Yadda 'yan sane suke yaudararka

Ba hannu kadai 'yan sane suke amfani da shi ba inji Caroline Williams suna amfani da raunin kwakwalwarka ma.

Babata tana da ido a keyarta. Ta kuma koyar da ni tun ina karama yadda zan kiyaye da bakin mutanen da ban yarda da su ba musamman ma idan suka ba ka wata kyauta.

Wanda wannan ne ma ya sa ta ke mamakin yadda wani mutumin kirki da ya ba ta fure har ya iya zare euro 20 daga cikin 'yar karamar jakarta ta hannu(alabe) duk da cewa tana rike da ita a hannu kuma tana kallonta.

Ta ce, ''ya gaya min cewa yana neman taimako ne na coci, saboda haka na dauko euro daya na ba shi sai ya ce min, a'a wannan ai ya yi yawa, ya nemi ya leka cikin jakar ya dauki abin da bai kai haka ba na tsaba(kwandala).

A nan ne na tabbata ya hada gaba daya da takardar euro 20 din, kuma ban san hakan ta faru ba sai bayan sa'a daya. Na ga wawanci na.''

To amma fa bai kamata ranta ya baci ba, har ma ta ga wawancinta, domin masana kai-kawon tunanin dan-adam sun ce ba karamin abu ba ne ke sa har a yaudari kwakwalwar mutum, yadda mutum yake da natsuwa da lura.

A gaskiya ma wani muhimmin abu da kwararren dan-sane ba wai kawai ya zama mai kuzari ko saurin zare abu ba ne kamar walkiya da hannunsa a'a, ilimin sanin raunin kwakwalwar mutane shi ne mafi muhimmanci.

Wasu 'yan sanen suna da kwarewa a wannan fanni da har ma masu bincike suna aiki da su domin sanin yadda tunaninmu ke aiki.

Mafi tasiri a cikin wannan rauni ko gazawa ta kwakwalwa shi ne, kwakwalwar mutum ba ta iya yin ayyuka da yawa a lokaci daya. Wanda kuma a yawancin lokaci hakan yana da kyau, domin ta hakan tana sa mu mayar da hankali a kan abubuwan da suka fi muhimmanci gare mu.

To sai dai kuma masaniya a kan ilimin kai-kawon tunanin mutum Susana Martinez-Conde,wadda ta rubuta littafin Sleights of Mind, ta ce, kwararren dan sane zai iya amfani da wannan ya yi maka sata.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Apollo Robbins( daga dama) yana kokarin daukar hankalin wani mutum ta yadda zai yi masa sane

Lalle za ta iya sanin hakan domin a matsayinta na mai bincike ta yi nazari a kan yadda Apollo Robbins yake yin daburansa na sane a shirin kwaikwayon da aka yi a Las Vegas.

Ta ce, ''Idan Apollo ya samu mutum a dandalin kwaikwayon, yana dauke hankalin mutum ne ta hanyar sa shi ya rika kallon abubuwa,kuma yana magana da shi, yana taba jikinsa, yana matsowa kusa da shi kuma yana sa mutum ya ji wani yanayi na daban yayin da yake mamaya ko shiga tunaninsa.... Abin dai kamar daukar hankali ne ta fannoni da dama a lokaci daya''

Saboda haka duk da cewa saurin hannu na da muhimmanci a harkar sane,amma abu ne da ya kunshi daukar hankalin mutum da wani motsi nan da can.

'yan-sane na titi su ma haka suke, suna amfani da wannan tsari ta hanyar kirkirar wani yanayi da zai dauki hankalinka nan da can.

Babban misali shi ne dabarar da gungun 'yan sane suke amfani da ita, ko ina a duniya ta kirkirar abin da za a iya cewa daki ko keji (a Ingilishi stall).

Da farko daya daga cikinsu ( blocker) zai shiga gaban mutumin da za a yi wa sanen(mark) yana tafiya, sai kawai ya tsaya ta yadda mutumin zai yi karo da shi, wani dan sanen kuma da yake binsu a baya, sai ya yi karo da dukkansu biyun, sai ya fara fadan karya da na gaban(blocker).

Ana cikin hakan ne, na bayan zai zare wa mutumin duk abin da zai iya, ya mika wa (sunna wa) wani dan gungun nasu na daban da yake binsa, wanda zai yi sauri ya bace daga wurin.

