacin Amurka ya gaya wa dansa cewa, ''idan ka mutu za ka ga Yesu, dan zai kasance cikin farin ciki da murna, da burin hakan, kuma ba shakka zai gan shi.''

''Zai dawo ya gaya wa Uban cewa baba ka yi gaskiya, lalle kam na gan Yes!''

To amma kuma akwai wani a cikinmu da zai iya cewa ga yadda Yesu yake idan ka gan shi ka san shi?

Ya ce, kai ba ka san Yesu ba, ni ma ban san shi ba, in ban da hoton wani mutummai farin gemu.

Ya ce, abin da ya fi kawai shi ne abar wannan magana kawai ta koyarwar addini a koma kan abin da yake a zahiri.

Amfani da hankali

Ya zuwa yanzu dai, Dakta Parnia da sauran abokanan bincikensa ba su gano wani abu da zai sa su iya gane mutumin da zai iya tuna wani abu da ya faru da shi a lokacin da ya shiga gargarar mutuwa ba.

Kuma babu wani bayani na dalilin da ya sa wasu suke bayar da bayanin abu mai dadi da ya faru da su wasu kuma suke bayar da na tayar da hankali a wannan lokaci.

Masanin ya ce, '' da alama mutane da dama suna gamuwa da wannan lamari, to amma wasu da suka farfado suna manta abin da ya faru da su saboda yawan kumburar da kwakwalrsu ta yi a lokacin a dalilin tsayawar zuciyarsu

ko kuma saboda magungunan sa barci da aka ba su a asibiti.

Ya ce ko ma mutum bai iya tuna bin da ya faru da shi farat daya, lamarin zai iya shafar tunaninsa.

A don haka ya ce yana ganin, wannan shi ne abin da ya sa mutanen da suka gamu da ciwon bugun zuciya har suka farfado daga wannan yanayi na mutuwa ba sa tsoron mutuwa yayin da wasu kuma sukan gamu da damuwa.

Tuni dai Dakta Parnia da sauran abokan aikinsa suka shiga shirin gudanar da wani binciken domin gano wasu daga cikin abubuwan da ke tattare da wannan yanayi na mutuwa.

Haka kuma suna fatan binciken nasu zai sa su warware sirrin da ke tattare da wannan lamari na mutuwa kamar yadda ake ganin lamarin a bangaren addini ko tunanin dan adam.

Dakta Parnia ya ce, ''yanayin na mutuwa abu ne da za a bincika a fagen kimiyya kamar sauran abubuwa kuma duk wanda ke da burin tsage gaskiyar abu yadda yake zai amince da fadada wannan bincike saboda muna da dama

da kuma fasahar yin hakan. Kuma yanzu yanzu ya kamata a yi binciken''