Shin kana tsoron lissafi?

Hakkin mallakar hoto z

Mutane da yawa suna da fargaba ko tsoron lissafi da ka, abin da yake sa musu tsoron lambobi a duk tsawon rayuwarsu.To me yake sa kwakwalwa ta tsaya ta kasa aiki idan mutum yana lissafin lambobi ko abubuwa masu yawa? David Robson ya duba wannan matsala.

Tafin hannunka na gumi ga gabanka na faduwa ga kuma makaki a makogaronka.Duk wadannan yanayi ne da wasu mutane kan samu kansu ciki idan suka fuskanci lissafi.

Babu wani abu da yake sa min fargaba da tsoro kamar a ce in yi wani lissafi a gaban jama'a. Hatta dan karamin lissafi mai sauki na abin da ya shafi kudin abinci da sauran 'yan abubuwa yakan ba ni wahala.

Duk yadda na mayar da hankali a kai abin na ba ni wuya, sai lissafin ya rika bace min, in rika hararo wani abu daban a matsayin amsar lissafin.

Lissafi abu ne da yake ba wa wasu mutane wahala , domin hatta takardar rasiti na sayen wani abu na sa su fargaba.

Kana iya tuna irin mafarkin nan da mutum kan yi inda ya kan farga cewa ya manta kayan sawarsa gaba daya a yayin wani bulaguro? To kamar haka lamarin yake.

Wani abu da lissafi shi ne duk yadda wahalarsa take idan ni kadai zan yi shi ba a gaban wasu ba, ba na jin wahalarsa. To amma ko da digiri nake da shi a lissafi idan ka ba ni dan karamin aiki na lissafin in dai a bainar jama'a ne

ko da tuna lambar bude mukullin dakina ne to fa ka hada ni da aiki.

Da na fahimci cewa ba ni kadai nake fama da wannan tsoro ko fargaba kan lissafi ba hankalina ya kwanta, domin abu ne da aka yi kyakkyawan bincike a kansa. Abin dai kamar tsoron lambobi ne kawai.

To amma ni abin nawa da sauki domin matsalata, ita ce idan a take ake son na yi lissafin kuma da ka. Haka kuma idan lissafi ne da yawanci ya kunshi harufa maimakon lambobi ba ni da matsala.

Amma a wurin mutane da dama matsala ce babba, da ta sa masana tunanin dan-adam suke gudanar da bincike kan abubuwan da ke jawo wannan tsoro na lambobi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Jarrabawar lissafi ta kan shafi bangaren kwakwalwar mutum ne da ke aiki idan ya ji wa kansa rauni.

Da farko dai masana tunanin dan-adam suna gwada tsoron da mutane ke da shi na lissafi ne ta hanyar amfani da takardar da ke dauke da wasu tambayoyi, inda suke bukatar mutum ya kwatanta yawan fargabar da yake ji idan

ya bude littafin lissafi zuwa shiga dakin wata jarrabawa mai muhimmanci.

Ko da ike dai ana gudanar da binciken ne a kan kananan yara, to amma ya nuna cewa abin zai iya shafar daliban jami'a da manya, domin ko kallon rasitin siyayyar kayayyaki ya kan tayar da hankalin wasu.

A baya bayan nan masana sun samu damar gudanar da bincike a kan lamarin, inda suka ga cewa duk da dai lissafi ba wani hadari ba ne na zahiri da mutum ke fuskanta, jikin dan adam yana tunkararsa kamar yadda yake

fuskanatar hadari na gaske.

Har yanzu ba a san dalilin da ya sa darasin lissafi yake sa wa mutum fargaba da tsoro ba kamar darasin sanin yanayin kasa (Geography).

Kasancewar lissafi abu ne da ke da amsa daya, ta ko dai ya rubuta ta daidai ko kuma ya fadi, babu wata hanya da mutum zai yi wata dabara, wannan ya sa ake ganin hakan ne yake sa mutum ya kasa kokari a kai.

