Abin da kila ba ka sani ba a kan barci

A yanzu ne aka fara sanin sirrin da ke tattare da barci.William Park ya duba wasu daga cikin abubuwa masu sarkakiya da masu bincike suka gano a kan barci.

Sanin yadda barci yake a yawancin lokaci abu ne da zai iya kasancewa mai rikitar da kai.Har yanzu masu bincike ba su da tabbaci a kan abin da kwakwalwarmu take yi, da abin da ya sa muke mafarki ko menene ma ma'anar mafarki.

To amma akwai wasu abubuwan mamaki ko masu sarkakiya da muka fahimta a shekarun nan a game da abin da zuciyarmu (tunaninmu) ke yi a lokacin barci.

Ga wasu abubuwan mamaki guda goma da suke karin haske kan dalilan da suke sa mu bukatar barci na hutawa.

1. Kanshin da ka saba ji zai iya sa ka haddace wani abu a kwakwalwarka a lokacin da kake barci, wanda hakan zai sa ka kara kokari wajen koyar wasu abubuwa masu sauki.

2.Layin da mutane ke yi a lokacin da suke gyangyadi abu ne da kusan kowa yake yi, wanda kuma ba shi da wata illa.

3.Wani dan karamin bincike da aka yi, ya nuna cewa koyon busa wani abu kamar algaita yana taimakawa barci, saboda ana ganin yana kara karfafa jijiyoyin numfashi.

4. Lokacin da ya fi dacewa mutum ya yi kailula (dan barcin rana) kamar yadda aikin jikinmu yake bukata shi ne tsakanin karfe biyu zuwa hudu na yamma.

Hakkin mallakar hoto SPL

To amma yayin da yin wannan barcin bayan wannan lokaci yake sa mutum ya warware sosai, yinsa kafin lokacin (biyu zuwa hudu na yamma) zai fi sa basirarka ta karu.

5. A nazarinmu na baya kan barci, mun nuna cewa wata kwayar halitta mai suna DEC2 za ta iya sa wasu mutanen su kasance ba sa bukatar dogon barci, ta inda za su iya barcin sa'o'i hudu a duk dare ba tare da wata matsala ba.

6. Sai dai watakila kai ba ka cikin mutanen da suke da wannan dama,domin kasa da kashi biyar cikin dari ne kadai na mutane suke barci dan kadan. Yawancin mutane suna bukatar barcin sa'o'i takwas, amma kuma kusan kashi 30 cikin dari ba ma barcin ma da ya kai na sa'oi shida a duk dare.

7. Wani nazari a kan dalilin da ya sa muke bukatar barci shi ne, kwakwalwarmu tana amfani da wannan dama ta hardace abubuwan da da suka shige ta a wannan rana.

Haka kuma barcin yana iya ba mu damar kawar da abubuwan rashin jin dadi ko na damuwa da suka same mu.

8.Wasu masu bincike sun yi amfani da ayyukan da kwakwalwar mutane take yi, suka sake fasalin hotunan bidiyon YouTube da mutanen suke kallo.

Ana tunanin za a iya amfani da wannan fasaha wata rana a sake kirkirar mafarkin da muke yi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

9. Masu bincike a fagen ayyukan soji, sun gano cewa, idan ka samu wadataccen barci ta hanyar kwanciya da wuri, idan ka samu kanka a yanayin da aka hana ka barci, lamarin ba za i yi tasiri a kanka ba sosai.

10. Idan ka yi kwana 12 a jere kana barcin sa'a shida kawai a duk dare, an yi kiyasin hakan daidai yake da kashi digo daya cikin dari (0.1%) na barasa a jikinka, wanda yake iya sa maganarka ta zama wata iri, sannan ba ka iya tsayuwa da kyau kuma ba ka iya tuna abu yadda yakamata. A takaice dai ka zama kamar wanda ya bugu da giya.

Idan kana bukatar karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What you may not know about sleep