Kazamin sirrin warin kafa

Hakkin mallakar hoto Getty

Kafa mai wari ba aba ce mai ba wa mutum kunya ba kadai, domin fahimtar abin da ke sa warin zai iya sa a ceto rayukan mutane. David Robson ya bincika duniyar halittun da ke rayuwa a tafin kafarmu suke fitar da wannan wari.

Renate Smallegange wata ce da za a iya cewa kwararriya a sanin kafa mai wari, wadda ta yi bincike na ban mamaki a wannan fanni domin gano duk wani abu da ke haddasa wannan wari.

A wasu lokutan ta kan tattara safar da aka yi amfani da ita da take wannan wari domin binciken kwakwaf.

Idan kuma hakan bai gamsar da ita ba, ta kan sa mutane su goga kafarsu a kwayoyin dutsan wuya na gilashi ta yadda tafin kafar zai yi gumi sannan su shafe gumin a wani wuri.

Idan kuma ba ta gamsu ba, tana son ta tsananta bincike, ta kan sa mutum ya sa kafarsa a jakar leda domin ta iya shinshina warin yadda take so.

A duk irin ayyukan da ke duniyar nan, wannan dai ba aiki ne da za a ce mai dadi ba, amma Smallegange ba ta ko gezau kan yadda take wannan aiki na bincike duk da irin yadda za ka ga kafar wasu mutanen har dauda ko kwantsa-kwatsa take yi.

Duk da haka ta gaya min cewa,''ai wannan ba wani abu ba ne.'' ta kara da cewa, ''ba shakka kafar wasu ta fi ta wasu saukin wari kamar yadda na fahimta.''

Wannan wari na kafa ba kowa yake damu ba. Duk da cewa wani warin idan ya yi yawa ya kan iya sa Smallegange har ta dan rufe hancinta, to amma wani abin kuwa da binciken na ta ya hada da shi, dadin warin yake ji, wannan

abin kuwa ba komai ba ne illa sauron da ke yada zazzabin Maleriya.

A kan hakan ne Smallengange take kokarin gano abin da yake sa kafarmu wannan wari, a kokarin da take yi na dakile yaduwar wannan cuta ta zazzabin cizon sauro da ke kisa.

Duk yadda kafarka ta kai da tsafta sai ta yi dan warin nan saboda yadda halittar kafar tamu take.

Hakkin mallakar hoto science photo library
Image caption Tarin kwayoyin bacteria na Staphylococcus na rayuwa a kafarka inda suke sa tafin kafar wari

Galibin kafar mutane tana da jijiyoyin da ke fitar da gumi 600 a duk dan wurin da bai wuce fadin murabba'in santimita daya ba (Per square centimeter), daruruwa fiye da yadda suke a hammata.

Wadannan jijiyoyi suna fitar da abubuwa daban-daban (da za a iya cewa kayan abinci) da ke samar da abinci mai dadi ga tarin halitttun bacteria.

A madadin abincin da halittun bacterian suke samu daga jijiyoyin gumin, su kuma suke fitar da wannan gumi da ya ke kunshe da kwayoyin da suke yin wannan wari.

Akwai kwayoyin bacteria masu tarin yawa da suke rayuwa a tafin kafarmu, da yawansu ya sa har masana ma sun kusan kasa gane wadanda suke sa wannan wari a kafarmu, da kuma takamaimai inda suke a kafar.

A baya bayan nan James Reynolds na Jami'ar Loughborough, da sauran abokan aikinsa sun yi kokarin amsa wannan tambaya ta hanyar gano yawa da inda kwayoyin bacteria suke a kafarsu.

A binciken da suka yi sun gano wasu rukuni biyar da suka fi yawa, wadannan kuwa su ne; Corynebacteria da Micrococci da Propionibacteria da Betaproteobacteria da kuma Brevibacteria.

Amma wadda ta fi fitar da wannan wari ita ce, Staphylococci kuma a ko da yaushe tana haduwa ne da wani ruwan sinadari mai muhimmanci mai suna isovaleric acid.

Reynolds ya ce, '' idan ka bude kwalbar wannan sinadari za ka ji kamar warin wani abu da ya rube, kuma idan ka dan zubar da shi a kasa a dakin bincike warin da za ka yi ta ji ke nan a duk ranar, abu ne maras dadi.''

