Ta yaya za ka fi maganin mantuwa

Dukkaninmu muna son a ce kwakwalwarmu tana aiki sosai ba tare da wata matsala ba yayin da muke girma. To amma ta wadanna hanyoyi ne za mu fi iya yin hakan? Tambayar da Micheal Mosley ya yi ke nan.

Ka tambayi duk mutumin da ya wuce shekara 40 menene yake damunsa da shekaru, amsar da zai ba ka ita ce fargabar manta abubuwa.

Na damu sosai kan yadda ba na iya tuna sunaye kuma idan wayata ta salula ba ta tuna min ba zan manta abubuwa da yawa da na shirya yi a kullum.

Akwai abubuwan da za ka kauce wa idan kana son kwakwalwarka ta zama da kyau, wato ba ka manta abubuwa.

Abubuwan sun hada da shan taba da kiba ko teba da kuma kaucewa cutar sukari nau'i na biyu.

To amma kuma wadanna abubuwa ne za ka yi da za su kara maka karfin kwakwalwa, ka rika haddace abubuwa ?

Da taimakon Jami'ar Newcastle mun samo mutane 30 da suka amince a gudanar da gwaji da su.

Kafin mu fara gwajin namu, mun gudanar da jerin bincike a kan dukkanin mutanen inda muka abubuwansu kamar karfin haddarsu da iya samo amsar wata matsala da kuma kuzarinsu na mayar da martani.

Daga nan kuma sai aka makalawa kowannensu wata na'ura da za ta rika nadar bayanan aikin da yake da kuma lokacin da suke tafiya.

Sai aka kasa su gida uku kuma aka ba wa kowana rukuni ko kashi wani aiki da mutanen rukunin za su yi har tsawon makwanni takwas.

Rukuni daya aka sa su su rika sassarfa wato tafiya da sauri-sauri ta yadda za su rika haki na karancin numfashi har tsawon sa'oi uku a kwana sati.

Dabarar hakan ita ce wannan tafiya ko sassarfa ko ma dai duk wani aiki na motsa jiki zai sa kwakwalwarka ta kasance cike da jini mai dauke da iska.

To amma wannan ba abu ne da wasu mutanen suke so ba. Kamar yadda Ann ta ce ba ta kaunar tafiya da kafa.( Newcastle tana da tsaunuka masu wuyar hawa)

Rukunin mutanen na biyu su kuma an ba su aikin hada haruffa ne domin fitar da sunayen kalmomi da sauransu wanda ake kira puzzles ko Sudoku. Su ma za su yi aikin ne na tsawon sa'oi uku a mako.

Dalilin wannan shi ne, ita kwakwalwa kamar tsoka tana son a sa ta wani abu da zai sa ta motsi, ma'ana wani abu da zai zama kalubale a wurinta. Yi amfani da ita ko ka rasa ta, kamar yadda ake mata take.

Rukunin mutanen na uku su kuma an sa su kallon hoton wani mutum ne Steve, wanda yake tsirara a aji, kuma su zana hoton. Su ma za su yi hakan ne na sa'oi uku a mako.

Sakamako;

A karshen mako na takwas kusan kowa a cikin rukunin mutanen farko da suke sassarfa ko tafiya ya ji cewa ya samu wani ci gaba sosai a lafiyar jikinsa gaba daya. Har ma ya zama ba sa jin wahalar hawan wani tsauni.

Su kuma wadanda aka ba su aikin hada kalmomi, da farko abin ya rika ba su wahala. Amma kuma yau da gobe zuwa karshen sati na takwas din sai ya kasance ba sa jin wata wahalarsa kuma sun saba har ma suna musayar

dabaru kan yadda ake yi.

Rukuni na uku kuwa wadanda aka sa su a aji suna kallon gunkin mutum tsirara suna zana shi, duk da cewa wasunsu sun ji wahalar zama a aji sau daya a mako tsawon sa'oi uku, to amma kuma dukkaninsu sun bayyana jin dadin hakan.

Daya daga cikinsu mai suna Simone, ya ce,'' yanzu na zama mai sha'awar zanen komai a ko da yaushe.''

''Yanzu har na sayo fensiran zane da littafin koyon yadda ake zane.''

Wannan ya nuna cewa zane daidai yake da wani abu na jin dadi da ban sha'awa. To amma 'yan wana rukuni ne suka fi jin dadin bunkasa kwakwalwarsu a sanadin ayyukan da aka ba su ?

Ba shakka dukkanin mutanen na rukuni ukun da aka sa wadannan ayyuka daban daban sun samu cigaba a fannin bunkasar kwakwalwarsu, amma 'yan rukuni na ukun nan da aka sa a aji su suka fi cigaba.

Hakan na nufin gunkin Steve, wanda yake tsirara, da aka ajiye musu ya yi matukar tasiri a kansu.

To amma ta yaya zuwa aji domin koyon zane zai haifar da wani sauyi a abu kamar kwakwalwa ko haddar mutum?

Hakkin mallakar hoto SPL

Daya daga masanan da suka gudanar da binciken daga Jami'ar Newcastle, Daniel Collerton, ya ce daya daga cikin amfanin hakan shi ne koyon wani abu sabo.

Ya ce, ''kokarin koyon sabon abu yana sa kwakwalwa kan abin da yake kamar mabudinta. Kwakwalwarka za ta farfado komai yawan shekarunka.''

Koyon yadda za ka yi zane ba sabon kalubale ba ne kadai ga 'yan wannan rukuni na uku, ba kamar masu koyon hada kalmomi ba, ya hada da farfado ko raya saurin tunanin mutum.

Zanen wani hoto a takarda ba abu ne mai sauki ba, domin ya kunshi koyon yadda za ka sarrafa tsokar hannunka ka rika juya fensir ko alkalamin da ka rike ko burushi ta yadda ya dace.

Bayan wannan kuma wani karin amfanin shi ne zuwa ajin na nufin za su tsaya tsawon sa'oi uku a sati suna zanen hoton. Kuma hakan kamar yadda bincike ya nuna mutum ya dade a tsaye wata hanya ce ka rage kiba da kuma

kara lafiyar zuciya.

Haka kuma shi ajin na koyon zane, wuri ne na walwala tsakanin 'yan wannan rukuni fiye da na sauran, wanda wannan wani abu ne da ke taimakawa idan kana son bunkasa kwakwalwarka ta rika tunani da hadda da kyau.

Sannan kuma 'yan wannan rukuni suna haduwa a wajen aji a kai a kai kuma ta haka suna rubuta wa juna wasika ta email, wanda hakan ma wata hanya ce ta kulla zumunta a tsakanin wasunsu kuma wannan yana da tasiri wajen raya kwakwalwarsu.

Dukkanin wadannan sun nuna cewa 'yan wannan rukuni sunsamu damar cin moriya uku idan ana maganar inganta lafiyar kwakwalwa.

Daya daga cikin 'yan wannan rukuni, Lynn, ta ce koyon yadda za ta yi zanen ya sa ta amfana da wasu abubuwan daban wadanda ba ta yi tsammani ba.

Ta ce,''yanzu rubutuna da yadda nake natsuwa idan ina abu duk sun inganta. Abin kamar ya bunkasa tunanina. Kai bana jin zan iya bayanin abin sosai, ni dai na son na karu sosai.''

Duk abin da za ka yi tare da mutane, wanda ya kunshi haduwarku da koyon wani sabon abu zai iya taimakawa wajen bunkasa kwakwalwarka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What's the best way to fight memory loss?