Wane irin mafarki dabbobi suke yi ?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idan dabbobi suna mafarki kamar yadda muke yi ,to su ina suke tafiya a barcinsu ? Jason G Goldman ya duba yadda za mu iya leka zuciyar kyanwowi da tsuntsaye da sauran dabbobi a lokacin da suke barci.

'' Kusan dukkanin dabbobi an lura cewa suna barci, ko da na sama ne, ko na ruwa ko kuma na tudu,'' kamar yadda Aristotle ya rubuta a littafinsa na Sleep and Sleeplessness (wato barci da rashin barci).

To amma abin tambaya a nan shi ne, shin sauran dabbbobi suna mafarki? A kan wannan ma masanin falsafan na kasar Girka yana da yana da ta cewa.

A rubutun da ya yi, The History of Animals, ya ce, '' Za a ga ba mutane ne kadai suke mafarki ba, su ma dawaki da karnuka da shanu da tumakai da awakai da sauran dabbobi suna nuna alamun mafarkinsu inda suke haushi ko kuka a lokacin da suke barci.''

Duk da cewa tsarin bincikensa ba shi da wata kwarewa ko hanyoyi na zamani to amma duk da haka, Aristotle bai kauce wa hanya sosai ba a kan lamarin.

Ba shakka ba za mu iya tambayar dabbobi ko suna mafarki ba, ko ba sa yi, to amma za mu iya ganin alamun cewa kila suna yi.

Akwai hanyoyi biyu da masana kimiyya suka fuskanci wannan lamari da za a iya cewa abu ne da ba zai yiwu ba.

Na farko shi ne lura da yadda dabi'arsu take a matakai daban-daban na lokacin da suke barci.

Na biyu shi ne, mu duba mu ga ko kwakwalwarsu a lokacin da suke barci tana aiki kamar yadda tamu take yi idan muna barci.

Tun a shekarun 1960 ne aka fara maganar, yadda za a yi nazarin tunani ko kwakwalwar dabbobin da suke barci.

Tun a wancan lokacin aka rika samun rahotanni a mujallun kimiyya na yadda mutane suke yin wasu abubuwa da suka danganci motsi a lokacin da suke barci.

Wannan abin mamaki ne domin a lokacin da muke barci jijiyoyin jikinmu kusan ba sa aiki ko sun tsaya cik.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Ko mafarki dabi'a ce ta dan adam kadai ? Sheda ta nuna cewa a'a.

Masu bincike sun gano cewa sanya dabbobi a yanayi na barci kamar yadda mutane suke zai sa su tabbatar da yadda suke mafarki.

A shekarar 1965, wasu masana kimiyya 'yan Faransa Michel Jouvet da J F Delorme, sun gano cewa idan aka cire sashen kwayar halittar kwakwalwa wanda ke tattara sako ya mika(the pons) zuwa wasu wuraren, a kwakwalwar

kyanwa, hakan yana hana ta shiga irin yanayin da mutum yake shiga inda jijiyoyin jikinsa suke mutuwa wato ba sa aiki ko motsi idan yana barci.

Masanan sun ga, idan aka cire wa kyanwar wannan sashe, maimakon ta kwanta shiru ba motsi idan tana barci, sai ya kasance tana tafiya nan da can kuma tana fada.

Wannan ya nuna tana mafarkin abubuwan da ta yi lokacin da ba barci take ba, wato tana farke. Bincike da dama da aka yi a baya ya nuna irin wannan dabi'a ko abu a kan dabbobi.

Wani masani kan dabbobi Adrian Morrison, wanda ya yi rubutu a kan wannan bincike, ya ce, kyanwa tana tafiye ne a wannan yanayi ( da aka cire mata wannan kwayar halitta a kwakwalwarta) kamar tana bin wani abu ne da ke jan hankalinta.

Wasu kyanwowin kuma suna tafiya ne kamar suna bin bera za su kama a mafarkin nasu. Su ma karnuka an ga suna irin wannan abu, da aka cire musu wannan kwayar halitta mai tattara sakonni a kwakwalwarsu.

Wasu mutanen ma suna yin mafarkinsu kamar a zahiri idan ya kasance sun samu kansu cikin wata matsala da ta shafi barci.

Mutum zai rika naushi da tafiya da bugu da kafa da gudu daga kan gado a lokacin da yake mafarki, alamu ne na abin da yake gani ko yi a mafarkin kamar yadda masana suka nuna.