Kuma wani abu ma shi ne wadannan abubuwa da suke sa wannan wari sun fi yawa a tafin kafa maimakon saman kafar, kuma sun fi yawa ma a daidai gaba da kwarmin tafin kafar kafin 'yan yatsu, wanda watakila hakan ya sa wannan wurin ya fi wari a kafar mutum.

Kwanta dauda ko maikon da kafar tamu ke fitarwa da kamar cuku(cheese na Turawa) ko man-shanu ya dace domin abin ya yi kama da su.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Da yawa daga nau'in cuku(cheese) daban-daban suna dauke da sinadarai daban-daban, inda cukun wanda ake kira Limburger ya fi kama da wannan maiko ko dauda ta kafa.

A karshe dai ana ganin wannan bincike zai iya samar da damar yin kayan kanshi fiye da da yadda ake da su a yanzu.

Reynolds ya ce, ''idan muka san sinadarai da nau'in halittun da ke samar da wadannan sinadarai to sai mu rika yin tufafin da za su iya dauke wannan wari ko kawar da shi.''

Sai dai wannan bincike zai iya kasancewa mai sarkakiya musamman yadda ya shafi kwayoyin bacteria mai wari.

Daga cikin kwayoyin bacteria da ke kafarmu,a kawai wadanda suke da amafani, wurin kare kafar daga wasu cututtuka.

To amma ba haka kawai halitta ta kasance ba, domin akwai bayanan da ke tattare da hakan, domin wani bincke da aka yi kwanan nan a Japan, an gano cewa wasu sinadarai uku da ake samu a 'ya'yan itace dangin lemo za su

iya kashe kwayar bacteria ta Staphylococcus ba tare da sun cutar da sauran kwayoyin bacteria na kusa da ita ba, wadnda ba sa haddasa wannan wari na kafa.

A wasu lokutan warin kafa ya wuce abin kunya kawai, domin ya kan iya jefa mutum cikin hadarin kamuwa da cutar da za ta iya kai shi ga halaka.

Wata masaniyar kimiyya 'yar kasar Holland Bart Knols na daya daga cikin wadanda suka gano cewa wani nau'in sauro da ke yada cutar maleriya yana son bin kafar mutum da wannan wari yake.

Tuni bincikenta ya sa aka ci ga ba da kara zurfafa bincike a kan wasu daga cikin nazarin baya bayan nan da Smallegange ta yi a Jami'ar Wageningen ta kasar ta Netherlands.

Akwai hanyoyi da dama da za a iya yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta hanyar amfani da wannan nazari.

Smallengange ta kuma yi nazari kan yadda ko hada wari iri daban-daban na kwayoyin bacteria a kafar mutum zai iya kare mutum daga cizon sauro, kamar yadda aka gano cewa wadanda kafarsu ke dauke da kwayoyin bacteria na Staphylococcus sauro ya fi binsu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawan warin kafarka yawan yadda za ta jawo sauron da ke yada cutar maleriya

A kan wannan, kokarin kawar da wannan kwayar bacteria zai iya samar da hanyar kariya daga cutar maleriya.

Za kuma a iya amfani da warin wajen yi wa sauro tarko, inda za a iya amfani da safar da aka yi amfani da ita mai wari, domin safa tana iya zama da wanna wari kwana takwas bayan an cire ta.

Haka kuma Smallengange tana fatan ganin yadda za ta hada sinadaran da za su samar da wannan wari ta hada a kwalba, yadda zai zama ana amfani da hadin wajen maganin sauro.

Ba a dai san yadda za a iya amfani da wannan dabara wajen maganin sauron ba. A yanzu dai ana wani karamin gwaji a tsibirin Rusinga na Kenya, inda ake bincike kan ko tarkon zai kashe sauro ko kuma ya hana sauro da yawa cizon da zai sa wa mutum zazzabi.

Akalla dai za a iya amfani da sakamakon binciken wajen gargadi, inda za a iya sanincewa sauron da ke yada maleriya yana kusa.

A wurin yawancinmu, kafar da ke da dauda-daudan nan ko maikon dattin nan da ke wari ba wani abu ne da zai gagare mu wanke wa ba.

Amma binciken da Smallengange ta sanya a gaba abu ne da ke da muhimmancin da za ka tuna, a duk lokacin da ka ga wannan dauda a tafin kafarka.

Domin tana kokarin ceto rayuka ne da abin da take yi, wanda mutane kadan ne a cikinmu za su iya jure masa, inda take tattara abubuwa masu dauke da warin kafa kamar su safa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Turanci latsa nan The disgusting secrets of smelly feet