Ko dabbobi suna son kayan maye?

Ko gaskiya ne giwaye da birai da kifi (dolphine) da sauran dabbobi su kan sha abubuwan maye domin su bugu? Jason Goldman ya bincika.

A kasar Afrika ta Kudu, akwai labarin kunne-ya-girmi-kaka da ke cewa giwaye suna son shan kayan maye. A kan ce sukan je su nemi wata bishiya mai 'ya'ya da ake kira marula, inda suke cin 'ya'yan wadanda suna da tsami da ke sa maye, su yi ta ci har ta kai sun bugu.

Wannan labari na shan barasar na giwaye ya kai akalla karni biyu baya. A shekarun 1830 wani dan kasar Faransa da ake kira Adulphe Delegorgue ya bayar da labarin yadda wasu 'yan kabilar Zulu, masu yi masa jagora a yawan da ya je na bude idanu a dazuka, inda suka sheda masa cewa sun ga giwaye suna wasu abubuwa ko halaye na ban mamaki bayan da suka ci 'ya'yan bishiyar marula.

A rubutunsa, Delegorgue, ya ce, ''giwaye kamar mutum suna da yanayi na yadda sukan dan bugu idan suka ci 'ya'yan ita ce da rana ta sa suka tsima, ta yadda za su sa dan maye.''

Ba giwaye ba ne kadai suke sha ko cin abubuwan da suke sa su maye ba. Akwai labaran da ke cewa wasu dabbobi a kasar Australiya dangin babba-da-jaka da suke shiga yanayi na maye ta hanyar cin wasu shukoki masu furanni masu launuka ko kuma karnuka da suma suke shiga maye ta hanyar shan wata guba da manyan kwadi na tudu ke fitarwa.

Akwai kuma labarin da ke cewa koren biri a tsibirin St Kitts na yankin tsakiyar Amurka(Carribean) shi ma yana shan kayan maye da na masu yawon bude idanu.

To amma nawa ne daga cikin wannan ya tabbata abin da muke sha'awa na tabbatar da cewa sauran dabbobi lalle sukan sha abubuwan da suke juyar da hankali?

Bincike da aka yi a dakin kimiyya na shekaru, ya nuna cewa za mu iya sa dabbobi maye ta hanyar ba su abubuwan sa mayen.

Hakkin mallakar hoto science photo library

To su kuma dabbobin daji su ma suna buguwa ko shiga maye?

Koren biri na daga dabbobin dajin da bincike zai iya sa ya tabbatar da amsar wannan tambaya.

Wannan biri dai asalinsa dan nahiyar Afrika ne, amma ya dan wasu a yankin tsakiyar Amurka.

A karni na 18 da na 19 masu bautar da mutane sun rika daukar wannan nau'in biri a matsayin dabbar dajin da suke ajiyewa domin sha'awa, kuma a lokacin da jirgin ruwan masu bautar da mutanen ya isa can biran sukan tsere ko kuma a sake su, su watsu.

Tun da yanzu ba sa cikin wata barazana daga wasu dabbobi sai su sake su zama kamar daman asalinsu a nan suke.

Tsawon shekara 300 biran suna zama ne a yankin da ake noman rake, saboda haka idan aka kona raken ko kuma ya tsima kafin a girbe shi, sukan sha shi, kuma su ji dadi ta yadda yake sa su maye.

Ganin yadda suka saba da sinadarin ethanol da ke raken da ya tsima,ana ganin da haka suka saba da dandano da kuma juriyar shan barasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai labaran da ke nuna yadda ake kama birrai ta hanyar musu tarko da ruwan sinadarin raken tsumamme wanda ke bugar da su a kama su ba tare da wata wahala ba. Tuni aka gudanar da bincike kan jikokin birran da aka kai yankin na tsakiyar Amurka(Caribbean) domin fahimtar dabi'arsu ta maye.

Wani nazari ya nuna cewa kusan duk biri daya a cikin biyar ya fi son a ba shi barasar da aka sirka da ruwan sukari maimakon ruwan sukari kawai.

Wani abin mamaki kuma shi ne matasan birrai sun fi shan barasar a kan manya, kuma matasansu maza da mata sun fi shan giyar.

Masu binciken karkashin jagorancin Jorge Juarez na Jami'ar Mexico ta Universidad Nacional Autonoma de Mexico, yana ganin dattawa ko manyan birrai suna kaurace wa shan barasa ne saboda kame girmansu, domin yanzu sun girma.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ba lalle ba ne a danganta wannan dabi'a ta wadannan birrai da ta kifin da ke shayar da 'ya'yansa ba (dolphin).

A 1995 masaniyar kimiyyar teku, Lisa Steiner, ta bayar da bayanin wata dabi'a da za a iya cewa ta daban da ta lura da ita a tsibirin Azores na kasar Portugal.

Masaniyar ta ga yadda wani taron kifi 50 zuwa 60 (dolphins), kamar suna cin abinci amma kuma suna wasu dab'u na daban ba kamar yadda aka san su da kuzari ba.

Kadan daga cikinsu suna cin abinci amma yawancinsu suna iyo a sannu-sannu.

Daga nan ne sai masaniyar ta lura da mushen wani kifi mai guba da ake kira puffer guda biyu wadancan manyan kifaye (dolphins) suna kamar wasa da su.

Da farko ta dauka wasa suke yi amma can a karshe sai take ganin manyan kifayen da alamu sun bugu ne da gubar wannan kifi domin kusan dukkaninsu manyan kifayen sun zama kamar wadnda lakarsu ta mutu.

Ba dai za a iya cewa ga abin da su manyan kifayen suke yi da gawarwakin wannan nau'in kifi mai guba ba takamaimai, amma yanayin da suke ya nuna kamar suna buguwa ne da gubar kifin.

