Ana yi wa bishiyoyi wasika a Melbourne

Hakkin mallakar hoto al amy

Wasu mutane sukan yi wa shukokinsu wasika, amma a Melbourne wasikar email suke yi wa nasu.An samu yin hakan ne kuwa saboda yadda hukumomin birnin suka sanya kowace bishiya a cikin taswirar birnin suka kuma sa mata lamba ta daban.

Kusan wasikun email 3000 aka mutane suka aika wa bishiyoyi daban daban a cikin shekaru biyu da suka wuce.

Wannan abu ya faro ne sakamakon matakin da hukumomin birnin na Melbourne suka dauka na kare bishiyoyin birnin daga mutuwa sakamakon karancin ruwa, domin zuwa shekara ta 2009 kashi 40 cikin dari na bishiyoyi 77,000 na garin da ake wa lakabi da birnin lambun Australia suna ko dai mutuwa ko kuma kokarin yadda za su rayu.

Kansila Aron Wood ya ce, ''da yawa daga cikin wadannan bishiyoyi suna gab da mutuwa, mun kusa rasa kashi 50 cikin dari na bishiyoyinmu masu kyau.

Wanda da hakan zai matukar bata yadda birnin Melbourne yake da kyau da muhallinsa ya kuma shafi yadda mutane suke son birnin da ma tattalin arzikinsa.

''Abin da muka yi shi ne, sanya dukkanin wadannan bishiyoyi a taswirar birnin daga nan muka ba sanya wa kowacce daga cikinsu wata lamba tata ta daban domin mutane su iya tuntubarmu ta hanyoyin zamani.''

''Ta hakan ne mutane za su iya aikawa da wasikar email kan halin da wata bishiya take ciki ko tana bushewa ko ganyenta na zubewa da sauran matsaloli, domin hukumomi su san bishiyar tare da kai mata dauki cikin gaggawa.''

Daga nan ne sai kawai mutane suka rika zabar bishiyoyi, wadanda suka ba su sha'awa suke aika musu da wasikar kauna, maimakon su gano wadda take da matsala su sheda wa hukumomi.

Ga wasu daga cikin wasikun da mutane suka aika wa bishiyoyin ta intanet.'' Ya abar kaunata, ''A karshe dai na same ki! Ina ganinki kullum zan je jami'a, amma kuma ban san wace irin bishiya ce ke ba. Ke ce bishiyar da ta fi kowace bishiya kyau a birnin, ina kaunarki.''

'' A daidai lokacin da nake ficewa daga Kwalejin St Mary yau, sai wani abu ya buge ni, wannan abu ba reshe ba ne face kyaunki. Dole ne ki samu wannan sako a ko da yaushe. Domin ke kyakkywara bishiya ce mai daukar hankali.''

Kansila Wood ya ce, ''haka mutane suke magana da wadannan bishiyoyi kamar mutane ne, suna gaya musu yadda suke kaunarsu, suna gode musu yadda suke kare su daga rana, kuma su ba su hakuri idan karnukansu suka yi musu fitsari a jiki da safe.''

'' Haka za ka ga irin wadannan tarin wasikun email, wasu masu ban dariya wasu kuma masu sosa zuciya.''

Akwai ma wasikun da aka aiko wa bishiyoyin daga mutanen da suke zaune da a birnin wadanda yanzu suke zaune a Jamus da Amurka, inda suke bayyana yadda suke kewar bishiyoyin.

Ana ganin nan gaba kadan za a samu karin tarin wasikun email na bishiyoyin domin hukumomin suna ganin shuka wasu karin bishiyoyin da suke shirin yi zai kuma rage zafin birnin a lokacin bazara da maki hudu a ma'aunin celcius.

Bayan rage zafin birnin ga jama'a, ana ganin shuka wasu bishiyoyin 3,000 a shekara zai sa a samu karin iska. Wasu bishiyoyin sun samu wasiku daga jama'a, suna yi musu godiya kan yadda suke taimakawa suna rage musu iska mai zafi daga muhalli.

Wata wasika da na fi so an aikawa bishiya mai lamba 1022165 ne a karshen watan Mayu na wannan shekara wadda ke cewa:

Hakkin mallakar hoto al amy

'' Ya abar kauna, Ina fatan kina son kasancewa a St Mary's. A yawancin lokaci ina son hakan ni ma. Ina cikin matsin karatu saboda na kusa fara jarrabawa. Ba ki da jarrabawa saboda ke bishiya ce. Ba na jin akwai wasu abubuwa da zan fada miki domin muna da banbanci da dama saboda ke bishiya ce. To amma ina farin ciki muna tare.''

A shekarar 1975, mawakinnan Don Estelle ya bayar da shawara yana cewa,''Ya ke ciyawa mai rada ka da ki gaya wa bishiyoyin, saboda su bishiyoyin ba sa bukatar su sani.''

Ga wasikar da wani mutum shi kuma ya rubuta wa wata bishiyar mai lamba 1494392 yana cewa:

''Ya wannan bishiya da ke kuka,

Ina zaune a ciki kusa da ke, sai na lura cewa a taswirar bishiyoyin birnin kina cikin kadaici, ba ki da abokai a kusa da ke. Wannan abin ban tausayi ne saboda haka nake son kisan cewa kina raina, ina tunaninki. Kuma ina son in gode miki saboda iskar da kike sama mana muke shaka a birnin nan da ke cike da hayaniya.

Na gode, N.

Shi kuwa wannan mutumin ya aika wa bishiya mai lamba 1039919 ne ranar 14 ga watan Yuki na 2015:

Ya wannan bishiya abar kauna. Na karanta wannan shiri mai matukar muhimmanci da ban sha'awa daga nan ne na yanke shawarar in rubuto miki wannan wasika daga wani bangare na duniya- Rasha.Ina fatan kina samun kyakkyawar kulawa ba kya rashin lafiya. Wata rana za mu hadu watakila.

Naki,R.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The Melbourne treemail phenomenon