Wani mai wasan sanen bogi da juyar da hankalin mutum(ya zama kamar rakumi da akala) da ke Birtaniya, James Brown, ya ce, ''mutane suna ganin kamar dauke hankalin mutum ake ya kalli wani abu can, amma abin ba haka yake ba, ana jawo hankalin mutum ne zuwa wani abu da ake so ya kalla.''

ya kara da cewa, ''Idan ina son in dauki hankalinka, ka daina kallon wani abu a kan tebur abu ne mai sauki a wurina in sa hankalinka ya karkata kan wani abu daban.

Idan na ba ka abubuwa biyu ko uku da nake son ka sa hankalinka a kansu, kuma wanda nake son ka kawar da hankalinka a kai ba ya cikinsu, hakan ya ma fi sauki domin akwai karin wasu abubuwan da hankalinka zai rabu kan wanda za ka sa ido a kansa.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu dabarun kuma na hankali ne. 'yan sane sukan labe a wuraren da ake sa wani rubutu na gargadin jama'a cewa, akwai 'yan sane a wurin domin su kula, saboda haka da zarar mutum ya ga rubutun abu na farko da zai yi shi ne duba kayansa (jaka ko kudi da sauransu), wanda kuma ta haka ya nuna inda kudin nasa ko wani abu nasa yake.

To amma yadda aka yi wa babata nata sanen, babbar dabarar barawon ba irin ta 'yan sane ba ce, ya zo mata ne da sigar mutanen kirki, ba kamar wanda zai sa ka zarge shi da wani mugun nufi ba ne, kamar yadda babar tawa ta gaya min.

James Brown, ya ce yana ganin karfin hali ma yana taka muhimmiyar rawa wajen yi wa mutum sane,'' babbar dabarar da masu wasan sane da kuma na gaskiya suke amfani da ita da lalle za ta dauki hankalinka, ita ce ta nuna karfin hali.''

Ya kara da cewa,'' a nazari, karfin daukar mutum da wata siga ta kamala kadai tana iya sa a shawo kan hatta wayayyen dan-birni ya mika dukiyarsa da kansa.

Domin a 2009 wata ma'aikaciyar banki a Rasha ta bai wa wata mata da ake ganin ta juyar ko ta dauki hankalinta (kamar rakumi da kala) sama da dala dubu 80.

Mr Brown, ya ce, ''wannan abu ne mai sauki idan kana da fahimtar juna da mutum kuma ya yarda da kai.''

Miyagun dabaru:

Mr Brown ya ce, ''ba shakka idan kana son wasa da hankalin wani, lokacin da ya fi dacewa shi ne can da daddare bayan bayan an gama 'yan shaye-shaye kuma hankalin mutum(ga masu shaye shayen) ya fara gushewa.''

Brown , ya ce, ya shafe wani lokaci mai ban sha'awa da daddare inda ya ga yadda 'yan- sane suke cin karensu ba babbaka a wajen wata mashaya da ke dandalin Trafalgar a Landan.

''Suna yin dabaru na wayo.Wani misali shi ne, yadda wata yarinya za ta zo wurinka a wajen mashayar, tana maka magana,tana haka har sai ta fara dan shasshafa ka, ta haka wanda take shafawar shi ma zai dauka tare suke ya

rika shafa ta, har ta kai kuna faduwa, tana taimaka maka tana daga ka ka dauka tana taimakon ka ne, su ma abokan sanen nata watakila su zo da suna su ma za su taimaka maka. Sai da safe ka wayi gari ka ga ba agogonka ba alabenka, ka rasa komai naka.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Bayan duka wadannan bayanan da Mr Brown ya yi, yana ganin yawancin satar da ake yi, ba da wata kwarewa ake yin ta ba, kawai dama ce barayin suke amfani da ita ta ganin galala ko ta-fadi-gasassa.

Ya ce, '' bayan zaman da na yi da 'yan-sane 'yan kasar Romaniya a Gadar Landan, abin ban mamaki shi ne, kwarewar da suke da ita ko kadan ba ta kai yadda kake tunani ba.''

Amma kuma ya yi gargadin cewa duk da rashin kwarewar tasu za su iya amfani da fasaha nan ba da dadewa ba ta yadda za su iya satar bayanan katin dibar kudi a banki na mutane.

Duk da haka, abu ne mai amfanin gaske ka san duka wadannan dabaru domin ta haka za ka iya tsira da dukiyarka, kuma Brown ya ce, yana da kyau ka guji gyangyadi ko sakankacewa a cikin jama'a.

Kuma kamar yadda ba shakka babata za ta tuna maka, yana da kyau kuma ka yi nesa-nesa da mutanen da ba ka sani ba musamman wadanda ke rike da furanni.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How pickpockets trick your mind