Ko masu sanko sun fi kokarin jima'i?

Sinadarin halitta na namiji wato testosterone, yana kara wa namiji karfin jima'i yayin da kuma yake sa shi sanko, kamar yadda nazari ya nuna. Sai dai gaskiyar hakan na da sarkakiya. Ga binciken da Claudia Hammond ta yi.

Ka duba mutane irinsu Bruce Willis ko Andre Agassi ko Micheal Jordan, za ka ga duka wadan nan mutane masu karfi ne da siffa ta masu kuzari, da duniya ta san su, wadanda suke da mata da yawa masu sha'awar wasanninsu.

To ba a nan kamannin nasu ya tsaya ba, idan ka duba, za ka ga akwai kuma wani da ya sake hada su, wannan kuwa ba komai ba ne illa sanko.

Da yawa a kan ce maza masu sanko suna da karfin jima'i. Bayanin da aka fi bayarwa dangane da dalilin hakan shi ne, irin wadan nan mazaje suna da yawan sinadarin kwayar halittar

namiji (testosterone) wanda yake sa jikinsu ya dunkule ya kuma kara musu karfin jima'i, amma kuma ya sa su yi sanko tun suna matasa fiye da yawancin maza. To amma gaskiyar wannan lamari na da sarkakiya.

Gaskiya ne sanko na da alaka da sinadarin kwayar halittar namiji ta testosterone. A 1960 wani likita na Jami'ar Yale ta Amurka mai suna James B. Hamilton ya gudanar da nazari a kan wasu maza guda 21 da za a fidiye su(ko dandaka).

Yawanci dai ana yi wa maza da suke da wata matsala ne ta dabi'a ko wadda ta shafi kwakwalwa wannan fidiya.

Likitan ya ci gaba da bibiyar wadan nan yara, wasu har suka kai shekara 18, inda ya lura ba su da wata alama ta yin sanko yayin da suke ci gaba da manyanta.

A daya bangaren kuma likitan ya ga sa'oinsu wadanda ba a fidiye ba, wato wato jikinsu yana samar da sinadarin halittar na namiji tuni har sun fara nuna alamun sanko.

Dakta hamilton ba shi kadai ba ne ya fara gano alakar sanko da kwayar sinadarin testosterone da ke jikin maza ba.

Tun shekaru daruruwa da suka wuce Hippocrates da Aristotle sun yi irin wannan bincike.

Binciken hamilton ya nuna cewa yawan sinadarin na testosterone a jikin namiji shi ke jawo masa sanko.

Sai dai a zahiri ba haka lamarin yake ba, domin ko da wannan sinadari ba shi da yawa indai akwai shi to zai iya jawo sanko, amma namijin da aka dandake ba saboda jikinsa ba ya samar da shi, to ba zai yi sanko ba.

Duk da wannan bincike har yanzu ba za ce an fahimci yadda wannan abu yake kasancewa ba sosai.

Amma dai abin da aka sani shi ne abin yana hada wa da wasu kwayoyin halitta da suke sauya wannan sinadari na halitta na testosterone zuwa wani sinadarin daban da ake kira

dihydrotesterone wanda yake sa kofar da gashi ke tsirowa ta tsuke a jikin wasu mutanen.

Ana ganin yana hakan ne ta hanyar hana jini da sauran kwayoyin abinci da za su samar da gashin.

Yayin da jikin ya zama haka, kofar gashin take kara tsukewa, gashin da jikin mutum yake samarwa sai ya rika sirancewa har ta kai ya ma daina fitowa wajen ya zaman sanko.

Duk wannan abu da ke faruwa ya tsaya ne a wurin gashin kokon kai bai shafi na haba ba, saboda haka ne shi gemu yake ci gaba da fitowa ko da mutum ya yi sanko.

Yayin da ake ci gaba da samun ilimi a kan tasirin sinadarin halitta na testosterone akan sanko haka kuma ake kara samun hanyoyin maganinsa.

A shekarun 1960 an yi ta kokarin yadda za a magance sanko, ta hanyar sanya wa mutum kwayoyin sinadarin na testosterone kai tsaye a kokon kan.

Da farko masu binciken sun fara jarrabawa ne da mai, sai ya kasance yana da maiko da kauri, inda hakan ya sa mutane ba su iya jure wa gwajin ba, hakan ya sa aka dakatar da wannan hanya ta amfani da na mai.

Yawancin mazajen da ake gwajin da su suka daina kafin wa'adin watanni goma da aka diba na gwajin ya kai.

Duk da cewa wannan gwaji na mai bai sa gashinsu ya sake fitowa ba, to amma wasu sun ce ya rage yawan zubar gashinsu, ko da ike wannan gwaji bai tabbatar da hakan ba.

An gano cewa wasu mutanen da ba sa sanko ko gashinsu ba ya zubewa ba su da sinadaran da ke sarrafa kwayar karfin namiji ta jima'i ta testosterone, saboda haka masu bincike suke

kokarin gano hanyar da za su toshe wannan sinadari a jikin wasu mutanen da nufin hana su ko magance musu sankon.

Wannan dabara dai ta yi aiki sai dai tana da tsada kuma dole ne a ci gaba da amfani da hanyar idan ba haka ba sankon sai ya dawo.

A yanzu dai masana kimiyya na ci gaba da kokarin gano yadda gashi yake daina fitowa.

A 2010 masu bincike sun yi nazarin jikin kan mutum, inda ke da gashi da inda ba gashi, suka gano cewa kwayoyin halitta suna nan a kofofin da gashi ke fitowa a duka wuraren biyu, amma

ba sa ci gaba da girma zuwa mataki na gaba da zai sa har su kai inda za su haifar da gashi.

Wannan binciken ya kara karfafa fatan da ake yi cewa wata rana za a yi maganin sanko, wanda a yanzu haka masana na ci gaba da gudanar da bincike.

Alamu na nuna sanko ya kunshi hikayoyi da dama fiye da wasu matsalolin na jikin dan-adama saboda watakila muna ganin kamar babu wani tsari ko ka'ida ta jiki da za a ce ga mutumin da zai yi sanko, saboda haka muke neman sanin yadda yake.

Idan kana da sanko, ka da ka dauka cewa lalle kana daga cikin mazajen da suka fi karfi, amma za ka iya dora alhakin samunsa a kan iyayenka. Domin ko ba komai suke yada kwayoyin halittar.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan; Are bald men more virile?