Wani shirin BBC da aka yi a kan manyan kifayen(dolphin) da ka yada a shekara da ta gabata shi ma ya gabatar da irin wannan ra'ayi.

Wannan magana dai tana da sarkakiya saboda gubar wannan kifi tana da hadari sosai domin 'yar kadan za ta iya kisa.

Masaniyar kuma tana ganin cewa abu ne mai wuyar gaske a ce dabbar ruwa mai kwakwalwa kamar wannan kifi(dolphin) ya taba gubar wannan kifi wanda gubarsa ta fi ta dabbobin da suka yi kaurin suna a karfin gubarsu.

Bayan haka kuma, masaniya Lisa Steiner, tana ganin ai ita gubar wannan kifi tana kashe laka ne ba ta juyar da kwakwalwa ko tunanin dabba, domin su wadancan manyan kifaye(dolphins) a lokacin da ta gan su a wanna hali suna wasu dabi'u na daban.

Hakkin mallakar hoto andreas maecker

A game da giwaye kuwa kimiyyar a bayyane take. Dabbar tana da girma sosai da ba karamin tarin wanna 'ya'yan ita ce na marula za ta ci ba kafin ta bugu ko ta shiga maye.

Masana kimiyya Steve Morris da David Humphreys da Dan Reynolds na Jami'ar Bristol, da farko sun ji labarin giwayen masu buguwa da barasa a lokacin da suke halartar wani taro a Afrika ta Kudu, daga nan ne sai suka nemi gudanar da bincike domin gano gaskiyar maganar.

Neman wani rubutu na binciken kimiyya ya ba da kwarin gwiwa cewa giwaye na iya buguwa da barasa.

Wani bincike da aka yi a 1984 ya nuna cewa wasu giwaye sun ji dadin shan wani ruwan da aka sirka da barasa ta kashi bakwai cikin dari, kuma da yawa daga cikinsu sun rika sha har sai da dabi'arsu ta sauya.

Duk da cewa ba su yi abubuwa kamar yadda mutum yake dangantawa da buguwa ba, sun rage lokacinsu na cin abinci da shan ruwa da wanka da kuma duba wasu abubuwa da sukan yi, sannan kuma sun nuna alamun gajiya ko rashin kuzari.

Da yawa daga cikinsu sun rika wasu dabi'u na kamar ba sa jin dadi ko suna da 'yar damuwa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Saboda giwaye za su iya buguwa da barasa, hakan ba zai zama cewa, suna shan barasa a daji ba daga lokaci zuwa lokaci da har zai sa a yarda da duk labarin kunne-ya-girmi- kaka na Afrika ta Kudun ba na cewa giwayen sun dauki bishiyar marula kamar giyarsu ba.

Saboda giwa mai nauyin kilogram 3,000 sai ta sha tsakanin lita 10 zuwa 27 na ruwan da kashi bakwai cikin dari aka gauraya shi da barasa sannan dabi'arta ta sauya.

Ko da 'ya'yan wannan bishiya da ake magana ta marula suna da ruwan barasa na ethanol kashi uku cikin dari giwar da za ta ci 'ya'yan itace a yadda ta saba ci, da wuya ta samu yawan giyar da za ta sa ta bugu a rana daga wannan dan itace.

Idan har giwa tana son ta bugu daga cin 'ya'yan itacen na marula, bisa la'akari da girmanta dole ne sai ta ci 'yan itacen da suka kai kashi 400 cikin dari na yadda ta saba cin abinci kuma ba tare da ta sha wani ruwa na daban ba.

''A bincikenmu,'' in ji masanan wannan abu ne da yake da wuyar gaske a ce ya faru.''

Har yanzu dai dole ne a san abin da ya sa giwayen da ke rayuwa kusa da bishiyar marula ke yin abu kamar wadanda suka bugu.

Morris da Humphreys da Reynolds sun kawo dalilai biyu da suke gani za su iya kasancewa dalili.

Da farko suna ganin giwayen suna dabi'u na daban ne idan suna wurin bishiyar saboda suna son 'ya'yan itacen sosai.

Dalili na biyu kuma wanda ya fi sarkakiya, shi ne akwai wani abin mai bugarwa da suke ci.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Masanan suna ganin bayan 'ya'yan itacen, giwayen suna kuma cin bawon bishiyar wani lokaci.

To bawon kuma yawanci yana dauke da tsutsar buzuzu (kwaro) wadda ita kuma tana dauke da wata guba da 'yan Afrika kamar yadda tarihi ya nuna suke amfani da gubar a bakansu(kibiya), a don haka kila suna buguwa ne sakamkon cin wannan guba.

Wannan tunani ne mai daukar hankali, ko ba haka ba? A ce sauran dabbobi suna sha'awar buguwa kamar yadda mutane suke yi ?

Duk da cewa akwai wasu labaran na gaskiya na yadda wasu dabbobin dawa suke ci ko shan wasu abubuwa su jirkita musu hankali, yawancin irin wadannan labarai, labarai ne kawai na kunne-ya-girmi-kaka, saura kuma ba ma su da wata sheda da za iya fahimtarsu.

Morris da Humphreys da kuma Reynolds sun nuna cewa galibin wadannan labarai na cewa dabbobi suna shan miyagun kwayoyi da giya har su bugu,kirkiraru ne ko kuma shaci-fadi ko hikaya.

A wasu lokutan kuma zai iya kasancewa mutane suna kuskuren danganta wata dabi'a da dabbar ta yi da halin da mutum ke shiga idan yana cikin maye.

Buguwa ko marisar naman daji ka iya kasancewa ne kawai a tunani ko idon wanda ya gani.

Idan kana son karanta wannan aharshen Ingilishi latsa nan Do animals like drugs and alcohol