Kuma duk da wannan, ana ganin tsoron lissafin kamar sauran tsoro da mutum kan ji abu ne da ba shi da dalili, wanda kuma zai iya shafar kwazon mutum a jarrabawarsa.

Misali a shekara ta 2012 binciken da aka gudanar a Amurka na hotunan aikin kwakwalwar yara 'yan tsakanin shekara bakwai zuwa tara, an gano cewa a cikin yaran da ke tsoron lissafi bangaren kwakwalwar da ke kula da abin

da ya shafi barazana ga rayuwar mutum, yana aikatawu sosai, wanda hakan kuma ya sa har yake shafar bangaren da yake kula da abubuwan da ba na zahiri ba kamar abin da ya shafi tunani.

Wannan yasa masanan da suka gudanar da binciken suke ganin, tsoro ko faragabar da yaran suke yi na dakile kokarinsu na tsayawa su mayar da hankali a kan lissafin da aka ba su.

Wannan tsoro zai iya samo asali daga wurare da dama. To amma wani abu da ake gani shi ne, malamai za su iya yada wannan tsoro ko fargaba, domin yara sukan iya ganewa idan manya suna cikin wani yanayi na tsoro, wanda su kuma daga nan sai su fara duba hadarin da zai same su su ma.

Hakkin mallakar hoto

A kan hakan ne ake ganin malaman da suke da shakku a kan kwarewarsu a darasin lissafi suke samun dalibai masu irin wannan fargaba.

Ana kuma danganta matsalar ta tsoron lissafi ga al'ada, domin ana ganin mata za su fi saurin kamuwa da matsalar musamman daga malamansu mata, watakila saboda abin da aka dauka cewa daman mata ba su da kokari ko

kwazo a banagaren lissafi.

Kwayar halittarka ma tana sa ka ji tsoro a yawancin lokaci, inda ta kan sa ka rika jin tsoron lissafi da duk wata barazana.

To ko ma menene sanadin dasa kwayar halittar tsoron a ranka, da zarar ta samu gindin zama to fa za ta iya ci gaba da girma ne da kanta.

Da zarar kana jin tsoron lissafi, to ba za ka iya yin sa da kyau ba, haka kuma yayin da kake kara tsoron tunkararsa, yana sa maka fargaba da damuwa a duk lokacin da ka tunkare shi.

Kuma masana tunanin dan-adam na ganin hakan na da babbar illa a kan mutum, domin mutanen da ke da wannan tsoro na lissafi, ba kasafai za su fahimci kididdiga a kan illar abincin da aka jirkita kwayoyin halittarsa ba.

Wannan kuma zai iya sa mutum ya samu mummunar fahimta kan wani hadari kamar na shan taba da kuma cin abinci da yawa ko da ya wuce ka'ida.

Masana tunanin dan-adam galibi sukan magance matsalar fargaba ta hanyar sa mutum ya fuskanci abin da yake ba shi tsoron domin ya saba da shi.

Abin takaicin shi ne yawan zuwa darasin lissafi da alama baya maganin wanan fargaba.To amma akwai wasu hanyoyin.

Wata hanya mai sauki ita ce, ta rubuta bayanin abin da yake damunka ko sa ka fargaba, domin sau da dama bincike ya nuna, bayyana abin da yake damunka zai sa wannan damuwa ta rabu da kai.

Wasu dalibai da aka sa su rubuta abin da ke ba su tsoro ko fargaba kafin su rubuta jarrabawa, hakan ya sa kokarinsu ya karu.

Wasu kuma suna amfani da wasu hanyoyi ne na karfafawa yara zuciya cewa su daina daukar jarrabawar a matsayin wata barazana, inda suke bayyana musu cewa tsoron da suke yi ba lalle hakan na nufin ba za su iya ba ne.

Shin wannan dabara ta sa in kalli lissafi wanda yake sa ni fargaba ta wata siga daban zai sa in dena jin tsoronsa?

Ba shakka zan jarraba. Idan ma hakan bai yi aiki ba, to ai wayata ta salula tana nan, ba abin da zan yi sai kawai in dauko ta in yi lissafina da ita kawai.