Me ya sa muke gaigayar farcenmu?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Abu ne da zai bata maka hannu ko ya zama alamar kazanta wanda kuma zai iya sa yatsanka ya rika yi maka ciwo idan abin ya yi yawa. To me ya sa duk da haka mutane suke yinsa? Tom Stafford wanda shi ma yake da dabi'ar ta gaigayar farce ya yi bincike a kai.

Menene ya hada tsohon Firaministan Biritaniya Gordon Brown da Jackie Onassis da Britney Spears da kuma ni? Dukkanninmu muna da dabi'ar gaigayar farce.

Ba wai dabi'a ba ce da nake alfahari da ita. Abu ne maras kyau wasu su gan ka kana yi, wanda yake bata maka hannu, ga shi kamar ma kazanta ne, bayan haka ma kuma zai iya sa dan yatsanka ciwo idan ka gaigayi farcen

sosai. A lokuta da dama na yi kokarin watsi da wannan dabi'a amma abin ya gaggara.

A baya bayan nan ina mamakin me yake sa mutum ya zama mai yawan cin farcensa kamar ni. Shin ba mu da karfin hali ne? Ko muna da dan tabin hankali ne? Ko mun fi sauran mutane jin yunwa ne? Watakila a fagen wani bincike

na tunanin dan-adam za a iya samun wannan amsa ta tambayata har ma kila a san yadda za a yi maganin wannan dabi'a marar kyau.

Bincikena na farko a rubuce rubucen da aka yi kan wannan dabi'a ya sa na gano sunan da masana kimiyya suka sa wa wannan dabi'a ta gaigayar farce sosai da sosai (sunan shi ne onychopagia).

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Likitocin masu tabin hankali ko kuma halayyar mutum sun bayyana ta a matsayin matsalar da ke zama al'ada ga mutum.

Amma wannan, a inda dabi'ar ta zama jiki ne a wurin mutum, har ta kai ana ganin sai ya bukaci taimakon likitan hankali da dabi'ar dan-adam, kamar yadda dabi'ar yawan cirar gashi kamar na hanci ko yawan kankarar fata ko jiki

don cire wata 'yar fata ko wani abu da mutum ya ke gani ba ya so a jikinsa.

To sai dai ni ban kai irin wannan matsayin ba. Ni ina rukunin yawancin masu wannan dabi'a ne wadanda suke dabi'ar ba tare da ta sa musu wata illa ba babba.

Kusan kashi 45 cikin dari na matasa suna gaigayar farce. Za ka iya cewa ai matasa ba su da yawa , to amma ba za ka iya cewa kuma kusan rabinsu ba sa bukatar a yi musu maganin wannan dabi'a ba.

Ina son fahimtar yadda wannan dabi'a ta gaigayar farce take wadda ba ta zama mai tsanani ga mutum ba amma kuma mutum yana son ya ga ya rabu da ita.

Laifin uwa ne
Hakkin mallakar hoto .

Masu maganin abin da ya shafi hankalin mutum suna da dalilan da a ganinsu suke sa wa mutum wannan dabi'a ta gaigayar farce.

Sigmund Freud ya dora alhakin ne a kan matsalar da ta jibanci yadda tunanin yaro ko mutum a fannin dabi'ar jima'i ya faro tun yana jariri.

Kamar yadda a ka san yawancin nazari ko dalilan da Sigmund Freud ke dangantawa ko bayarwa kan dalilin wata dabi'a ta mutum, halayyar jariri ta ba wa bakinsa fifiko a kan komai, a watanni 18 na farkon rayuwarsa, na zama

sanadiyyar abubuwa da dama kamar su rashin cin abinci sosai ko cin abinci da yawa da yawan shan nonon uwa ko kuma rashin kyakkyawar dangantaka da uwa.

Haka kuma wannan lokaci da jariri yake ciki na rayuwarsa idan har wata matsala ta samu wadda ke da alaka da wannan dabi'a ta shi ta sanin bakinsa fiye da komai ana iya ganin tarin matsaloli ko wasu dabi'u a halayyarsa idan ya girma, daya daga cikinsu ita ce dabi'ar cin farce.

Ba wannan ba kadai, mutumin ma yakan kasance mai dabi'ar habaici ko gugar-zana, da shan taba da shan giya da son jima'i ta baki, kamar yadda bayanin Sigmun Freud ya nuna.

Wasu masana hanyoyin magance dabi'ar kuma suna ganin matsalar cin farce na iya samun mutum ne saboda wata damuwa da yake da ita.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu masanan na ganin cewa masu cin farce yawanci za su fi iya kasancewa masu shan giya, sai dai shedar hakan ba ta da yawa.

Kamar dalilai da dama na masana kimiyya wadannana bayanai za su iya zama gaskiya, amma kuma babu wani dalili da zai sa a ce lalle-lalle haka suke a yarda da su.