Mutanen da suke da irin wannan matsala suna yawan jin rauni har ma su ji wa wadanda suke barci da su.

Hakkin mallakar hoto spl
Masu bincike sun sake tsara yadda beraye ke zirga-zirga a lokacin mafarkinsu.

Motsi na zahiri ba shi kadai ba ne hanyar gano yadda mafarki yake. A yanzu masu bincike suna iya nazari kan yadda kwayoyin halitta da ke kwakwalwa suke aiki a jikin dabbobi a lokacin da suke barci.

A 2007 wasu masana na Cibiyar Fasaha ta Massachusetts MIT, Kenway Louise da Matthew Wilson, sun yi nazari a kan aikin da wani sashe na kwakwalwar bera da ake kira hippocampus, sashen da ke aikin kula da samar da bayanai da kuma fassara bayanai.

Sun yi nazarin yadda kwakwalwar take aiki a lokacin da bera yake guje-guje a aminsa da kuma yadda take aiki a lokacin da yake barci.

A binciken nasu sun ga cewa wurin da beran yake kasancewa a dai-dai wani lokaci, a lokacin da ba barci yake ba, haka kuma kwakwalwarsa take aiki idan yana barci a wani lokaci idan yana mafarki.

Kuma ta hakan har masanan suna iya sanin dai-dai inda beran zai kasance idan da a zahiri yana tafiyar ne idan aka yi nazarin aikin kwakwalwar tasa.

Amish Dave da Daniel Margoliash na Jami'ar Chicago, sun gudanar da irin wannan bincike a kan kwakwalwar wata tsuntsuwa nau'in benu (Zebra finch) suka ga irin wannan aiki ko dabi'a.

Haka kuma wadannan masanan biyu, sun yi nazari a kan tsuntsaye kan yadda suke waka.

A bincikensu sun gano cewa tsuntsaye suna koyon waka ne ko kukansu tun suna kanana, ba wai wani abu ba ne da yake a dashe a kwakwalwarsu da suke amfani da shi idan suna son su yi waka ko kuka ba.

Da hakan masu binciken suka gano cewa har ma, za su iya sanin yadda wakar tsuntsayen za ta kasance daga farko zuwa karshenta, ta hanyar bin yanayin motsin kwayoyin halittar cikin kwakwalwar.

Can kuma a lokacin da tsuntsayen suke barci, Dave da Margoliash sun duba yadda aikin kwayar halittar cikin kwakwalwar tsuntsayen yake, inda suka ga aikin yana tafiya ne cikin tsari kamar yadda yake idan suna waka ko kuka lokacin da suke a farke.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Da hakan suke ganin za a iya cewa tsuntsuwar nau'in benu tana koyon yadda take waka a lokacin da take barci

Ko za a iya cewa dabi'ar kyanwa da aka yi nazari a karkashin binciken kimiyya, a ce lalle wannan abu da take yi mafarki ne?

Ko beraye suna sanin cewa suna guje-guje a lokacin da suke barci a cikin tunaninsu ko kwakwalwarsu (kamar yadda mutum yake sanin wasu abubuwa da yake yi a lokacin barcinsa, wanda hakan ke kasancewa mafarkinsa).

Ko tsuntsaye sun san cewa suna kuka ko waka a barcinsu? Wadannan tambayoyi suna da wuyar amsawa kamar yadda tambaya kan hayyaci (conciousness) take. Abu ne mai wuyar sha'ani ko sarkakiya.

Mu mutane ba kasafai muke sanin muna mafarki a lokacin da muke yi ba, sai bayan da muka farka daga barci.

Ko wannan tsuntsuwa nau'in benu tana iya tuna mafarkin da ta yi a matsayin mafarki a lokacin da ta farka daga barci?

Ko za ta iya bambanta ainahin duniyar da take ta zahiri da kuma wadda ta shiga a lokacin mafarkinta.

A yanzu dai ba tare da wata tantama ko shakku ba, za mu iya cewa, mun lura beraye da tsuntsaye da kyanwowi da wasu dabbobi suna abubuwa da jikinsu da kuma kwakwalwarsu kamar yadda mutum yake yi a lokacin da yake mafarki.

To amma sanin ainahin yadda ake ji idan an yi mafarki, idan har kai ba mutum ba ne, abu ne da har yanzu yake kamar dabo, wanda ba gano ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What do animals dream about ?