Gaskiya ne Apple na gab da kera mota?

Jita-jitar cewa kamfanin Apple zai fara kera motoci ta kasance daya daga cikin mayan labarai na fasaha da suka fi bazuwa a dan wani lokaci da ya gabata a shekarar nan.

Ya yuwuwar hakan take, kuma wana kalubale kamfanin zai fuskanta wajen zama mai kera motoci ? Jack Stewart ya bincika.

A halin yanzu dai duk wannan magana dai jita-jita ce kawai da sauran maganganu na cewa ya hakan za ta kasance duk dai a kan tunanin me zai faru idan kamfanin Apple ya karkato da fasaharsa kan titunanmu.

Wannan ba shi ne karon farko da aka fara wannan rade radi ba, domin akwai rahotannin da ke cewa kamfanin na Apple yana daukar hayar kwararru daga kamfanin da ke kera mota mai amfani da wutar lantarki irinsu Tesla da

kuma masu yin baturan mota.

Kuma an ce suna aikin kera wata mota a shekaru da dama a asirce.

Bloomberg ya yi ikirarin cewa kamfanin na kwamfuta yana son ya kera mota ne zuwa shekara ta 2020.

Kuma wani mai watsa labaran fasaha ta shafin intanet, Gruber, wanda ya yi watsi da jita-jitar da farko, yanzu ya sauya ra'ayinsa bayan da ya gano cewa kwararrun da Apple ya gayyata sun hada da wani babban mai daukar

ma'aikata daga Tesla.

Hakkin mallakar hoto Aston Martin

Masu sharhi kan harkokin fasaha suna ganin motoci su ne za su kasance sababbin wayoyin tafi-da-gidanka.

Ko bikin baje-kolin kayan laturoni da aka yi na wannan shekarar na Las vegas ya zama kamar taro na manyan kamfanonin kera motoci inda ya shafe bikin baje kolin motoci na Detroit, wanda aka yi bayan 'yan kwanaki.

A wurin bikin na Las Vegas an baje kolin fasahohin irin motocin da ake shirin kerawa a nan gaba da kuma fasahohin tuki.

''Abin da muke gani sauyi ne da zai zo a ababan hawa ya fara kunno kai.'' In ji Bryan Reimer na Sashen Sufuri a jami'ar New England.

Shi dai kwararre ne a fannin kiyaye haduran ababan hawa da kuma dabi'ar matuki.

Ya ce, ''ana ganin tsarin da sanfurin motocin da za su zo nan gaba zai sauya sosai a 'yan shekaru masu zuwa, inda za a ga motoci masu wasu ayyuka ko karin abubuwan fasaha daban.

Wannan ke nan zai sa sabbin kamfanonin kera motoci su fara wasu karin ayyuka kamar su Google da Uber( masu sanya na'uar da ke nuna kudin da mutum zai biya a tasi idan ya shiga).''

Reimer na ganin yadda kamfanin Apple ya samu karbuwa wajen jama'a saboda irin kayayyakin fasaha da ya kirkiro, hakan zai ba sa ya samu kasuwa fiye da sauran kamfanoni idan ya shigo kasuwar kera motoci na zamani.''

Ya ce, ''ina ganin abin da Apple zai kawo idan zai shigo wannan fage shi ne iyawa da kuma kudin yin wani abu na daban.''

Idan kalubalen da Google ya gamu da shi wajen yin motoci wani abu ne da za a yi la'akari da shi, to fa sai a ce abin da kamar wuya.

Hakkin mallakar hoto PA

Kamar yadda BBC ta gano a lokacin da wakilanta suka ziyarci dakin binciken kimiyya da fasaha na Google a bara, ta ga cewa kamfanin ya dauki shekaru da yawa kafin ya iya sake tsarin motocin da za su rika tuka kansu da kansu.

Sabuwar motar ta zamani mai tuka kanta ta kamfanin na Google tuni ta gamu da kalubalen shari'a, inda hukumomi suka tilasta wa kamfanin ya sa abubuwan da za a iya tuka motar da su kamar sauran motoci kari akan wanda

suka tsara mata na ainahi na tuka kanta da kanta, wanda wani abin dannawa ne kawai.

Farfesa Jeffrey Miller na cibiyar kwararru ta Institute of Electrical and Electronics Engineers(IEEE) da kuma Jami'ar Southern da ke Carlifornia, ya ce shi kam ba ya ganin Apple na shirin shiga harkar kera motoci ne.

Ya ce, ''ina ganin kamfanin dai yana sha'awar sanya abubuwan da yake kerawa ne a motoci kawai amma ba kera motocin ba.''

Ya ce ''kamar dai yadda Google yake hada gwiwa da kamfanonin kera mota a sa fasaharsa ta yadda mota za ta tuka kanta da kanta, shi ma Apple zai yi hakan ne ya zo da wasu fasahohin ta yada da za a samu gogayya.''

Ya kara da cewa, ''daman tuni Google da Apple din suke gogayya da juna kan abubuwan da suka sa a motoci na sanfurin fasahar Android da iOS. Kuma wadannan duka kwararrun kamfanonin kera manhajar kwamfuta ne da ke

da kwararrun masana da za su bunkasa kasuwar motar mai tuka kanta.''

Motar Google; kamfanin na fasaha shi dai yana son fara kera motocinsa ne maimakon ya dogara ga irin motocin da aka saba kerawa, amma har yanzu da sauran kalubale inji Miller.

Hakkin mallakar hoto AP

Ya ce akwai bukatar kara inganta yadda na'urar kwamfutar motar mai tuka kanta take, ta yadda za ta iya gane abin da yake tsaye da kuma wanda ke tafiya a titi.

Kuma ya ce, sai an yanke shawara kan hakan a bisa bayanan da aka samu kuma a sanya ka'idoji na shari'a

Shi kuwa Reimer ya ce kalubalan bai tsaya a nan ba, inda ya ce babbar matsala ga Apple ta shiga wannan fanni ita ce ba su taba aiki a fagen da ake da dokoki masu tsauri ba kuma hukuka take sanya idi sosai a kai.

Yana ganin harkokin kayan laturoni daban suke da na mota, wadanda akwai dokoki masu tsauri a kansu kuma sun bambanta daga kasa zuwa kasa.

Ya ce, ''akwai dai dama, to amma maganar ita ce ya Apple zai iya fuskantar kalubalen da ke wannan fage maras girma.''

An kuma san Apple da tsayawa ya natsu ya kirkiro abin da yake mai nagarta da inganci ba wai kawai ya kirkiri abin da kawai za a ce shi ma ya bullo da nasa ba.

A matsayinsa na kamfani Apple da alamu ba ya damuwa ya ce wai sai ya zama na daya a kasuwa, burinsa kawai shi ne ya yi abin da za a saya da daraja.

Idan kuwa ya yi haka a harkar kera motoci, to ba shakka zai san ya shiga kasuwar da ake gogayya.

To amma kuma duk da haka kamfanin yana da dimbin kudin da zai iya saye wani kamfanin kera motocin da aka sani ya mayar da shi yadda yake so. Ba abin da zai gagara.

Ko ma ya lamarin ya kasance, ranar da mutane za su taru a wajen sayar da motoci domin sayen iCar kamar yadda suke yi wajen sayen sabon sanfurin wayar iPhone, watakila wannan rana na da sauran lokaci.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Could Apple really be about to make cars?