Mutumin da yake da kafafuwa 13

Hakkin mallakar hoto Getty

A yanzu mutanen da ke amfani da kafafuwa ko hannuwa na roba ko karfe ba sa wadatuwa da guda daya kawai kamar yadda Frank Swain ya gano.

A duk lokacin da Jozef Metelka ya tashi daga barci da safe abu na farko da ke zuwa ransa shi ne wacce daga cikin tarin kafafuwansa na roba zai yi amfani da ita a wannan rana.

Tun bayan da ya rasa kafarsa a wani hadarin babur a 2009, Metelka wanda ke matukar sha'awar yin wasanni daban-daban ya sa aka yi masa kafafuwa na roba na musamman iri daban-daban har 12, wadanda aka tsara za su iya yin komai, kama daga wasan hawa tsauni da keke da kuma na wasan sulu da katako a kankara da sauransu.

Kafar Metelka ta farko, kafa ce ta roba wadda zai iya tsayawa da tafiya da ita kawai, wadda kuma aka yi masa a karkashin shirin kula da lafiya na jama'a na Birtaniya (NHS).

Bayan nan ne kuma sai ya hadu da kwararru a wannan fanni na yin kafar roba, inda daga nan sai ya fara tara kafafuwan daga wannan nau'i zuwa wancan na wasanni da yanayi daban daban.

Hakkin mallakar hoto prosthetic legs stairs

A duk lokacin da ya yi tunanin wani wasa ko wani abu da yake so ya yi da kafa amma a kafafofin da yake da su babu wadda za ta yi sai wadannan kwararru su dukufa kan yadda za su yi masa kafar kamar yadda yake bukata.

Kirkirar kafar roba wadda za ta iya aiki kamar kafar mutum ta sosai a yanzu ba abu ne mai yuwuwa ba.

A maimakon haka, duk kafar robar da aka kera ana yinta ne domin wani abu daban. Kowacce daga cikin tarin kafofin Metelka na roba tana zuwa ne da tsarinta na daban. Kuma sai an yi la'akari da irin abin da zai yi da ita da wuri da kuma inda zai yi amfanin da ita.

Metelka ba shi kadai ba ne da yake sa a yi masa irin wadannan kafafuwa. A shekarun nan ana samun hannaye na roba da kafafuwa na musamman iri daban daban, kowanne ka ga ni da yadda mai su zai yi amfani da su daidai da bukatarsa.

David Blum, wanda manomi ne yana da kafar roba mai karfi wadda zai iya irin aikinsa da ita.

Shi kuwa zakaran wasan tseren motoci Mike Shultz, ya fahimci cewa kafarsa ta roba, ba za ta iya jure wahalar tseren mota ba, saboda haka ya kera kafarsa da kansa da kayan keke.

Hakkin mallakar hoto prosthetic legs high heels

Kera kafar roba da za ta yi aiki tare da kafar mutum ta sosai ba karamin aiki ba ne.

A wani lokaci da Metelka ya je wasan sulun kankara, yanayin tsananin sanyi ya sa kusoshin kafar ta shi ta roba suka cije, ba sa motsawa har sai da aka yanke su, sannan aka sa masa wata kafar.

To amma kuma a daya bangaren ita ma kirar kafar roba tana da irin nata saukin, domin ba kamar kafa ta Sosai ba, ba za ka takura kanka sai ka yi ta yadda za a iya yin komai da komai da ita ba.

Metelka ya ce, ''duk da cewa ba za a iya yin kafar roba da za ta iya aiki kamar yadda kafa ta sosai take ba, to amma kuma za a iya yin ta robar da za ta fi kafar ta sosai aiki a wani fannin.'' Ya kara da cewa, ''a halin yanzu ma muna kan wannan hanya.''

A misali, kafin gasar Olympics ta 2012 hukumomin wasanni da kwararru masu kera kafar roba sun yi muhawara kan ko kafar robar da dan tseren Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, yake amfani da ita, tana ba shi dama fiye da masu kafafuwa na sosai wadanda ba nakasassu ba ne.

Bincike ya nuna Oscar din bai samu wata dama ba fiye da sauran 'yan tseren wadanda ba nakasassu ba.

Amma Metelka, ya ce, zuwa shekara ta 2019 za a iya ganin wata gasa ta wasa da mutane masu lafiyar jiki ba za su iya fafatawa da nakasassu wadanda za su iya samun kafafuwan roba da kwararru suka yi su da fasaha sosai ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Paul carter, shi ma wani nakasasshen ne da ke da kafofin roba daban-daban, ko da ike nasa kadan ne. Shi dai an haife shi ne ba kafafuwa ba kuma hannaye. Yana da kafofin robar saiti uku(guda shida, wato hagu da dama) har ma da irin na gudun nan na taya amma masu karfe kamar reza din nan, wadanda Pistorius ya yi suna da su.

Lokacin da Carter yake yaro, maikatan asibiti da sauran kwararru masu kula da shi, sun ba shi kafofi da hannunwan roba iri daban-daban ta yadda zai iya yin kusan kowane abu.

Ya ce,'' ina da abubuwan yin komai da za ka iya tunani, kama daga balla maballin riga da sa wando da cin abinci da komai.

To amma yayin da na girma na samu 'yancin dogaro da kaina, wani aiki ne in rinka yawo da wadannan abubuwa barkatai.

Daga karshe dai sai Carter ya ga cewa gara ya koyi yadda zai rika yin komai da kansa maimakon ya dogara da wadannan kafafuwa da hannaye na roba iri daban-daban.

Dukkaninsu biyun, shi Carter da Metelka sun yi maganar bukatar tsara yadda za a tabbatar kana da kafafun robar da suka dace da kai kowana abu za ka yi, ba sai ka rika sauyawa ba daga wannan zuwa waccan.

Matar da ta yi fice wajen yin kafafuwa da sauran sassan jiki na roba irin na kawa ita ce Oliveira Barata.

A dakin baje kolin kayayyakin da take yi na nakasassun na kawa ne za ka ga abubuwa na ban sha'awa da mamaki da aka kawata su.

Babu wani hannu ko kafar roba da ake samu a araha, domin kafar roba mai takalmin sulu mai karfe guda daya ana sayar da ita dala 4,000, ita kuwa kafar Metelka mai taya ta musamman dala dubu 900 ce.

Tsadar wadannan abubuwa ita ce Carter yake ganin babbar matsalar wadanda suke son a yi musu kafafu ko hannuwa na roba na musamman.

Inda shi da kansa ya ce,''idan da kudi ba matsala ba ne, da sai na samu duk irin kafofin da nake bukata.'' Yana dariya yana cewa, ''zan zama Imelda marcos ta masu kafafuwan roba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Prosthetics: Meet the man with 13 legs