Mutumin da ke satar bayanan waya da na'ura a cikin jikinsa

Idan ka bai wa Seth Wahle wayarka ta salula, tamkar ka mika masa sirrinka ne, idan ya ga dama, domin zai iya sace hotunanka da duk wasu abubuwanka na sirri da suke cikinta, cikin kiftawar ido.

Seth Wahle daya ne daga cikin mutanen da ake samu yanzu wadanda suke sanya wata 'yar karamar na'ura a cikin jikinsu.

Image caption Wahle ne a hannun hagu Soto kuma a dama

Shi dai tsohon kurtun sojin ruwa ne na Amurka, wanda yanzu kuma injiniya ne a wani kamfani da ake kira APA Wireless.

Yana amfani da jikinsa wajen sanya wata na'ura ya yi kutse a wata kwamfuta(a turance biohacker).

Yanzu dai Wahle yana amfani da wannan 'yar na'ura ya nuna yadda harkar tsaro ta intanet za ta iya zama a nan gaba.

Ta hanyar amfani da wannan 'yar na'ura da aka sanya masa a cikin hannu, Wahle da abokin aikinsa Rod Soto ya nuna yadda zai iya kutse cikin wayar salular mutum ta hanyar taba ta kawai.

Mutanen biyu, ba suna amfani da wannan fasaha ba ne ta wata muguwar hanya, suna dai nuna wa duniya ne wata hanyar boye ko dabara ne da za a iya satar bayanai a cikin wayoyinmu da kwamfutocinmu wata rana ba tare da mun sani ba.

Haduwar wadannan mutane biyu ta faru ne a wani gidan cin abinci inda Soto, wanda mai bincike ne kan fasahar tsaro wanda kuma ya shirya wani taro da ya shafi hanyoyin kutse a kwamfuta (mai suna Hackmiami) a Florida, ya

fahimci cewa Wahle mutum ne mai sha'awar harkar kwamfuta bayan da ya lura cewa akwai alamar 'yar wannan na'ura a cikin jikinsa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Daga 'yar hirar da suka yi ne, Soto, wanda ke aiki galibi a kan kutse a abubuwan da suka shafi kayayyakin kwamfuta da manhajarta abin ya ba shi sha'awa har ya bukaci Wahle ya gabatar da wata kasida a wani taro da ya shirya a 2014.

A wurin ne, Wahle, ya bayar da bayani kan wata fasaha da yake son ya bullo da ita ta amfani da wannan 'yar na'ura da ke cikin hannunsa a matsayin mukullin bindiga, inda bindigar za ta tashi ne kawai idan tana hannunsa.

Soto, ya ce, ''bayan wannan kasida da Wahle ya gabatar ne, sai muka yi wani tunani cewa me zai hana mu bullo da wata fasaha ta yadda za mu iya amfani da wannan 'yar na'ura da aka binne a cikin hannun Wahle, mu tura

wata manhaja ta satar bayanai cikin wayar wani ta hanyar rike wannan waya ta mutum a hannun Wahle (wato idan Wahle ya rike wayar mutum a hannunsa mai 'yar na'urar sai ta tura wannan manhaja da za ta debo bayanai daga wayar).

Yadda suka gabatar da fasahar shi ne, da zarar mutum ya mika wa Wahle wayarsa ko kwamfutarsa ko ma duk wata na'ura ta kwamfuta wadda ke amfani da fasahar karbar bayanai daga wani wuri (NFC wato Near Field

Communication), sai kawai 'yar na'urar wadda aka binne a cikin jikinsa, a tsakanin babban dan yatsansa da manuni, sai na'urar ta tura wa wayar wata alama ta yaudara da ke bukatar mutum ya sabunta wata manhaja a wayar

tasa da zarar ya amsa, sai kawai a samu sadarwa tsakanin wayar da wata kwamfuta da ke wani wuri da suka adana wadda ta hanyarta za a debo abubuwan da ake so a wayar da Wahle ya rike.

A nunin da mutanen biyu suka yi na wannan fasaha, fitowar wannan alama a wayar da Wahle ya rike za ta iya sa mai wayar ya ki amsa wannan bukata ta sabunta wata manhaja a kan fahimtar cewa wata hanya ce ta zamba.

To amma mutanen suka ce wannan ma ba wani abu ne mai wuya ba, su kauce wa hakan, ta yadda ba ma sai ka ga alamar hakan ba, in dai har wayar ta shiga hannunsa za su iya yin kutse a cikinta su debi abubuwan da suke bukata.

Wannan fasaha da mutanen biyu suka bullo da ita, za ta iya kasancewa farkon yadda za a rika satar bayanai ta hanyar amfani da 'yan mitsi-mitsin na'urori da ake boyewa a cikin jikin mutum.

Ba ta wayoyin salula kadai za a iya satar bayanai da wannan fasaha ba, hatta tsarin katin biyan kudi na banki (credit card) da makamantansu za su iya fadawa wannan tarko.

Abin ba wai sai an karbi wayarka ko katinka ko wani abu da za a saci bayanan daga cikinsa ba ma, domin kusanci kawai ake bukata a samu da wayar taka ko 'yar jakar hannunka da kake sa katinka na banki da sauran abubuwa

sai kawai a kwashi sirrinka.

To sai dai ka da hankalinka ya tashi tukuna, domin ya zuwa yanzu ba a kai lokacin da za ka rika haduwa da mutanen da suke da irin wannan 'yar mitsitsiyar na'ura ba a cikin jikinsu.

Shi kansa Wahle ya ce, ba abu ne mai sauki ba kafin ya sa na'urar a cikin jikinsa, domin sai da ya duba da gaske ya tabbatar bai dauki wadda za ta sanya masa gubar dalma ko wata guba ba a jikinsa ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Daga nan ne ya samu irin masu zanen nan da wuta a jikin mutum, ya sanya masa na'urar a tsakanin 'yan yatsunsa ta hanyar amfani da allura.

Maganar doka:

A kan yadda mutanen biyu Soto da Wahle, suka jarraba yadda fasahar take a zahiri, babu wata doka da suka karya, inda suka yi amfani da wayar Wahle, wanda kuma ya san abin da zai faru.

Amma idan a ce wani ya yi amfani da wannan fasaha a kan waya ko wata na'ura ta wani mutum ba da saninsa ba, abubuwa sai su dauki wani salo na daban, kamar yadda Andrea Matwyshyn, masaniya kan harkokin shari'a kuma

farfesa a cibiyar tsare tsare ta fasahar sadarwa a Princeton da ke Amurka ta ce.

A wurin Soto da Wahle wannan ba wani abu ba ne da ya shafi satar hotuna ko wasu bayanai a wayar mutum ba, abu ne da ya shafi bayyana rauni ko hadarin da na'urorin da jama'a ke amfani da su yau da kullum suke fuskanta.

Wahle ya ce, ''abin da muke nufi da wannan abu kawai shi ne, ''mu karya wani abu domin mu nuna wa wani cewa za a iya karya wannan abu.''

Shi ma Soto ya amince da haka, inda ya ce,'' babban dalilin wannan abu shi ne idan ka tona wani abu na zamba, abin zai bayyana ga jama'a, mutane za su san da shi, ba zai yi aiki ba, za a iya samun kariya daga gare shi shi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen ingilishi latsa nan The man who hacks phones with an implant under his skin