Kokarin kirkiro maganin cutar sukari

Hakkin mallakar hoto AFP

Masana kimiyya na da kwarin gwiwa sinadarin insulin da aka kirkiro wanda kuma ake jarrabawa yanzu zai iya taimaka wa masu cutar sukari.

Maimakon maras lafiya ya rika yin gwajin jini ko da yaushe da kuma allura a duk tsawon rana domin daidaita sukarin jininsa, amfani da sabon sinadarin insulin din da aka kirkiro zai taimaka masa, ta yadda zai rika yawo a jikinsa, da zarar bukatarsa ta taso sai ya fara aiki.

Binciken da aka gudanar akan dabbobi ya nuna cewa sinadarin yana aiki a jikin bera.

Kuma ana shirin gwada shi a jikin dan-adam nan ba da dadewa ba kamar yadda mujallar PNAS ta ruwaito.

Sai dai kwararru sun nuna cewa za a yi shekaru ana gwajin kafin a fara amfani da shi wajen yi wa marassa lafiya magani.

Marassa lafiyar da suke da nau'in cutar sukari na daya wadda ake kira type 1 a turance, wadanda ko dai jikinsu ba ya samar da sinadarin insulin ko kuma ba ya amfani da shi, sun dogara ne ga allurar sinadarin na insulin wajen

samun lafiya, kuma in ba da hakan ba yawan sukarin jininsu zai yi yawa matuka wanda hakan illa ce ga lafiyarsa.

To amma kuma yin allurar sinadarin insulin ita kanta za ta iya sa yawan sukarin cikin jinin maras lafiyar ya ragu sosai wanda kuma hakan ya sa dole ne maras lafiya da ke fama da nau'in cutar na daya ya rika duba yawan sukarin

jinin nasa domin ya tabbatar daidai yake.

Saboda wannan abu ne kwararru a kan cutar ta sukari suke ta kokarin gano hanyoyin saukaka yadda maras lafiya zai rika kula da yawa ko karancin sukarin jinin nasa, wanda a kan hakan ne maganar wannan sinadari na insulin

da ake neman kirkirowa ta zo.

Akwai nau'in wannan sinadari na insulin 'yan kadan da masana kimiyyar suke kokarin kirkirowa ko hadawa, kuma dukkansu ana tsara su ne ta yadda za su rika sa kansu da kansu aiki da zarar yawan sukarin jinin mutum ya yi

yawa, kuma su daina aiki da kansu idan yawan sukarin ya dawo daidai.

Hakkin mallakar hoto alfred pasieka

Dakta Danny Chou na makarantar fasaha ta Massachusetts (Massachusetts Institute of Technology), yana jarraba sinadarin na insulin wanda shi da abokan aikinsa suka kirkiro.

Dakta Chou ya ce, ''burina shi ne na saukaka tare da inganta lafiyar masu cutar sukari.''

''Kuma wannan muhimmin cigaba ne a fannin maganin sinadarin insulin.''

Shugabar Gidauniyar bincike kan cutar sukari ta JDRF, wadda ke Biritaniya, Karen Addington, ta ce, ''daidaita yawan sukarin jinin mutum shi ne abin da masu cutar sukari nau'in ta daya suke fama da shi a kullum.

Inda kuma wata matsala da ke tattare da kokarin yin hakan ita ce, idan suka yi allurar insulin din har sinadarin ya yi yawa sai ya sa yawan sukarin ya yi kasa sosai, a daya bangaren kuma idan allurar ta yi kadan yawan sukarin

sai ya yi sama wato ya karu sosai, wanda kuma hakan zai haifar wa da maras lafiya illoli a can gaba.

''Shi sinadarin insulin da masana kimiyyar suke kokarin kirkirowa zai kawar da matsalar da masu cutar sukarin nau'in ta farko suka fi fama da ita ne ko ta fi damunsu, wadda ake kira hypo, wadda take kasancewa idan suka yi

allurar insulin din sinadarin ya yi yawa, ya sa sukarin jininsu sai ya yi kasa sosai.

Sinadarin na kimiyya zai rika daidaita yawan sukarin jinin masu larurar ne da zarar yawan sukarin ya yi kasa. Kuma allura daya a rana ko ma a mako ce za ta rika yin wannan aiki. Wanna abin ban sha'awa ne kwarai.''

Dakta Richard Elliot na Diabetes UK, ya ce, ''ana bukatar karin bincike da gwaji na shekaru domin a gano ko akwai wani magani mai tasiri da masu cutar sukarin za su iya amfani da shi lami lafiya ba tare da wata illa ba.''

Cutar Sukari;

Hakkin mallakar hoto bbc

Cutar sukari iri biyu ce; nau'in ta daya da nau'in ta biyu wato type 1 da type 2 a turance.

Nau'in cutar na daya wanda kusan kashi 10 cikin dari na masu cutar sukarin suke da shi, garkuwar jikin maras lafiyar ne take lalata kwayoyin halittar da suke yin sinadarin na insulin.

Shi kuwa nau'i na biyu na cutar yana kasancewa ne idan ko dai idan jikin mutum ba ya iya yin isasshen sinadarin insulin din ko kuma kwayoyin halittar ba sa aiki a kan sinadarin.

Masu cutar sukarin nau'in ta farko suna bukatar magani ne da sinadarin na insulin, yayin da su kuma masu cutar nau'in ta biyu za su iya kula da lafiyar tasu ne ta hanyar cin abinci mai kyau da motsa jiki a kai a kai da kuma kula

da yawan sukarin jininsu.