An sake kirkirar hoton yakin duniya na 1

Masu sha'awar hotunan abubuwan da suka faru a lokacin yakin duniya sun sabunta wani hoto da aka dauka a lokacin ta yadda ya zo daidai da zamanin yau inda dubban jama'a suka yi tururuwa suna jinjina da nuna goyon baya ga sojoji.

Shekaru 97 da suka wuce wasu dubban mutane sun taru inda aka dauke su hoto a kan wani tsauni a kudu maso gabashin Landan.

Sun yi gangamin ne a dandalin Hilly Fields da ke Brockley domin nuna goyon bayansu ga kokarin da ake a kan yakin duniya na biyu.

An yi taron ne kuwa a ranar Lahadi 4 ga watan Agusta na 1918, a lokacin cika shekara hudu da fara yakin duniya na daya kuma alokacin ana irin wannan taro a fadin Birtaniya kamar yadda aka yi a wannan rana a duk tsawon lokacin yakin.

Rahotannin jaridu sun nuna cewa, gangamin da aka yi a wannan tsauni a wannan shekara shi ne mafi girma da aka taba yi a wannan yanki har zuwa yau.

A lokacin taron ya hada 'yan siyasar yankin da coci-coci da ma'aikatan motocin daukar marassa lafiya da 'yan agaji na Scout da tsofaffin sojoji da sojojin kansu.

An ruwaito magajin garin yankin Leftana Kanar Sir William Wayland yana cewa, irin wannan gangami ''abu ne mai muhimmanci idan suka gamu da mutanen da a shirye suke su mika wuya''.

Sakamakon gangamin ya samar da hoto mai muhimmanci, wanda yanzu aka sake sabunta shi.

A ranar Lahadi dubban jama'a suka sake taruwa a wannan wuri, domin kirkirar irin wancan taro da yanayi da aka dauki wancan hoton, sai dai a wannan lokacin da dan bambancin yanayin halin da mutanen suke ciki.

Shugaban kungiyar al'ummar yankin na Brockley,Clare Cowen, haifaffen Afrika ta Kudu, kungiyar da ta shirya taron, ya ce, '' na ji matukar dadi kuma ina alfahari.''

Suna ganin kusan mutane 6,000 ke cikin hoton na da, a wannan sabon kuma sun kai 5,000, amma dai ana ci gaba da nazarin hoton na da domin tantance ainahin yawan mutanen.

Shugaban ya kara da cewa,'' ina ganin kusan duk wani bangare na al'ummarmu yana nan,tsoffi da matasa da 'yan Afrika da 'yan Asiya da 'yan yankin Gabas ta tsakiya da kuma Turai.''

Kungiyar ta samu hoton ne na taron na 1918 a tarin takardunta na tarihi da wani rahoto da wata jarida ta zamanin nan ta yi.

A don haka ne suka yi shawarar sake kirkirar yanayin da aka dauki hoton domin ya zo daidai da tarukan cika shekara dari da ake yi da fara yakin duniyar na daya.

Rahoton jaridar ya bayyana yadda aka fara gangamin, inda aka fara tattaki dauke da tutar Ingila daga dakin taro na Deptford zuwa tsaunin na Hilly Fields.

Jaridar, a cikin rahoton, ta kuma kawo takaitattun jawaban da aka yi wa mutane a wurin a wancan lokacin.

Daya daga cikin jawaban shi ne wanda Rabaran J W Niven ya yi inda yake cewa, '' Yau masu adawa da tashin hankali da yaki suna tsaye a gefe shiru, suna kallo, suna gabatar da huduba da jawabai kan yadda bata-gari zai sauya ya zama mutumin kirki da yadda mai kisan mutane zai rungumi addinin kirista yayin da ake duka wannan ita kuwa Jamus ba huduba ta gari take so ba, abin da take bukata shi ne a yi mata lugude, ba zaman lafiya ba, so take a lallasa ta.''

An ruwaiti magajin garin yana cewa wadanda suka bukaci zaman lafiya ta kowa ne hali,''sun manta da abubuwa kamar su nitsar da jirgin ruwan Birtaniya Lusitania da amafani da iska mai guba da kisan mata da kananan yara da rugurguza garuruwa da kauyuka da duk wani mugun aiki na makiyi wanda burinsa kawai shi ne ya cuce ka.''

Sai dai a wannan gangamin na sake sabunta yanayin hoton mutanen ba s kasance kamar na wancan lokacin ba sosai, cikin kaguwa ta yaki.

Shazia Saleemi wadda ke zaune a kusa da tsaunin Hilly Fields inda aka yi taron, wadda kuma iyayenta da 'yan uwanta Indiyawa ne amma kuma ta zo Birtaniya daga yankin Afrika ta Tsakiya ita ma ta je gangamin inda ta ce,'' ba na jin akwai wasu wadanda ba fararen fata ba ne a nan, idan aka duba hoton na ainahi.Yanzu akwai jinsin mutane daban daban. Akwai ma'aurata na jinsi daban daban.''

Ya zuwa yanzu kungiyar mutanen ta Brokley ta kasa samo wani da yake cikin hoton na ainahi ko wani dangi.

Daya daga cikin tsoffin da suka shiga gangamin na ranar Lahadi, shi ne Arthur Guidotti, mai shekara 90 wanda yake da zama a kusa da dandalin duk tsawon rayuwarsa.

Ya ce, ''mutanen unguwar sun sauya sosai. A layin da nake, Wickam Road, wuri ne na attajirai da manyan mutane a lokacin da nake matashi. Ba ta yadda za ka zauna a layin sai kana da bayi.''

Kungiyar ta mutanen na Brokley ta sa wani mai daukar hoto Simon Terrill ya dauki hotuna na musamman a lokacin taron na ranar Lahadi, wadanda za a fito da su ranar 15 ga watan Agusta.

Idan kana son karanta wannan cikin harshen Ingilishi latsa nan Recreating a WW1 picture involving thousands