Abu mafi muhimmanci ma a wurina shi ne babu wata sahawara da suka kawo ta yadda zan raba kaina da wannan dabi'a ta cin farce.

Kuma game da dalilin da suka bayar na danganta rayuwar jariri ta lokacin yana shan nono,cewa zai iya dauko dabi'ar daga wannan lokaci sakamakon wata matsala da ya gamu da ita da ke da nasaba da wannan lokaci, a nan ma

abin ba haka yake ba a kaina, domin ko ina cikin nishadi da walwala a lokacin da ba wani abu na takurawa a gabana na kan kama farcena ina gutsirre shi da hakorina.

Saboda haka ina ganin babu wata sheda da ke nuna cewa an yi wata nasara ko za a yi wajen maganin wannan dabi'a ta dalilan da masanan suka bayar da suke kawo ta.

Abin takaicin bayan duk wadannan hasashen sai kokarin samo bakin zaren wannan dabi'a ya lafa.

Binciken da na yi na littattafai ko rubuce-rubucen kimiyya 'yan bayanai kadan kawai na samu kan maganin dabi'ar.

Wani daga cikinsu ya nuna cewa ne, duk wani mataki ko hanyar da za bi don rabuwa da dabi'ar wadda ke sa mutum ya tuna cewa yana yinta, yana taimakawa, amma bayan wannan ba wata magana kuma.

Abin takaicin ma shi ne yawancin rubuce rubuce a kan cin farcen suna farawa ne da mamakin rashin wani cikakken rubutu a kan lamarin.

Ganin cewa ba wata hanya ko mataki na kimiyya na maganin dabi'ar, a don haka na ga ni ma ina dama na yi shaci-fadi.

Saboda haka ga abin da nake gani da ke sa mutane suna wannan dabi'a ta cin farce da kuma yadda za a yi maganinta.

Da farko dai ina ganin babu wani abu da ke sa mutum ya dauki wannan dabi'a ta cin farce. Ba wata maganar sanadin shan nonon uwa ko wata danuwa ko rashin samun kaunar uwa.

Amfanin wannan bayani nawa ma shi ne, ba sai mun yi wahalar gano wata dangantaka tsakanina na Gordon Brown da Jackie Onassis da Britney Spears ba.

A maimakon haka, ina ganin dabi'ar cin farce abu ne kawai da mutun ke yi saboda wasu abubuwa daban-daban da suke tattaruwa su haifar da wata dabi'a maras kyau a kan mutum.

Da farko dai, sanin kowa ne mutum ya kai yatsansa baki ba wani abu ne mai wuya ba. Wannan daya ne daga cikin halayyar cin abinci da girma da mutum ke yi, a don haka wannan abu ne na wajibi daga cikin abubuwan da

kwakwalwa ke yi, ma'ana abu ne da zai iya zama jiki cikin dan kankanin lokaci.

Kari a kan wannan kuma, akwai maganar gyara ta hanyar cin farce, domin mutum zai iya yin hakan domin wata hanya ce mai sauki ta rage farcensa wanda kuma yinsa a wannan yanayi yana kasancewa tattare da nishadi, duk da

cewa abin zai iya kaiwa ga mutum ya tsaga farcen.

Idan aka hada wannan amfanin da kuma saukin da mutum yake yin hakan ba tare da bata wani lokacinsa ba, za a ga hakan zai iya zama dabi'ar mutum.

Bayan taba marenanka abu ne mai wuya ka ce ga wani abu da za ka yi wa kanka da kanka ka ji dadi kai tsaye kamar cin farce kuma ga shi abu ne da ba a hanawa ko a makaranta ma.

Da zaran ka fara hakan abu ne mai sauki ya zama dabi'a a wurinka.

Akwai lokuta da dama da mutum zai kasance hannunsa da bakinsa ba sa aikin komai.

Shin dabi'ar cin farce tana da wata hanyar magancewa mai sauki?

Daukar cin farce a matsayin wata dabi'a abu ne da za a iya cewa ba mai dadin ji ba idan ana maganar yadda za a yi maganin dabi'ar, tun da mun san cewa abu ne mai wuyar gaske mutum ya yi watsi da wata dabi'a maras kyau.

Yawancin mutane akalla a rana daya za su rikice idan ba su gaigayi farcensu ba.

A ganina dabi'ar gaigayar farce ba wata aba ba ce da za ta nuna yadda wani mutum yake, ba kuma wani abu ne da ke samun mutum ba sakamakon wani abu na rashin dacewa da ya gamu da shi a lokacin yana jariri.

Dabi'a ce kawai da jikinmu ke dauka saboda tsari ko siffar shi kansa jikin da yadda dabi'ar kai hannu baki ke samun zama a kwakwalwarmu da kuma tunaninmu na dabi'a.

Haka kuma na gaigayi farcena a lokacin da nake wannan rubutun. A wani lokacin hatta nazariyya mai kyau ba ta iya taimakawa wajen samun mafuta kan wata matsala da ake neman warwarewa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do we bite our nails?